← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 120

Sashe 5

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasu hawayen ne suka sake gangarowa daga jajayen idanuwansa kafin ya bude bakinsa muryansa a sanqare da sanyi duk da yasan suna sane da waye din amma bude baki yayi yace

"Nine Abdul"

Katsesa Gali yayi da cewa

"Lafiya kuwa cikin sanyin?

Bude baki yayi zaiyi magana amma Galin ya wuce cikim sauri yayi masallaci sbd jin angama kiran.

Baba ila ne ya kallesa cikeda baqin ciki da tsana me tsananin gaske yace

"Allah ya tsinewa sanayyar datake tsakanin Sakina da Uwarka dan kuwa babu abinda kuke qararta dashi sai baqin talauci da baqaqen masifun da kuke yawo dashi,
Ace har tsakar dare bata huta da masifunku ba,
Yanzu ubanme zatai muku da asubar farin??

Wani abu me daci da nauyi Abdul ya hadiye kafin ya bude baki yace

"Haihuwa ummana tayi"

Cikin sabon baqin cikin daya tirniqe baba ilan ya tsaki tsokin daya saka Abdul din rintse idanuwansa yace

"An haifowa sakina wata sabuwar Masifar kenan,to wlh tallahi baa gidana ba,
Na gaji bazan iya ba,duk yanda nake shan rantsuwa da masifa sakina ta ture bata ji bata gani saita ringa daukan abincin danake wahala ina nemowa na gidana ta baku to daga yau ankai karshe sbd bazai yiyu ni ban tara nawa yaran dazan ringa ciyarwa ba haka kawai na koma ciyar da 'yayan wani katan"

Juyawa yayi ya koma ciki yana fasa zuwa masallacin bakinsa na cikowa da kumfan masifa sbd yasan yana tafiya wlh sai an dauki abincin gidansa ko wani abin antafi dashi sbd sakina dai sedai ya barwa fatima da 'danta dan bazata iya rabuwa dasu ba.

Abdul cikin tsananin sanyi da azabar data gama shigarsa ya bi bayan baban da sauri dan kada ya hanasa ma shiga.

Kai tsaye dakin sakina ya nufa ya kiran sunanta cikin tsananin baqin ciki da masifa taresa bacin rai yana cewa maza ta fito.

Daman ba wani nauyin bacci ne da ita ba dan haka cikin bacci taji yana kiran sunanta da karfi ta bude idanuwanta tana kokarin tashi zaune ya shigo dakin sbd daman baa dakinta ya kwana ba ranar a dakin uwargidansa ya kwana.

Yana shigowa dakin ta lalubo fitilarta ta kunna haske ya wadata dakin,

Akan Abdul dayake tsaye a kofa bai qarasa shigowaba idanuwanta suka sauka.

Faduwa gabanta yayi da sauri ta janyo dankwali tana daurawa akanta ta miqe daga katifar datake kai tana ambatar sunansa baba ila ya katseta da cewa

"Ayau idan har kika fita gidan nan kika bi yaron nan gurin uwarsa wlh tallahi a bakin aurenki hakama abinci na ko wani abin dayake nawa a gidan nan kika basu shima a bakin aurenki,
Bazan iya ba na gaji da renan 'da da uwar da banda hadi komai dasu bare yanxu wata wahalar da aka sake haifowa......

Da sauri sakina ta dago idanuwanta da ciko da hawayen tashin hankali da firgicin maganarsa ta farko ta kalli Abdul jin maganar haihuwar.

Shima dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta cikeda girgiza da tsoron abinda Baba ilan ya fada.

Gangarowa hawayensa masu tsananin zafi sukai ya dan ja baya ahankali batareda ya iya cigaba da tsayawa ba sbd bai san me zai fadawa mama sakinan ba kuma.

Bude baki tayi ahankali tace

"ABDULAZIZ"

Cak ya tsaya batareda ya dagoba.

Kofar inda kayanta suke tai batareda ta cewa baba ilan komaiba,

Zannuwan kayanta na sakawa masu tsafta ta dauko tareda guda biyu da rigarta ta sanyi daya da ita kadai takeda ita ta dauko wanda itace da kanta ta siya abinta da yan kudinta.

