← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 120

Sashe 113

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammar ma juyawa yayi yana kasa kallanta kuka me karfin gaske yana zuwar masa kaman yanda Maheer ma kasa kallanta yayi kansa n qasa idanuwansa sunyi jajir.

Securities mata aka kira da sauri suka fito aka fara banbareta daga jikin dad dinta ta sake qanqamesa tana qin sakinsa tana tsananta kukanta tana kiran sunansa.

Kasa cireta daga jikinsa akai zuwa lokacin shima kukan yakeyi sosai sbd gabaki daya zuciyarsa matacciya ce akan 'yarsa..

Dukanta Securities din suka farayi tana qin sakinsa dan haka suka fara tsanantawa Ammar ya juyo da saurin yana rufeta jikinsa hakama Maheer dad ya rufe wanda shima ake dukansa sbd rufesu da duka akai ana kokarin rabasu jannah na sake riqe dad din wanda yake banbareta da jikinsa shima sbd a dena dukanta.

Ba tausayi aka rufesu da duka gabaki dayansu dan haka Dad ya saka karfinsa ya cinketa daga jikinsa akai saurin riqeta tana zubewa qasa cikin tsananin kukan dayake neman qare mata tana rintse idanuwanta bakinta na fidda jini.

Jansu akai zuwa ciki da karfi kowannensu bakinsa da hancinsu na fidda jinin dayake kona zuciyarta yana kasheta ahankali.

Sai alokacin aka fito da Anny da dr Abraham wanda zaa miqa kasarsu acan xai karba nasa hukuncin sbd acanma sun kashe rayuka akai ciki dasu Anny bata iya ko tsayuwa sbd daurin dayake hannuwa da kafafunta.

Ana shigewa dasu aka saketa tareda barinta zaune a gurin tana kukan da babu sauti sai numfashi kawai.

Duk yanda taso sake ganinsu baa bata damaba dan haka a gurin ta wuni sai dare ta koma gida zazzabi me karfi na cinta.

Kwantawa tai kawai bata iya komai sai jikinta dake rawar zazzabi har wani azababben bacci ya dauketa a gurin.

Tsakiyar dare cikin bacci taji motsi a kofa ta bude idanuwanta ahankali daqyar sbd nauyinsu ta motsa tareda dafawa ta tashi zaune ta miqe tsaye tareda nufar window datake jin motsi kullum tinda ta dawo kwana dakin kullum tana jin motsi kaman akwai wanda yake kwana kofar dakin dan haka yau bude window tayi kai tsaye.

"SALEEM" ta furta cikin tsananin sanyi da mutuwar jiki tareda kasa yadda da abinda idanuwanta suke nuna mata.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
93
*SHOP WITH ME by RANO*
08030811300
Best children's clothing shop💯
https://chat.whatsapp.com/Gk4H76TlRgyAAWIWgx3Jo7

Kina neman in da zaki samun kayan yara classy kaya na yan gayu at a very affordable price? Ko kina son fara kasuwancin kayan yara amma baki da jarin da zaki saro kayan? Nesa ta zo kusa, kiyi joining community din nan muna saka kaya masu kyau available da inganci a farashi me sauki da zaki dauka ki tallata har ki samu naki kema.
Burinmu shine kowacce mace ta samu sanaar da zata dogara da kanta.

**************
Dakatawa yayi cak daga kokarin barin gurin dayake tareda kasa juyowa yana rintse idanuwansa da sukai wata irin rama suka qanjame.,

Bude kofar dakin tayi ahankali zata fito takarda me tsayin gaske ta fado daga jikin kofar wadda ta sakata dakatawa tana kallan takardar kafin ta dago ta kalli bayan saleem din wanda da alama shine ya saka mata ita

Durqusawa tayi ahankali ta dauka tareda budewa hannuwanta na rawa tafara karanta abinda yake ciki.....

Subucewa takardar tayi daga hannunta cikin wani irin slow na mafi munin tashin jiri ya dibeta tayi baya zata zube ya juyo da sauri ya tareta jikinsa yana sauke idanuwansa akanta.

