← Book details Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 120

Sashe 79

Kalbima Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amsawa yayi yana rungumesa batareda komai a ransa ba yace

"Yaya muka sameku?

Anny ma Mimi ta rungume tana musu barka da dawowa kafin suka qarasa ciki gabaki dayansu.

Falaq ma fitowa tai da murnanta taiwa Mimi oyoyo tana rungumeta.

Cikeda kauna Mimin ta rungumeta tana cewa

"Falaq yaya kike?
Yaya baqunta?

Murmushi tai tana amsawa tana sake musu sannu da zuwa.

Fiddausi da sauran yan aikin gidan fitowa sukai suna musu barka da dawowa.

Da daddare bayan kowa ya nutsu ya huta suna kan dining suna cin abinci Jannah data iso tareda falaq din kallansu kowa yayi cikeda tausayin Jannah,

Zama sukai suka fara cin abincin Ammar ya kasa samun nutsuwan ganin abincin da Jannah zataci dan haka da kansa ya miqe ya sake serving nata wani abincin sbd gaba daya ta zabge kamar bata cin abinci.

Cikeda kulawa yace

"Kici wannan you don't look good"

Thank you" tace tana murmushi.

Falaq data kasa cin abincinta tana kallansa jin tai gabaki daya cikinta ya cika dan haka fasa cin abincin tai ta miqe tabar dining din.

Babu wanda yace komai hakama dukkaninsu jannah suka zubawa ido suna kalla.

Batace komaiba itama hakama bata dagoba tsawon mintina 2 sai sukaga ta miqe tana bin bayan Falaq din.

A tare dukkaninsu suka sauke ajiyan zuciya mara dadi banda Ammar da baqin ciki da takaici suka rufesa ya miqe yabi bayan Jannah din dakinta.

Tana shida dakin daidai fuskansa na bayyana akan screen din ipad din Falaq data saka kiransa video call.

Ta bayanta jannah din ta bayyana Ammar na bayanta zai miqa hannu ya riqota Muryan AZIZ din ya bayyana yana ambatar sunan falaq
Dukkaninsu Screen din suka kalla Ammar na kasa motsawa hakama jannah din falaq ma juyowa tai ta kallesu ganin inda Daddyn nata yake kalla taga Jannah da Ammar a tsaye.
#MAMUH

ZAFAFA BIYAR

KALBIM 500
mamuhgee

A DUNIYATA 500
Huguma

AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

Pay at
0022419171 AccessBank
Maryam sani gummi

Shedan biya
09033181070

Or mtn vtu at
09032345899
*_KALBIM_*
_Mamuhgee_
64
*UMMU_MAHNOOR LUXURIES*
(Best luxuries shop)
08034469681
08135142610
Aslm Alaikm ina kuke masu neman luxuries na kayan alfarmar kece raini?
Ina masu son su saka sitirar alfarma ta zamani ta manyan mata masu aji da zaa kalleki kallo daya asan sitirar alfarma e kika saka?

Shin kunsan me ake nufi sa kayan asalin yan gayu da nuna gayu?
Sitirar Alfarma kikeson sakawa?
Sitirar da kike ganin manyan mata da ita?
Sitirarda zakiyi gayun sallah dake da yaranki a dauka waje kikaje da kanki kika siyota?
To kizo ga damarki ta sameki sbd UMMU_MAHNOOR LUXURIES ta kawo miki sauki har gida,
Karkice se masu kudi ke iya siya har kema me yar dama zaki samu naki da saukin kudi kuma best quality da kalar zamani data yan gayu,

Nidai Mamuh nace duk wadda ke son a buga gayun sallan bana da ita da 'yayanta to tazo gurin UMMU_MAHNOOR LUXURIES tai siyayyar sallanta harma zuwa gaba dan nasan zakuji dadi da fahimtar abinda nake fada akan kayanta💯💯
Abubuwan da zaki samu a gurinta with the best quality na wayayyun mata masu aji yan gayu sune;

Atampopi
Laces
Shadda
Materials
Shoes
Bags
Veils
Trolleys
Jewellerys
Oil perfumes

Numbers
08034469681
08135142610

Handles
Instagram @ummu_mahnoor_luxuries
TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries
Facebook ummu_mahnoor_luxuries

*************
Dauke idanuwansa yayi akansu tareda maidawa akan 'yarsa yana kallanta ya bude baki yana jingina bayansa a sofan dayake zaune cikin free size balenciaga shirt da three quarter fuskansa ta qara haske sosai a natse yace

"Yaya nake ganin fuskanki da damuwa?
Akwai abinda yake damunki?

