Sashe 24
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da take jin kamar taje ta sha'ko wuyansa ko uwar me yake a dakin oho! A cunkushe! ta kalli Asp din da fadin " Ranka ya dade ya kamata mu tashi mu tafi wannan mutumin ya mayar damu shashashai! ya shige daki ya bar mu a zaune zaman jiransa." Ya kalli agogon dake daure a hannunsa da fadin." Hakane nima nayi mamakin jimawarsa amma bari na kira wayarsa naji." Uwale kuwa gyangyadi take bata ma san ma abunda ke faruwa ba. Yana kokarin kiran wayar tasa, suka fito a tare hannunta na cikin nasa. Har suka zauna bata kallesu ba, cika kawai take tana batsewa! wani mugun abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya. Gwiwa a kasa Hamra'u ta gaishe da Asp, ya amsa da fuska a sake yana janta da wasa, murmushi kawai take ta kasa hada ido dashi, gabadaya farin ciki ya mamaye zuciyarta, tayi mamakin yanda akayi ya santa har yake kiranta da amarya hakan ya sanya ta sake gazgata maganarsa. Tashi tayi kawai ta kama hanyar fita ba tare da ta tankawa kowa ba, Nabilan ta kalli mahaifinta nata da fadin." Daddy bari muje kawai sai ka shigo." Ya mike da fadin.'' Aa ku jira ni mana saurin me kuke." duk da taji abunda yace hakan besa ta tsaya ba, ta bude kofa ta fita, ita Nabilan ita ta jira mahaifin nata har sukayi sallama cikin girma da mutunta juna. ***** Washe gari da wuri suka shirya tafiyar, bahaushe yace sabo turken wawa, 'yan kwanakin da tayi a tare dasu ya sanya duk jikinsu yayi sanyi har dashi Asp din kawai ya daure ne domin ya san dole watarana yarinyar zata bar hannunsa, Madam dai kasa hakuri tayi sai share hawaye take a fakaice. Al'amarin ya bata mamaki mutuka! ta rasa wane irin so matar take mata, gabadaya sai jikinta ya mutu ta rungumeta da fadin." Mommy kiyi hakuri ba mu rabu da juna ba insha Allah zan dinga ziyartar ki, bayan haka kuma zamu dinga gaisawa ta waya ki daina kuka." tana maganar tana share mata hawaye. Hannunta ta rike da fadin" Idan kin isa gida lafiya kice ina gaishe da mamanki kuma insha Allah idan an kwana biyu zamu kawo muku ziyara dani da Nabila." A sanyaye tace."To shikkenan in Allah ya yarda zan sheda mata sa'kon ki daga zarar na isa ." Nabila ta fito daga daki ta same su cikin damuwa, a sanyaye ta zauna kan kujera tana kokarin magana ya k'araso gurin yana duba agogon dake hannunsa, ya kalleta da fadin." Tashi muje ko." Ta mike tana gyara mayafin jikinta, Nabila ta kalleshi da fadin." Dady zan je nima." kai ya girgiza da fadin." Ki bari idan an kwana biyu zaku shirya zuwa keda Madam." Kamar za tayi kuka tace." Dady ni nafi so naje yau." be saurareta ba ya kama hanyar fita, itama da sauri tabi bayansa domin bata so ta tsaya dogowar magana zuciyarta ta karye, gabadaya suka bita da kallo cike da alhinin rabuwa da ita. Wayarsa ya kira ya sheda masa cewa sun fito suna jiransa. Da yake tuntuni ya shirya tafiya sai kawai ya fito daga gurinsa kai tsaye bangaran su Uwale ya nufa domin yi musu sallama. Fitowarsa ta dauki hankalinsu daga ita har Asp din......Yana sanye da kayan mu na hausawa shadda milk colour dinkin tazarce har kasa, sai yayi amfani da hula zannar bukar mai duhun zare, kafafunsa sanye da bakin takalimi mai gidan yatsa, agogon dake d'aure a hannunsa ma baki ne, yayi kyau sosai fuskarsa tayi kar! sai fitar da annuri take. Kasa janye idonta tayi daga kansa suna magana da Asp yana tsokanarsa cewa yayi kyau a cikin dogwayen kaya, murmushi kawai yayi kafin ya fara duba cikin motar, sai suka had'a ido da sauri ya janye nasa yana gyara yanayin fuskarsa, babu fara'a a fuskarsa ya kalleshi da fadin." Ya za'ayi tafiyar ne."