Sashe 97
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ta kashe wayar tana kyalkyala dariya. Kafafunta sukayi sanyi kalau da kyar take jansu ga ciki tirtsitsi a gaba ta iske inda yake tsaye da turare a hannunsa. Wani irin yanayi ya shiga ganinta cikin muguwar damuwa! ya riga yaji komai matar abokinsa ta fasa k'wan wanda dama yana shirin fasa shi a ranar. Hannuwansa ya bude tana zuwa ya rungumeta yana shafa gadon bayanta cikin nutsuwa yasa bakinsa a kunnanta ya sanyayyar da murya a hankali yace." Ta fada miki zanyi aure ko."? Kanta ta dago tana kallonshi kafin tace." Tayi min jirwaye dai! nasan dama akwai wannan ranar tunda kasha fada min cewa kana da burin auran mata hudu to amma me yasa ka boye mana ai wannan munafurci ne." Yaji haushin kiranshi da tayi munafiki, amma sai ya danne yace." Ki dinga tausasa harshenki gurin yi min magana ban ji dadin wannan kalmar da kika kira ni da ita ba." Tayi saurin cire jikinta daga nashi, tana masa wani irin kallo kafin tace." To wane suna ka dace dashi? shin idan ka sheda mana cewa za kayi aure zamu hana kane."? Ya daga mata hannu da fadin." Ya isa kada ki zage ni."! Ya zuba masa rikitattun idanuwanta dake cike da fitina! Ya duba agogon dake daure a hannunsa, lokaci ya kure babu damar ya tsaya yi mata dogon bayani, kawai ya kama hanyar fita ba tare da yace mata komai ba. Da sauri ta tare masa hanya duk ta firgice kamar yau ne ranar da aka farayi mata kishiya. "Wacece wacce zaka a ura."? Wannan tambayar tayi masa. Sai kawai yaga babu amfanin jayayya a tsakaninsu, tunda ta bukaci sanin ko wacece bari kawai ya sheda mata ya wuce gurin. " Kayi shuru kana kallona ga alama baka da gaskiya." Ta sake narka masa wata bakar maganar. 'Bacin ransa ya danne kafin ya daidaita kansa yace." Nabila ce." Wani irin murda cikinta yayi jin sunan wacce ya kira, a take gabadaya jikinta ya kama rawa!! "Nabil.....Nabila wacece haka."? Ta tambayeshi idonta a tsaye a kansa. Kauda kansa yayi kafin yace." Yarinyar abokina Asp nasan yanzu kin gan......Kafin ya karasa maganar ta daddage ta kurma ihu! tana rike kanta! "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! ya kira kafin yay gaggawar rike ta yasa a jikinsa, cikin dakin suka koma tana ta tuttureshi yana sake riketa, wasu mugwayen hawaye ne suke ambaliya a fuskarta. Yaji zuciyarsa tana nema ta karye koda yayi yunkuri tashi ya tafi aiki sai ya kasa, bayaso ya fita ya barta cikin wani hali. Ta dinga kuka tana kallonshi! bakinta sai rawa yake tsabar tashin hankali da mamaki ya hana ta magana. Shima nasa idon yana kanta gabadaya jikinsa yayi sanyi ya rasa da kalmomin da zai rarrasheta. Sai kawai ya cire kakin jikinsa ya nemi guri ya kwanta baya tsammanin zuwa gurin aiki a cikin wannan yanayi. Murya a dashe tace." Dama can kai kake neman auranta shine saboda munafurci ka boye min har da cewa da kai aka kar'bi kudin auranta." Ya tashi zaune yana kokarin tarairaiyota jikinsa ta janye ta matsa can gefe har yanzu kukan take tana masa wani irin kallo na ba kayi min adalci ba. Murya a raunane yace." Bani bane daga baya Allah ya juya al'amarin kaina Zinatu ki nutsu nayi miki bayani abinda ya faru." Hanci taja ba tace komai ba kawai ta zuba masa ido tana sauraransa. Ya sake raunana murya tunda ya gane hakan da yake yana saurin kassarata shiyasa ya mayar da hankali.........Cikakkenan bayani yayi mata yanda zata fahimta sosai ya kuma shigo da maganar bazawarsa wacce da yake neman auranta a boye ya dora da fadin." Dalilin faruwar wannan al'amari na janye auranta ba don bana sonta ba, sai dai domin na rufawa abokina asiri, kuma ni a ganina auran Nabila ba matsala bane a tattare