← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 120

Sashe 47

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zaa dorata akan activities da zaa fara kiyayewa da dorata akai tin yanzu batareda an daga mata hankali tasan meyake damuntaba dan tayi qanqanta data san hakan kuma sbd Nata baiyi nisan da zaa cire rai ba sedai kuma bamusan abinda gaba zatai ba wadda idan har ankai stage din da baaso to sai anyi mata heart transplant din wanda samun donor shine abinda yakeda wuyar datafi komai a duniyar nan"

Hotuna da videos na yanda ake heart transplant ya kunna yana cigaba da musu bayani cikin kwantar musu da hankali da kokarin ganin ya fahimci komai tareda sanin ba wani abu ne me mugun tashin hankaliba sbd ciwonta baiyi nisa ko girman da zai gagaresuba insha Allah.

Sayd dagowa yai ahankali daga jinginen dayake yana saukar da idonsa da kyau akan hotinan dake yawo akan babban screen din na heart transplant da asalin tabon dayake bari a kirjin da duk aka cire zuciyar ko dasata.

Kasa dauke idanuwansa yayi daga hoton wanda ya saka kunnuwansa daukewa daga jin sautin bayanin da doctors keyi sbd mamaki me tsananin gaske da shock dayake neman shigarsa sbd sanin wannan shine irinsa sak a kirjin Ummitah wanda bai taba saninta dashi ba dan ko ranar da zaa kaita asibitin haihuwa shine ya saka mata kaya da kansa dan bazata iya ba kuma babu wannan dinkin a kirjinta sai bayan rasuwarta ya gansa.

Juyawa kansa ya farayi sedai kuka Cs akai mata aka ciro Falaq,
Ana cs na haihuwa a kirji ne??
Girgiza kansa yayi idanuwansa na sauyawa yana kokarin tina babu dinkin cs da akai mata a mararta.

Jin yayi ya dena gane komai kansa na yin dum..

Jajayen idanuwansa da suka sauya gaba daya a take ya kalli dr Raheem ya bude bakinsa muryansa a shaqe yace

"Dr a wane gefe na kirjin ake aikin?
A jikin dan adam akwai inda zaa iya masa tiyata a cire 'da bayan cikin?
Meye dinki a kirji kuma a bangaren hagu yake nufi??

Kallansa dr yayi yana mamakin tambayarsa
AY kuwa sam bayama cikin cikakkiyar hayyacinsa na fahimtar me Sayd din yake tambaya yana zaune shiru idanuwansa sunyi laushinda ayau zaka gane rauninsa a bayyane.

Cikin bude masa komai da kyau dr yace

"Babu inda ake iya cirewa mace baby bayan cikinta maana qasan cikinta wanda wasu ana yankan tsaye wasu kuma na kwance,amma idan har kana magana ne akan wannan yankan na setin zuciya wanda ya tafi daidai irin wannan da kake gani to idan a jikin rayayye ne akwai tabbacin antaba masa aiki a zuciyar, idan kuma matacce ne to tabbas shima anyi masa aikin ne a zuciya kokuma ma an cire zuciyarne tinda a macen yake"

Jiri ne ya dauki Sayd daga zaunen da yake sbd kansa kasa gane komai yai
Jin yake kamar bai taba zama aji karatu ba sbd jin yayi turancin ma kamar ya dena ganewa dan haka ya juyo idanuwansa da sukai nauyi sosai ya kalli AZIZ wanda shima kwata kwata jinsa yai qasa akan bayanan likitocin gameda ciwon daya bayyana lokaci daya a tattareda rayuwar yarsa wadda bayan kuruciya ma yanzu babu abinda zata gane a ciwon ko anmata bayani.....

"Innalillahi wainnna ilayhi rajiun,Ya salam"

Ya fada yana tallafe goshinsa da hannuwansa biyu idanuwansa na rufewa ya budesu tareda jimawa shiru kafin ya dago ya kalli kowannensu ya bude baki baki yayi musu godia tareda miqewa.