? Asp din na 'ko'karin magana direban da zai jasu ya iso gurin, gaisuwa ya mi'ka kafin ya bude motar ya shiga Asp din yayi saurin zama a kusa dashi, ya kalleshi cike da mamakin abinda yayi wato yana nufin shine zai zauna kusa da yarinyar. Ba tare daya shiga motar ba ya kalleshi da fadin.'' Ni yafi kamata na zauna anan gurin." Ya kalleshi da murmushi a fuskarsa yace."Akwai dalilin da yasa nayi hakan kai dai kawai shiga mota mu, tafi." Ya jima yana kallonsa gami da hasaso dalilin da yasa zai ce dole ya kusanci yarinyar, ajiyar zuciya ya sauke bada son rai ba ya bud'e motar ya shiga da bisimillah a bakinsa. Duk maganganun da suke tana jinsu, itama taji haushin abinda Asp d'in yayi kome yake nufi oho! dalilin da yasa kenan yana shiga motar ta kawar da kanta tana ya mutse fuskarta. Shima bai ce mata komai ba ya mayar da hankalinshi gurin tasbihin da yake ja da carbin dake yatsan shi a ma'kale. Jefi-jefi suke hira a tsakaninsu kafin Asp din ya juyo ya kalleta da fadin." ZINATU yau sai kwanan gida ko."? Baki ta ta'be kafin tayi masa wani irin kallo mai kama da harara! kamar wanda yayi mata laifi, ta d'auke kanta uffan ba tace ba. A maimakon hakan da tayi masa ya 'bata masa rai sai kawai ya fashe da dariya yana kallonta da fadin." Ke kam kin zama hukuma! sai rarrashi abu kad'an ke tunzura zuciyarki kamar ba d'azu ki ka gama kuka ba okey mu yanzu dai ba za kiyi kukan rabuwa damu ba kenan." Ta kalleshi still dai bakin ta tabe kafin tace." Ranka ya dade meye had'a ni daku da zan zauna ina kukan rabuwa daku ni burina ma nayi nesa daku." Ya dinga girgiza kanshi yana mamakin furuncinta, yace." Ni dai na san a'iya zaman da mukayi dake banyi miki wani abu ba ballanatana ki k'ullaceni, meye duniyar ma da kuke gaba da junanku dalilin da yasa na shirya zamanku a kujera daya domin ku gaisa da junanku duka ku yafi junanku, duk da ba wani laifi kukayi wa junanku ba amma duk kun tsangwami kanku da kanku, ke ZINATU kece 'karama ya kama kiyi wa abokin zamanki sallama ki gashe shi sannan kiyi godiya akan alkairin da yayi miki wannan shine zaman duniya." Ta dinga kallon Asp din tana jin takaicin maganarsa, a maimakon tayi abinda ya umarceta kawai sai ta juya tana galla masa harara! wacce ta sanya shi juyowa yana kallonta ido suka hada hakan besa ta daina hararsa ba...........Yanayin fuskarsa kawai ya gyara ba tare da yace mata komai ba ya janye idonsa. Hakan da yayi ya 'bata mata rai sosai! wato ya ma mayar da ita mahaukaciya, tsaki taja mai tsayi ta kawar da fuskarta. Beyi niyyar kula taba amma tsakin da tayi masa yasa ya kalleta cikin shan mur! yace." Wa kikewa tsaki."