Inda take ajiye kudi ta duba tana saka hannu cikin kofin silver me murfi taji babu komai a ciki.

Juyawa tayi ta duba gurin ajiyarta daya taga dari bakwai ne kadai da ita dan haka ta dauko dari biyar ta juyo ta nufi kofar ta fito.

Kayan ta miqa masa cikeda kunyarsa duk da yana qaramin yaro ta bude baki asanyaye tace

"Ka siya mata koko me zafi sauran canjin ka siya itace ka dafa mata ruwan zafi tayi wanka itace da abinda aka haifa"

Hawayensa ne suka gangaro ahankali suka sauka akan dari biyar din data dora masa a tafin hannunsa.

Kasa magana yayi kai ya gyada mata ahankali yana damqe kayan hannuwansa na qara daukan sanyi.

Baba ila daya kasa motsawa sbd baqin ciki da mamaki kallanta yayi ita kuma taqi kallansa
Baqin ciki sake rufesa yayi kamar zai fashe sbd baqin ciki yace

"Sbd ki nunamun ban isaba shine a gaban nawa ko matsawa daga inda nai maganar banba zaki dauki abubuwa ki basu??
To meye amfani na a rayuwarki sakina tinda kinada Fatima da 'danta ai saiki fice ki bisu kije na bar musu ke wlh"

Abdul kafafuwansa da sanyi yayiwa mugun shiga ya ja ahankali yabar gurin yana qanwame kayan data basa da kudin.

Yana ficewa gidan Mama sakina ta dago ta kalli baba ila har zatai magana sai ya katseta cikin tsananin zafi da cewa

"Wlh tallahi na barwa fatima ke kawai ki tattara ki bar mun gidana ki bita can saiki kwasheta kiyi kauyenku da ita da 'yayanta"

Kofa ya nufa yana ball da butarta dake hanyarsa ta wucewa yana jin zuciyarsa na wata irin tafasa da bacin rai me tsanani.

Numfashi me sanyi da mutuwar jiki ta sake tana danne zuciyarta akan furucinsa wanda shedan ke ingizata data bar masa gidan nasa ta tafin sbd su fatima sunfi buqatarta amma kuma girman auren nata take kalla ta danne zafi da bacin da ranta yayi dan yanzu ne zata biye masa suyita masifa a cikin gidan har wayewar gari da wuni zasu iya wuni suna masifa.

Butarta dayayi wurgi da ita ta nufa ta dauka tana qarasa zubar da ruwan ciki da suka rage ta nufi gurin diban wasu ruwan tana duba butar idan bai fasa mata ita ba.

Tana diban ruwan bandaki ta fara shiga tana fitowa tai alwala ta shige dakinta.
#MAMUH
#ZADEENS
#LIMBAS