Sayd ma miqewan yayi baa hayyacinsa ba sbd yayi mugun zurfi da nisa da tinanin dayake sake toshe kansa.

Ta email akaiwa Sayd forwarding copies na results dinta da sauransu sbd duk inda zasu sauya ganin likita ko qasar ma zai zamana sunada record dinta.

Tafiya suke babu me magana hakama babu wanda yake cikin cikakkiyar hayyacinsa har suka isa mota suka shiga kowannensu yayi shiru.

Sayd kasa tada motar yayi sbd bayajin zai iya driving cikin daurewa ta juyo ya kalli LIMBA da babu abinda yake iya cewa sai yaji tsananin tausayinsa dan ganin rauninsa da karyan kowa ne yace ya gani.

Jin yayi jarumtarsa ta dawo dan shine tamkar bangon dayake taresa a duk lokacinda rauninsa ya taso dan haka yake koyaushe a shirye daya basa kariya koda shi zai rasa nasa ran sbd kaunar Ummitah data hadasu haduwa ta har abada.

Numfashi me sanyi da ciwo ya sauke yana dora hannunsa ya tada motar yana tattaro nutsuwa da karfin hali ya hau hanyar gida.

Tafiya ce ta damuwa da rashin haske ko kadan a cikinta sukai har suka isa gida..

Suna isa kai tsaye babu wanda ya gansa ya shige bangarensa ya rufe kansa sai alokacin yaji kirjinsa nai masa radadi da ciwon daya sakasa zubewa palo qasa yana dafe kirjinsa yana lumshe ido yana karban radadin sbd babu yanda zai iya dauresa.

Yana jiyo ihun falaq din da Fiddausi da dayar me aikinsu a baya suna wasan daya sakasa rintse idanuwansa yana jin inama shi Allah ya kaddarowa wannan ciwon ba Falaq ba sbd harko yaushe yana fatar kasancewa da Ummitah koda a fatalwa ne idan har zasu hadu.

Falaq ce jinin Ummitah daya rage masa a duniyar,
Falaq itace take rage ciwon radadin rashin mahaifiyarta daya bar zuciyarsa empty idan har ciwonta barazana ce ga rayuwarta da zata iya rasa zuciyar da itace rayuwar yaya zaiyi da wannan kaddarar da Allah daya kaddaro masa shi kadai ne zai kawo masa dauki...

Zuciya ce zata buqata idan lokaci yayi wanda ba aba bace da tarin dukiyarsa zata siya,
Meye amfanin kaf abinda ya mallaka idan har bazasu nemo masa abinda zai buqatan ba?

Falaq dake wasan ruwa da water guns dasu Fiddausi farin ciki kawai take jin kanta yana ciketa wasa sukeyi sosai batama san daddynta ya dawo ba kuma yana jiyota radadin zuciyarsa na qaruwa duk dariyarta ta shiga kunnuwansa sbd ahankali ahankali wannan farin cikin da dariyar zasu disashe daga rayuwarsu kenan.

Sai magrib suka dena wasan suka dawo ciki Fiddausi na janta daki ta sakar mata ruwan zafi sosai sbd sanyin da sukai wasa dashi karya kamata.

Cikin jallabiya milk me tsadar gaske ya fito fuskansa tayi fresh sbd wankan da yayi ya fiton,.

Fuskansa babu walwala ko kadan sedai sam fuskansa bata bayyanarda fushi,

Sayd ne shima ya fito sanyeda riga da wandon fendi masu haske suka nufi masallaci wanda saima anyi tafiya da mota ake zuwa.

Koda sukai sallan magrib basu dawoba a masallacin suka tsaya AZIZ din karatun AlQuran ya ringa yi har lokacin isha yayi akai sallah suka fito suka kamo hanyar zuwa gida.

A hanyar ne ya dan kalli Sayd din a natse kafin ya maida kallansa kan Wayarsa yace

"Kafin gobe a saka binciken qwararrun manyan likitocin zuciya na duniya gaba daya zan gansu"

"Yes AY" Sayd ya fada yana ciro wayarsa dan fara saka binciken.