? Kallon gefen ido tayi masa ta sake jan wani tsakin! ba zato! ya matseta jikin motar! lebunan ya kama ya shiga ligwigiwitasu! hawayen azaba! suka fara sauka saman fuskarta, Asp ya kalleshi da fadin." Ka kyaleta haka mana." Be kalleta shi ba ballanatana yaji maganarsa ya cigaba da ligwigwita leban! hannunta tasa kan nasa tana kokarin cirewa ya rike sosai! yace." Yau zanga karshen rashin kunyarki." Asp yace." Ka janye haka tayi kuskure tana neman afuwa." Yace."Da bakinta nakeso ta nemi afuwar idan ba hakaba to zamuje a haka ban damu ba." Asp din ya kalleta tayi wujiga-wujiga! ta shiga hannun maza! hawaye harda majina!! dariya ta kusa kubce masa ya danne ya kalleta da fadin ." Ni zan zama sheda idan zaki bada hakuri." Kanta ta d'aga alamun ta yarda. Ya kalleshi da fadin." Ta yarda zata bada hakurin ka saketa." Ba lokaci guda ya saketa ba sai da ya niyya tukkuna sannan ya saketa! kawai sai ta kifa kanta jikin motar tana wani irin kuka na tsantsar takaici da bakin ciki. Asp ya kalleshi da fadin." Baka kyauta ba, nida na had'a ku zama guri daya nayi hakan ne da kyakykyawar munufa dana san abunda za kayi kenan da ban zaunar da kai a kusa da ita ba. Ta'be baki yayi bece komai ba ya cigaba da jan carbin dake hannunsa. Motar tayi shuru na 'yan mintina 'kasa-'kasa sautin kukanta yake tashi tare da ajiyar zuciya. Asp yace." Kiyi hakuri kinji ki bar kukan kada mu sauka a haka wasu su dauka wani abu ne. Hannu ta dora saman lebanta da yayi tudu ya kumbura saboda ligwigiwatar daya sha ta kalleshi da fadin." Asp ni zaku yiwa haka ko? shikkenan yau zaku ga gatana." Asp yace."Aa ni meye laifi na babu ruwana wanda yayi laifi ai ya san kansa duk hukuncin da ya kamata kiyi masa daidai ne amma kema ki kiyaye ki dinga girmama na gaba dake." Bata iya ce masa komai ba taja mayafin jikinta ta rufe fuskarta dashi, gabad'aya jikinta laushi bakinta sai zafi yake, bata tsammanci rashin imaninsa ya kai hakaba ya ligwigwice mata le'be saboda tsabar mugunta har sai dai ya kumbura! wallahi ko za'a mutu ba zata bashi hakuri ba. Shima ganin yanda ta galabaita yasa beyi wata magana ba, yana dai jin yanda take sauke ajiyar zuciya dalilin kukan da taci, har suka isa masarautar bata sake magana ba, a maimakon tayi farin cikin dawowarta mahaifarta, kawai sai ta shiga kumbure-kumburen kiris take jira ta fashe da kuka. Maimartaba da kanshi ya fito domin yi musu barka da zuwa, direba yana parking ta bude motar ta fito, ba tabi ta kan kowa ba ta wani fashe da da kuka kamar wata kan'kanuwar yarinya taje ta rungumeshi tana shashshaka! shi kam fuskarta ya dago yana goge mata hawaye tare da rarrashinta, Aunty Maijidda ce ta jan hannunta suka nufi sashenta tare, hakan beyi wa Safah d'adi ba, ganin yanda yarinyar tayi kamar bata gansu a gurin ba, koda yake daman dole hakan ya faru tunda ita din ta kasance mai yi mata fada gami da nuna mata kuskuranta. Bata iya barin gurin ba sai da ta tabbatar da cewa an sauki bakin a guri mai kyau da kuma dukkan abun bukata. Gimbiya Aysha kuwa kunya da kawaici ya hana ta fitowa tarar su, amma tana zaune labarin abinda yarinyar tayi ya isa kunanta daga bakin 'yan uwanta Hassana da Husaina wanda su d'in ma ta