← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 120

Sashe 106

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali idaniwanta na yin ja tafara bayyana mata waye Ummitah da AZIZ LIMBA,
Su waye asalin iyayensu hakama waye mama a gurinsu,
Waye Sayd a gurin Ummitah da kuma waye asalin mahaifin Falaq tareda yanda rasuwar Ummitan ta sauya rayuwar kowanne a cikinsu musamman AZIZ da irin jinyar dayasha da mutuwar daya kusan yi wanda anan ne ma ya samu duk matsalar da ake tinanin yanada ita..

Dena sauti kukan Jannah yayi sai ahankali kukan ke fita sbd karfinta daya kare tareda zuciyarta da azabar ciwo da radadi,
Qunci ne kawai take ji tako ina yana tsagata yana kashe duk wani halittar da Allah yayi a jikinta kalaman Fiddausi na yaga azabtaccen radadi akowane saqo na jikinta da zuciyarta dake karban kowane zancen da ciwonsa dayake yankanta direct.

Miqewa Fiddausi tayi ta fita dan kawo mata ruwa ko zata iya dawowa daidai sbd gabaki daya ta koma kalar qunci da tsananin tausayi,
Idanuwanta sunyi munin da ko gani sosai bata yi dasu.

Awanni ta share a zube tsakiyar palon tana kukan da har zuciyarta ta kasa dauka kafin ahankali ta tashi hannuwanta babu karfi ta tattara takardun palon ta fice dasu.

Fitowa tayi babu karfi ko kadan a jikinta bare zuciyarta ta fice daga gidan.

Yau securities basu hanatava sbd ganin yanayinta kamar ta zare dan ko gani sosai batayi gashi kuma dai suna cikin tsananin jimamin abinda yake faruwa dan haka babu me energy na hayaniya.

Tafiya takeyi da kafa tana dafe zuciyarta dakejin kaman zata buga,
Ciwon gaske take mata ba iya na qunci ba ciwon azaba take mata.

Tafiya tayi sosai kafin ta samu motar data tsayar ta shiga tana rintse idanuwanta da babu kyan gani ko kadan tanajin tsananin tausayin AZIZ LIMBA da ahalinta da rayuwar kowannensu ta lalace a daidai gabar da ake yanzu dukkaninsu sbd ita,

Kaddara ta riga ta hada rayuka biyi a guri daya,
Gangar jikin Zaadens da Zuciyar Limbas wanda kowannesu a yanzu neman mafitar fita daga wannan mummunan kaddadar suke.

Asibiti ta iso Allah yasa Saleem yana dawowa kenan shima dan haka shine ya biya mai motan yana kallanta cikin mummunan tsoron wata masifar ce ta kunno kenan.

Ciki sukayo tana handa hanya bata gani sosai hakama jikinta yayi weak sosai....

Suna isa dakin da Dad yake zaune Maheer yana basa tea ahankali yana sha Mimi ma na zaune gefe tayi shiru tareda nisa a tinani sosai batama san tinanin datake ba sbd depression da yayi mata mummunan kamu itama.

Shigowan Jannah din da yanayinta ya sakasu duka juyowa kanta suna kallanta da mamakin ganin yanda ta koma kamar mahauciyar da batada gata ko kadan.

Takardun hannuwanta ta dago hawaye masu tsananin ciwo suna gangarowa daga cikin idaniwanta ta miqawa Maheer tana bude bakinta dayayi tsananin nauyi muryanta bata fita sosai tace

"Shin dukkanin abinda yake cikin nan da gaske ne?
Shin ni har nakai matsayin macen da zaa hallaka rayuka da dama sbd na rayu?
Shin mummunan kaddarata takai na saka imanin ahalins ko nace iyayena fita su iya kisan mutane da dama harda me tsohon cikin datake rokon a saukaka mata?????

Zubewa tai qasa tana fasa sabon kukan dayake fitowa rin daga zuciyarta tana rintse idanuwanta hawaye na fita sosai.

Dad kasa dago idaniwansa da sukai jajir yayi yana jin ciwo da radadin da Jannah din ke ji na samunsu da wannan mummunan aikin da shine yake lalata rayuwar kowa a yanzu harda tata din da sukai komai dan ta inganta.

Maheer kuwa damqe file din yayi shima ciwo da radadin abin na saka idaniwansa jajir hannuwansa na rawa sautin kukanta na ratsa kowa dakin.

Mimi ce ta kalli Dad gabanta na faduwa kafin ahankali ta dawo da kallanta kan Maheer da hawaye masu tsananin ciwo suka gangaro masa...

Jin tayi gabanta ya sake mummunan faduwa ta kalli saleem da shima mafi girman tashin hankalin ya shiga yana kallansu kafin ya miqa hannunsa yana rawa ya ciro file din daga hannun Maheer ya fara budewa yana karanta abubuwan dake a ciki a fili muryansa na wani rawar tashin hankali da firgici....

Yana isowa na Ummitah ya ambaci sunanta wanda yake hade dana AZIZ LIMBA take Mimi tayi baya tana jan numfashi ta fada jikin bango shima Saleem dagowa yayi hawyae na bin fuskansa ya kalli jannah wadda ta bude baki tace

"Zuciyar Ummitah Limba ce a kirjina,
Zuciyar mahaifiyar Falaq ce take bugawa a kirjina,
Zuciyar macen da aka kashe ce da tsohon ciki ce a kirjina,
Zuciyar macen da a nata ahalin itace haske kuma idaniya a kirjina.........