Suna isowa gida ya nufo ciki yana sako kai falaq dake fitowa hanyar bedroom din mama da gudu tayo kansa tana murmushin farin cikin ganin halittar datafi mata kowa da komai tana cewa

"BestDaddy"

Rungumeta yayi yana sauke boyayyar ajiyar zuciya da wani lafiyayyar murmushi daya sakawa fuskansa wani irin sabon nutsuwa da kwarjinin gaske.

Sayd bai qaraso ba bedroom dinsa ya nufa yana wayoyi..

Yana gama wayar ipad dinsa da tinda suka dawo asibiti yake kai yana wani irin binciken dayake neman juyar masa da kai,

Gaba daya zarewa yake neman yi kawai daurewa yake sbd kada AZIZ yasan komai akan abinda baida tabbaci amma kuma ya tabbatarda dinkin kirjin Ummitah sabo ne kuma a asibitin data haihu ta samesa sbd ya sake tabbatar da cewan ranar da zasu tafi da ita koda ya saka mata kaya a jikinta babu raunin komai a jikinta bare dinki,

Kuma a yanzu bayan dawowansu ya rufe kansa a daki ya kira likitocin duniya sunfi goma zance daya suke basa akan abinda dr Raheem ya fada baa taba aikin komai a kirji kuma bangaren hagu saina zuciya hakama indai mace ta haihu babu alamar tiyata a qasan cikinta koda daga gefe ne to da kanta ta haihu ba cs akai mataba.

Dafe kansa yayi dayake juyawa yana neman zare masa idanuwansa sukai jajir,

A ranar da aka shiga cs da Ummitah babu kowa a bangaren kaman yanda babu ko hayaniya alamar kebantaccen guri ne dayake nuna alama da vip area ne na asibitin,
AZIZ baisan suna meyake faruwa ba bare yasan asibitin dasuke bare yasa a basu special treatment hakama Alh Saad baisan suna asibiti a lokacin ba sbd basu tsaya sanar da kowa ba sbd tashin hankali,,,,to meyesa aka kaisu Vip area din????

Ko sisinsu baa karba ba idan ya tina harsuka bar asibitin da gawar Ummitah........

Miqewa yai da sauri ya nufi windon dakinsa ya bude iska ta daki fuskansa ya rintse idanuwansa sbd sarqewa numfashinsa keyi yana neman zaucewa...

Iska ya shaqa numfashinsa ya dan dawo daidai ya dawo da sauri ya wafci ipad dinsa yana sake bin bincikensa daki daki sedai yasan shedan ne kawai keson illata zuciyarsa da tinaninsa dan babu yanda zaayi ace anyiwa Ummitah aikin zuciya basu saniba,

Kodai dataje rasuwa ne sukai kokarin hana zuciyarsa dena aiki sukai mata aikin zuciyar??

Me wannan tinanin yakeyi a kansane??
Menene yake damunsa?
Wane irin jahilin tinani ne wannan yake yawo akansa??

Laptop dinsa dake bude itama yana binciken da ita ya duk ya rikice yayi da wayarsa yayi da ipad yayi Laptop ya kira waya duk ya neman haukacewa yake neman yi......

Cikin wani irin zafi ya dauki Laptop din ya bugata da qasa yana yana dafe kansa tareda zubewa a couch yana rintse idanuwansa hannuwansa na dan rawa.

Numfashi yake saukewa da karfi karfi yana sauka ahankali yana kokarin dawowa daidai hayyacinsa.

Bude idanuwansa da sukai ja yayi Ahankali yana dawowa da tinaninsa daidai..

Akan tinanin Abinda yake shirin faruwa tinaninsa ya tsaya da hankalinsa..

"Bayyanar ciwon falaq na Bayyanar musu abinda basu sani bane ko me?
Kaddara ce ko Haske ne yake buduwa a garesu??

Numfashi ya sauke tareda miqewa ya fada toilet yayi wanka kansa ya dan sake alokacin ne ya shirya ya fito sallan magrib da suka fita da LIMBA.
Chapter 47 · 0% Book details