Numfashi ta ringa saukewa ahankali ahankali tana jero ajiyar zuciya tana samu tana neman karbo hankalinta dayake barin jikinta,

Karfi ta harhada ta zame daga jikinsa tareda miqewa tsaye daidai ta daga hannu cikin rufewan ido ta sakar masa wani lafiyayyan mari tareda cakumosa bakinta na rawa hawaye masu tsananin zafi na gangaro mata tace

"Me nayi maka zaka mun hakan???
Mene nayi na cancanta wannan abinda zakamun??
Idan ka zabi barina me zaka cewa ubangijinka da nauyina a yanzu ya dora maka?
Me nayi dazan cancanci hakan?

Sakinsa tayi tana yin baya tana neman kuka amma ya kasa zuwa tace

"Ka tausayawa maraicina karka mun haka Saleem,
Kai kadai gareni a yanzu,
Mutuwa zanyi idan ka aikata abinda kake niyar aikatawa,
Karka mun hakan,
Dan Allah karka mun hakan saleem karka kasheni"

Rungumeta yayi da karfi yana fasa kuka a jikinta yana girgiza mata kai cikin radadin zuciya yace

"Mutuwa zanyi kamar yanda Mimi ta tafi,
Zuciyata ta dade da bugawa banda sauran amfani a rayuwata yanzu bayan na bawa falaq zuciyata sbd nemawa ahalinmu sassauci da samun yancin fitowa daga azabar da suke ciki,
Babu wanda zai iya janyewa ya kashe case dinnan su Dad su futo idan ba AZIZ LIMBA ba"

Girgiza kai takeyi da karfi tana qanqamesa kaman zata shige kirjinsa ta boye zuciyarsa...

"Jannah su Dad bazasu taba fitowa kashesu zaayi kaman yanda suka kashe wanda rayuwarki ce zata mutu ta lalace kwata kwata idan hakan ta faru,
Banda amfani,banda tinanin kaina,banda iko ko karfin da zan baki kariya dan hakanne na zabi zama donor din Falaq Aziz sbd kubutar da Dad da Ammar wainda zasu baki kariya da karfinsu da rayuwarsu......"

"No,no,no,no Saleem,pls pls pls dena fada,
Bazan taba barin hakan ba koda zan rasa raina bazan taba barin kayi hakan ba,
Falaq zata rayu,zata samu Donor,
Zan bata tawa amma dan Allah Saleem karka mun hakan,
Karka zabi barina a wannan quntacciyar duniyar ni kadai banda kowa sai kai,
Karkayi Saleem kaine sanyin zuciyata a yanzu,kaine gani na da jina dan Allah karka barni ina buqatarka,ina tsananin kaunarka mutuwa zanyi idan kayi hakan"

Gabaki daya ta fita hayyacinta batama san me take fada ba tana qanqamesa da karfi koina jikinta na wata irin rawa tana neman zarewa gabaki dayanta.

Rawa shima jikinsa yakeyi yana janyeta jikinsa amma sam taqi sakinsa dan haka ya koma da ita ciki suka zauna taja jikinsa tanata surutai bakinta na rawa hakama jikinta.

Rarrashinta yafara kokarin yi yana tattaro karfin hali sbd tagama kashe zuciyarsa da jikinsa da yanayinsa da yanda ta fita hankalinta fit lokaci daya da jin abinda zaiyi din.

Shiru sikai yana shafa bayanta ahankali yana mata karatun adduoi a cikin kunnenta ahankali suna ratsata kafin ya fara karantu alqurani a cikin kunnen yana samar mata da nutsuwa da dawowa hayyacinta sbd alamun zarewa da suka bayyanar mata.

Ratsata karatun keyi tana sakewa a jikinsa tana rufe idanuwanta ahankali ahankali har dare ya sake ratsawa sosai kamar wadda akayowa aiken bacci sai gashi ya dauketa ahankali ajikin Saleem din wadda yake kuka sosai yana mata karatun har lokacin.