Maheer ne yayi saurin miqewa yana isa ga jannah din cikin dana sani da ciwo
Yace

"Duka sbd ki rayu ne Jannah"

Wani mummunan jan numfashi Mimi tayi tana zubewa qasa sbd tsananin shock da tashin hankalin jin abinda bata taba jiba....

Saleem da ganinsa da jinsa ya dauke take shima zubewar yayi qasa zaune yana qurawa Maheer da Dad idaniwansa...

Ahankali Maheer ya bude baki yafara fadar duk abubuwan da suka aikata din wanda take zuciyar Mimi da Saleem harma da jannah suka kasa dauka
Mimi tafara jan Numfashinta dake neman katsewa tamkar me asthma,

Ganin tana neman rasa numfashinta Saleem da baya gani sosai yayi kanta sa rarrafe yana kokarin ambatar sunanta amma bakinsa ya kasa buduwa hakama hannuwansa shima sun mutu sai yaji kawai komai baya motsawa a jikinsa hawaye suka fara gangaro masa kafin yayi yunquri yana ji yana gani Mimin ta juye a gurin numfashinta ma dakatawa cak.

Ita kanta jannah a jikin Maheer ta zube dan haka dole Maheer din hankali tashe ya nemo likitoci aka kwashesu su ukun zuwa emergency.

Dad da maheer kuwa jigum sukai babu me iya cewa komai suka zubawa sarautar Allah ido suna fatan ba wannan shine karshensu ba na shedar da mutuwar rayuka mafi soyuwa a rayuwarsa akan laifin da sune suka aikataba.

Har dare babu labarin komai da kowa a tsakanin su ukun dan haka Dad da Maheer din suka sake shiga mummunan yanayi na dana sani da damuwa me tsanani.
#MAMUH
#BEST LOVE
#AZIZ AY LIMBA
#JANNAH ZAD
#LIFE CHANGING
#NEW LIFE
#NEW BEGINNING
#AYSH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
87
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

***************
Cikin dare sosai Likitoci suka samu fitowa daga dakin Falaq zuciyoyinsu da fuskokinsu babu farin ciki ko kadan saima tausayinta dana familyn nata da suke asibitin a cikin mummunan yanayi na sanyi.

Dr Ashir ne ya tsaya gabansu tareda sauke ajiyar zuciya me sanyi yana kallan AZIZ LIMBA wanda idanuwansa sukai ciki gabaki daya sbd tsananin tsoro da damuwar data gama cinye dukkanin kuzari da jarumta tareda karfin halinsa.

Irin kallan da dr Ashir yake masa ya saka dukkaninsu juyawa suna kallan AZIZ din wanda ya koma ahankali ya zauna yana dauke idanuwansa daga kan ashir din Mama tai saurin dafasa tana riqe hannunsa cikin kokarin basa kariya da kwarin gwiwan da itama bata dashi.

"Ta riga takai stage din datake buqatan heart transplant batareda bata lokaci ba ko daukan lokaci ba...."

Ahankali ya zame daga kujeran dayake zuwa qasa yana qanqame hannun mama datake riqe dashi ya cusa fuskansa a tafin hannuwanta wasu hawaye masu tsananin zafi da tashin hankali suna gangaro masa jikinsa na daukan rawa gabaki daya wanda ya saka kowa dayake gurin tsit kafin kukan daya kasa riqewa ya kubce masa sbd kaman ana fada masa ne Falaq tafiya zatai ta barsa kenan..

Sautin kukansa ne ya tayarda tsikar jikin dukkanin wanda yake gurin yana ratsa zuciyoyinsu,

Jijjiga jikinsa keyi sosai fuskansa na tafin hannuwan mama datake hawayen tausayinsa har cikin ranta,

Sayd ma silalewa yayi ya zauna a qasa hawaye masu tsananin zafi da radadi na tsinke masa sbd kai tsaye kaman dama ce aka sanar dasu ta kwanakin dasuka ragewa Falaq a duniya.

Mama ma ganin kukan Sayd sai ta kasa riqe sautin kukanta ta rintse idanuwanta tana sake jin saukan hawayen AZIZ masu zafi a tafin hannunta.

Dr Ashir da suke saka hawaye taruwa a idanuwansa barin gurin yayi yana jin tausayin familyn gabaki daya sbd shi kansa yasan samun donor abu ne me wuyar gaske da ahaka suna ji suna gani lokacinta zaiyi tabar duniya.

Daqyar mama ta iya kama hannunsa ta dagar dashi ta kama hannun Sayd shima dayake kuka rasa 'yarsa da har yau batasan matsayinsa na mahaifintaba,
'Yar dayake kallo a lokutan quncinsa ya samu sassauci da sanyi,
'Yar dayake wa kallan mahaifiyarta daya rasa,
'Yar da har yau bata taba kallansa a uba ba bare ambatarsa da sunan uba ko so daya ba...

Dakin falaq din mama ta shiga dasu ta isa dasu har bakin gadonta ta saki hannuwansu suna kallan yanda Allah ya Maidata a lokaci daya ba kyan gani,

Oxygen ne da wasu abubuwan a fuskanta da bakinta harma da kirjinta,
Chapter 106 · 0% Book details