damu bakid'aya! a matsayinki na uwargida nake neman alfarma a gurinki cewa ki kwantar da hankalinki kada kiyiwa al'amarin mummun zato! kisa a ranki cewa babu yanda Allah baya juya alamarinsa! inaso kuma ki sani cewa har yanzu matsayinki na nan a cikin zuciyata, babu wata mace da zan aura da zata fiki matsayi a gurina, samun zaman lafiyar gidana yana tattare dake, gabadaya kece zaki wanzar da samuwarsa idan kinyi min haka kin gama min komai wallahi. Gabadaya jikinta ne ya mutu, maganganunsa sun kassarata mata jiki! ya fita gaskiya! ta ko'ina, kuma bata da wata hujjar da zata ha nashi auran yarinyar, idan ta cika 'yar halak to yana da kyau ta marawa mijinta baya, ma'ana ta bashi goyon bayan auran Nabila dalilin mutunci da karamci da dattakon Asp yafi karfin komai a gurinsu, wannan dalilin yasa zuciyarta tayi sanyi ta amince da auran, babban farin cikinta, yarinyar tana da tarbiya kuma tana ganin mutuncinta, amma dole ta sake jadadda masa cewa ya ja mata kunne tun kafin ta shigo gidansu a tsare yake basa bukatar wani tsari nata kawai tazo bi shine kwanciyar hankalinta. Da yake neman kwanciyar hankali yake a gidan nasa yace." Insha Allah ta kwantar da hankalinta babu wata matsala da zasu samu da yarinyar, amma dai duk da haka zai sake jadadda mata cewa dole ta basu girmansu. Sai daf da sha biyu ya tafi gurin aiki. Asp ya sameshi a ofis yana duba wasu takardu suka gaisa a tsanake kafin ya sheda masa cewa Yarinya fa ta amince sai dai fatan zaman lafiya da juna. Yayi farin cikin jin haka daga gareshi godiya ya shiga yi masa bakinsa kamar gonar audiga, shi kuwa Asp din da yake akwai barkwanci sai ya shiga tsokanarsa yana kiransa da ANGO! sai washe baki yake suna tsokanar junansu kamar ba surukan juna ba. **** A daran itama Hamra'u ya sheda mata abinda ke da akwai, aikuwa basu rintsa ba, dan kwana tayi tana kuka da rokonsa ya janye auran! kada ya kawo musu wacce zata lalata musu zamantakewa. Duk yanda yaso ya fahimtar da ita abun yaci tura sai kawai ya rabu da ita ya shirya ya fita gurin aiki.........Da kyar Uwale da Zinat suka fahimtar da ita, sai daga baya itama ta gane cewa Asp ya wuce haka a gurinsu. A cikin kwanaki biyun da suka rage soyayya ce mai karfi ta kullu a tsakaninsu, A waya yake kasheta da kalamai tun tana jin kunya da nauyi har ta sake itama ta fara mayar masa da martani. gabadaya idonsa ya rufe ya manta shaf da cewa ita din fa yarinyar abokinsa ce, koda yake ai NAMIJI ba abun kunya ne a gurinsa. A na gobe daurin aure yaje har gidan Asp din da sunan zance a cewarsa yana so su tattauna da amaryarsa. Asp kunya ta kamashi kawai sai ya girgiza kai domin al'amarin abokin nasa a yanzu mamaki yake bashi. Dabararsa ta zuwa shine ya jadadda mata manufarsa cikin wayo da dubara yake nuna mata zamantakewar gidanshi cewa tayi hakuri da matanshi ta kuma dauke kai akan duk abunda zai faru, duk abunda ta tarar a gidan tabi mutukar bai sa'bawa sharia ba, insha Allah shi kuma yayi alkawarin kwatanta adalci a tsakaninsu. Taji dadin bayaninsa domin munafikin namiji sam beyi ba a rayuwa, da alama shi wannan daban yake a cikin maza. Nan ta tabbatar masa da cewa insha Allah tayi alkawari daga 'bagaranta wata matsala ba zata faru ba.......! *Wannan shine karshen labarin GOJE! ina rokon Allah ya yafe min kuskurena.....Allah kuma yasa a amfana da abunda na rubuta! Allah yasa damu da alkairi masoya NAGODE sai mun sake haduwa daku cikin wani littafin nawa mai zuwa da yardar ALLAH* *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* Times New Roman Times New Roman !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office 166358e7e4764345849e753b72da8c8f