Juyawa tai ta saci kallan Ammar dayake bayan jannah zuciyarsa na tafasa ta dawo da kallanta kan jannah datai sanyi
Sai taji tausayinta me tsanani ya rufeta dan haka ta dawo da kallanta kansa ta girgiza kai alamar ba komai.

Ammar ya jefawa kallan dayafi kama dana mutum ne ko aljan kafin ya dawo da kallansa kan Jannah din batareda ya ambaci sunanta ba yace

"Meya sameta?

Nunfashi ta fara saukewa a sanyaye kafin ta dago ta kallesa tana danne damuwarta tace

"I dont know kawai ta fasa cin dinner ne"

"Akwai abinda kukai mata ne datai loosing appetite nata,
So me kike jira da bazaki mata dubarn da zataci ba?
Kunason ta kwana da yunwa ne?
Idan akwai specific abinda taji tanason ci a nema mata a bata mana,
Komai sai anfada miki yanda zakiyi¿
You ar unbelievable...." ya qarasa fada yana kashe wayarsa.

Ammar daya mutu a tsaye sbd tsananin mamaki da tashin hankali da baqin cikin baisan lokacinda ya kalli jannah da zuciyarta ke mata ciwo ba yace

"Is he okay?
Like is this Guy normal?
Yasan waye jannah zad kuwa?
Yana wasa da rayuwarsa ne?
Haka yake treating naki duk tsawon lokacin nan?

Juyawa Jannah tai batareda tace komaiba tabar dakin sbd Falaq sam bata kaunar ayi maganar Daddynta da daga murya bare rashin girmamawa ko cin fuska haka dan haka ta fice dan tasan zai biyota ne.

Suna isowa babban palo ta dakata tareda juyowa ta kallesa ta bude baki cikin damuwar datake ciki tace

"Meye kakeyi hakan a gaban Falaq?zata iya kwana tana kuka and hakan zai iya sakata wani ciwon da zai..... kasa qarasawa tai tana hadiye sauran zancen da damuwarta idanuwanta na sauyawa.

Cikin zafi da baqin ciki mai tsananin gaske Ammar ya daga murya yana cewa

"Idan yana taqama da yana tsananin kaunar 'yarsa bai hadata da komai da kowa ba to mun dade da wucesa a gurin sbd har abada bazai iya abinda mu mukai akanki ba,
Me zakiyi da aurensa idan har tin kina gida a gabanmu yana miki hakan?
Meye a cikin aurensa?
Meye zakiyi dashi?
Meyasa kikai shiru kina hadiye wulaqancinsa?
Why,why Jan?

Wani irin nauyi da tsananin ciwo ne ya toshe zuciyarta hawayen datake riqewa suka gangaro mata ta rintse idanuwanta tana jefawa zuciyarta itama Why ta kamu da tsananin sonsa irin hakan,
Da zata iya bawa Ammar amsa data fada masa menene yake azabtar da ita.

Gabaki daya su Dad da hayaniyar ta kawosu palon tsayawa sukai suna kallan hawayenta dake sauka zuciyoyinsu na radadi da ciwo tareda jin auren kwata kwata ya fita ransu a yanxu yancin yarsu kawai sukeso.

Bude idanuwanta da sukai jajir tayi taga irin kallan da suke mata ta juya batareda ta tsaya jin abinda zasu fada ba ta nufi kitchen sai ganinta sukai ta fito dauke da tray ta wuce zuwa dakinta.

Saleem ne ya isa gurinta ya karbi tray din yana cewa ta kawo ya daukan mata cikeda kulawa da kaunarta me tsanani.