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
#ZafafaBiyar

5
*ZUZEAMVENTURES*
08144015291
Aslm barkanmu da wannan lokaci
Ina Mai farin cikin sanar daku cewa Zuzeam ventures takawo maku ingantattun magunguna masu inganci cikin Aminci Muna da kaya kamar haka
Mallaka Maganin sanyi
Maganin cire tumbiMaganin farin jini
Maganin matsiMaganin mata
Maganin sa ni’ima da dandano
Dulka Amare Set na gyran jiki
Set na amarya
Tabaje tsumin Gomba
Xuma kiba ta hips and Brest
Magungunan gyran Brest
Magungunan Karin hips
Maganin sliming
Muna da kaya masu inganci cikin sauki da rahusa
Ina wadda keneman mallaka sahihiya quaranty wlh hajiya kixo ga zuzeam ventures xakiji ddin mallaka duk fadin ran ogah duk fadansa wlh sai yyi sanyi 08144015291
Idan maganin mata kikeso akwai
Idan gyran jiki kikeso gyran fata gyran Brest magungunan sa kiba da hips
DOMIN samunta Kai tsaye kira wannan no 08144015291 DOMIN mgn da ita whatapp 08144015291muna tura kayanmu ko ina cikin iKon allah 🥰👌🏻
Bononza Bononza Tsimin mangoro 1k🥭 Tsimin dabino 1k Gumba ukku balai 700 Gumba aya da nonon rakumi 700 Garin kafi ciccibi 500
Garin bata gaban kishiya 500
Matsin mallaka tada zaune tsaye 2500
Turaren mallaka ba aba mai kishiya 2500 Total kayan 9500
Za a bakisu akan 3800
Kuma mutun goman farko nadakyautar Abun 2k
🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️🗣️ ASSALAMU ALAIKUM ALHAMDULILLAH YAN UWA NEW PROMO YA KAMMALA💃🏽💃🏽💃🏽😁😁😁 da 5k dinki ki kwashi kayan 12k hajiyata 💃🏽💃🏽💃🏽😃🙃Kazar gadali ta mallara Rabi 3500 Tsimin gam gam 1500 Ruwan kara zunzurutun dadı😋800 Garin 7in1 1k Gumba 3 balai 500 Gumba kwakwa da dabino 500 Infection ruwan tsarki 1k Garin zunzurutun dadi 1200 Matsin ba a fira d wando 500 Matsin infection mai matse mace gam 500 12k All at 5k kedai dannan link dinnan don samun naki ki maza kiyi bucking koda kudinki saida Rabonki

************
Abdul kuwa yana fita gidan tafiya me dan tsayi yayi kafin ya durkushe a gurin yana fasa wani irin kuka me tsananin gaske sanyin gaske na ratsatsa.

Saida aka fito masallaci kafin ya daure ya qarasa gida,

Koda ya isa zanin dayake rufe da umman me sanyi kawai ya yaye mata ya rufa mata daya daga cikin wanda mama sakina ta basa,
Leqa babyn datake kwance gefen umman yayi yaga bacci takeyi lafiya kalau dan haka ya fice.

Alwala yayi ya dawo daga kofar dakin ya samu inda yayi sallah.

Yana idarwa ya dawo cikin dakin ya taba ummansa yaga tana numfashi.

Ajiyar zuciya me tsananin sanyi ya sauke kafin ya fita sbd gari ya waye sosai.

Gurin me siyarda koko ya tafi
Sai alokacin ma take hada wutar hada kokon dan haka yabar kudinsa ya koma ya nufi daji ya samo abinda zai hura wutan ruwan zafin da mama sakina tace.

Duka sun jiqe abubuwan daya tsinto amma hakanan yaje ya siyo ashana ya karbo kokon daga nan ya kawo mata.

Daqyar ya iya taimakawa umman ta tashi zaune ya dora mata robar kokon wadda ta bude bakinta daqyar kokon na shiga wanda zafinsa ya sakata jin hanjinta da suka nade suka dunqule fara warwarewa harma cikin na dan mata ciwo.

Tana gama shanye kokon amai ya taso mata gabaki daya ta amayar dashi.

Wutar ya hau hurawa wadda ta cinye gaba daya ashanar daya siyo sai daya koma ya qaro wata itama saida ta kusa qarew kafin wutar ta kama jikinsa na rawa ya dora ruwan.

Hura wutar ya zauna yanayi sosai batareda ya hutaba har saida ruwan sikai zafi sosai.

Umman daqyar ta iya tasowa ta nufi bandaki yakai mata ruwan shima ya fito ya dauko babyn ya fito daga daki sai a lokacin ya zuba mata idanuwansa yafara yi mata wani irin kallan tsafta me hade da wata irin kauna me tsananin gasken da batada sirki.

Wanka sosai umman tayi ta gyaro kanta ta fito har lokacin bata iya ko tsayuwar kirki.

Uwar haihuwar data bari a dakin ta shiga ta dauko ta goma gefen gidansu daya zube ta binneta daqyar jikin yana kakkarwa sosai sbd jirin gaske ma take gani.

Yana ganin hakan ya shiga dakin da sauri ya dan gyarosa ya share ya goge duk sanyin dakin tas ya sake shimfida mata wani zanin akan qaramar katifarsu umman ta kwanta.
Chapter 5 · 0% Book details