Duk yanda yaso yaci karfin zuciyarsa kasawa yayi sbd yanason kubutar da ahalinsa su rayu sbd rayuwar jannah din kawai,
Hakama yanason ya bawa AZIZ LIMBA hope na sabuwar rayuwar daya rasa ta hanyar bawa falaq KALBIM dinsa a lokaci daya kuma ya biyasu zuciyar Ummitah da suka lalata musu komai akanta.

Zare jikinsa yayi daga nata tareda kai bakinsa yana wani irin kuka me tsananin gaske mara sauti yayi kissing goshin jannah din ya rufe mata jikinta da doguwar hijab dinta tareda ciro dukkanin abinda yake jikinsa na dan kudaden dayake gararin samu ya ajiye mata ya fice daga dakin tareda rufewa ya bar gurin yayi tafiya me nisa kafin ya samu guri ya shige ya zube qasa yana wani irin gunjin kuka har asuba tukuna ya fito ya wuce yabar anguwar gabaki dayanta.

Karfe 7 na safe tafara bude idanuwanta ahankali tana motsawa,

Nauyi idanuwan sukai mata dan haka ta maidasu ta rufe kafin ta sake budewa tana motsawa ahankali ta tashi zaune tana duba gefenta taga bataga saleem dinba,

Bude idanuwanta tayi sosai tana duba dakin taga bata gansa ba,

Miqewa tsaye tai jiri dibarta ya zubar qasa,
Bata damuba ta sake dafawa ta miqe tana nufar kofar ta bude tareda fitowa tana waiwayan koina,

Waje gabaki daya ta fita tana dafe kirjinta ahankali dayayi nauyi ta tabbatarda dai Saleem ya tafi kenan...

Faduwa tayi kofar gidan zaune tana cusa kanta cikin kafafunta kirjinta na zafi da nauyi kuka ya kasa zuwa kwata kwata.

Tana gurin har rana ta fito sosai ta kasa motsawa sai daga baya ta iya daddafawa ta koma ciki ta zauna gaban kudin daya bar mata ta zuba musu ido batareda ko kyaftawa ba.

A ranar kasa zuwa headquarters tayi sbd zazzabi me karfin gaske tareda ciwon zuciya dayake neman taso mata.

Sai washe gari ta shirya kamar almajira ta nufi headquarters gurin ganinsu dad wanda daqyar aka bari ta gansu.

Ganin yanayinsu ya sakata fita ta siyo musu bread da lemu da pure water ta kawo musu daqyar aka bari suka ci
Sunaci tana kallansu tana hawaye masu dumi batareda sun cewa juna komaiba musamman dad da baya gani sosai.

A haka ta wuni can sai dare ta dawo tai sallah ta kwanta shiru ba motsin komai.

Sati guda tayi tana yawo gurinsu dad kafin aka fara shiga kotu dasu inda lamarin ya dauki zafi sosai basuda lawyer basuda me tsaya musu hakama itama dukkanin abinda take dashi a yanzu ya qare tsaf ko sisi batada shi sai yawo da busashen baki.

Dan haka ta maida hankali sosai gurin addua da fadawa Allah ya duba lamarinsu yaji qan ahalinta yayi musu mafita a wannan case din.

*******
Tsananin kusanci da Kauna tareda shaquwar datake tsakanin Dr Nico da AZIZ LIMBA ne ya saka wannan karan dole ya tattar yabaro Italy ya dawo Germany sbd shine likitansu daya zama family hakama ya zama tamkar da a gurin mama tin ba yanxu ba daman.

Shine ya fara tarewa a Germany kafin isowansu dan haka koda suka iso ya kwana biyu sosai a qasar.

Dr Nico tin lokacin Jinyar AZIZ LIMBA a lokacin rasuwar Ummitah shine ya kasance wanda yafi kowa sanin girman depression da trauma din daya samu kansa aciki sbd shima Yanada kanwar da ita kadai garesa bai hada komai da itaba,

Mum dinsu yar Africa ce yar asalin Ghana wadda bayan ta rabu da Dad dinsa ta koma qasarta ta ghana tai aure ta haifi qanwarsa wadda agurin haihuwarta ta rasu kuma tin daga lokacin kanwarsa ta dawo hannunsa,
Chapter 113 · 0% Book details