Dad bai iya cewa komaiba palonsa ya wuce
Maheer ma nasu palon ya wuce Anny na gefensa riqe da hannunsa.

Mimi Ammar dayake jin kaman zai kama da wuta ta nufa ta kama hannunsa tana maidasa dining ta zaunar tanason yaci abincin amma sam bai iya ci ba idanuwansa sunyi wani irin jajir maganganun da LIMBA ya fadawa Jannah suna yawo a kunnuwansa.

Suna isa daki falaq suka tarar a zaune idanuwanta sunyi jajir alaman kuka tayi tana ganinsu ta zubawa jannah ido da itama idanuwanta suka nuna kukan tai
Take taji jikinta ya sake sanyi.

Tashi tayi ta nufo Jannah din sedai kafin tace komai jannah ta kama hannunta tana kokarin sauya yanayinta ta zaunar da ita a sofa tana cewa

"Zo kici abinci"

Girgiza kai falaq tai tana cewa

"No kema bakici ba"

Saleem daya ajiye tray din akan table din gabansu cikeda kulawa garesu su biyun yace

"Dukanku zakuci abincin ai yanzu dolenku"

Kallansa Falaq tai tana sanyi tace

"Idan jan zataci zanci,
Idan bazata ci ba nima bazanci ba"

Murmushi ya sake yana kallan falaq din kafin ya kalli jannah yace

"Your baby tace bazata ci ba idan bazaki ci ba so Ms Jan limba me kikace??

Kallan falaq din tai tana sauke ajiyan zuciya ta miqa hannu tana cewa

"Zanci"

A tare sukaci abincin shikuma saleem din yan kokarin sauya yanayinsu har suka sake suka dawo walwala da dariya.

Har kusan 10 da mintina yana dakin har saida ya tabbatarda sun gama dawowa cikin farin ciki tukuna yai musu saida safe ya fice.

Harya fito duk tsawon wannan lokacin Mimi da Ammar na palo zaune zuciyoyinsu ba dadi dan haka ya sanar dasu komai ya daidaita sun dawo walwalwansu duk su dukan.

Yar ajiyar zuciya Mimi ta sake tana juyawa ta nufi dakinta

Ammar kuwa ko sunan Falaq din jin yayi baya kaunar sake ji dan haka shima barin palon yayi ya nufi bangarensa yana jin kaman ya dawo da rayuwarsu baya ya goge shigowan AZIZ LIMBA rayuwarsu ya hana haduwansu dashi kwata kwata.

Wanka Falaq tafara yi tai shirin bacci ta hau gado ta dauko ipad dinta lokacin jannah na cikin toilet gurin wanka ta saka kiran Daddynta.

Daman kiranta zaiyi sbd tabbatarda taci abinci bata kwana da yunwa ba.

Zaune yake a bedroom dinsa shima sanye da fararen kayan bacci ya dora Cardigan akai me girma sbd yanzu ya gama conference meeting da wasu presidents dinsa na U-LIMBAs companies.

Cikin kulawa da sakewa tareda kauna take sakin murmushinta me kyau sbd yasan ta dake bata cikin damuwa dan kada yayiwa Jan dinta fada tace

"Daddy naci abinci tareda My jan kuma bana cikin Damuwan komai yanxu"

Hancinta ya kalla fuskan Ummitansa na bayyanar masa akan fuskanta ya saki wani Kyakkyawan murmushi yace

"Thank god Besty zaiyi baccin nutsuwa kenan tinda falaq Aziz taci abinci"

Dariya tayi sosai kafin tace

"Daddy pls ka dena yiwa my jan fada ni banaso,
Banason tayita kuka,
Koyaushe kayi fada sai tayi kuka sosai,
Ka ringa rarrashinta nakeso kaman yanda kakemun,
Kaji???

Bakinta dayake maganar ya kalla kafin ya basar yana cewa

"Ki fadamun abinda ya sameki tukuna"

Mantawa tai da tace bazata sake nuna masa damuwanta anan ba ko fada masata gyar zama tana turo baki tace
Chapter 79 · 0% Book details