Sashe 77
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ki kai mata wannan ne kadai zai sanya na saurareki. Sai kawai ta fashe da kuka da fadin." Wallahi ni ba zan bata hakuri ba, kuma duk wanda ya fada maka cewa na tozarta ta Allah ya isa tsakanina dashi, ka tambayi Uwale itama idan zata fad'i gaskiya ai a gabanta komai ya faru! sau biyu tana gaura min mari! a fuskata amma saboda son zuciya za'a ce na bata hakuri! ni kam duk abunda za'ayi sai dai ayi ba zan bata hakuri ba." Yace." Ashe baki da mutunci dama."? Shuru gabanta sai bugawa yake! yace." Okey shikkenan tunda haka ki ka za'ba zan baki mamaki." sai kawai ya kashe wayarsa yana jan tsaki! Ta kalleshi da fadin." Nifa idan saboda ka faranta min rai kake wannan abun to ka daina, domin hakan ba burge ni kayi ba...........koda yarinyar nan tayi min laifi na hukuntata tuntuni ka dai ja mata kunne ta kiyaye! idan kuma taki za fuskanci b'acin rai." Yace." Akan hakan zan iya janye auranta sai me."? Tace." Duniya za tayi Alla wadai dakai! wane irin hallaci ne yarinyar ba tayi maka ba, ai samun nutsuwarka ka aureta, ni bani da matsala domin ban san abinda Allah ya rufe a tsakaninku ba." Yace." A da can baya ina sha'awar auranta saboda kyawawan halayenta amma yanzu duk ta fice min rai saboda d'abi'un data sauya, bayan haka kuma mutukar ba zata zauna lafiya dake ba, to kamar yanda na fada a farko zan iya janye auranta." 'Yar dariya tayi tare da girgiza kanta tace." To Allah ya rufa asiri ya tabbatar da alkairi ni dai duk wanda ya nufe ni da sharri kansa zai koma." daga wannan maganar ba ta sake cewa uffan ba, ta shige cikin bargo tana gyara lulluba, tashi yayi ya fita, minti goma ya dawo dakin, ya kashe fitila kai tsaye gadon ya nufa ya kwanta kusa da ita, kamar zai daure ya danne abinda ke cinsa, sai ya kasa ya matsa jikinta sosai yana shanshana sassan jikinta, gabadaya ya rikice jikinsa sai rawa yake ya birkito ta rungumeta yayi tsam a jikinsa yana kesses din fuskarta da wuyanta. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/19/22, 15:08 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *113&114* Da asubar fari 'Dayyiba ta fice daga gidanta da mummunan kudiri a zuciyarta. wani k'aramin kauye ta yiwa tsinke anan take sanya ran biyan bukatar ta, to duk da sammakon da ta buga sai da ta samu kusan mutum biyar suna zaune tsumayin fitowar wacce ta shiga zauran malamin. Dayyiba ta kama layi ta zauna a kusa da wata mata hankalinta kaf yana kan hirar da suke da abokiyar tafiyarta. Magana suke tattaunawa akan abinda ya kawosu gurinsu bokan wacce tayi kamanceceniya da wacce ta kawo ta, ta kalli matar da fadin." Nima abinda yake tafe dani kenan, ni abinda nakeso ma a rabasu gabadaya ko kuma a haukatata ta shiga duniya." Matar tace." Wannan duk mai sauki ne mutukar kin cika sharud'ai to bukatarki za ta biya." Tace." A shirye nake bani da matsala duk abinda akace zanyi mutukar bukatata za ta biya." Wannan shine 'karshen magana.......Fitowar matar dake ciki ya katse maganarsu, wacce take kan layi tayi saurin shiga ita kuma wacce ta fito daga zauran ta tsaya tana musu sallama da wani irin murmushi a fuskarta da alama akwai nasara a kan abunda tazo dashi gurin. To d'aya bayan daya suke shiga har layi yazo kan Dayyiba ta shiga ta gurfana gabansa kafin ma ta fara yi masa bayanin abinda yake tafe da ita yace." Kina tafe da aikin babban aljani wanda yake da bukatar kafa hud'u ina fatan kin fahimta." Gabanta yana faduwa tace." Malam har aikin nawa ya kai haka."? Ya buga mata tsawa da fadin." Tashi ki fita ashe da sauran imani ta tare dake tunda kike jayayya damu." Tace." Ayi hakuri ranka ya dad'e ina neman alfarma na bada kafa biyu amma samuwar kafa hud'u a gurina zai yi wuya." Ya shiru yana kallon wani jan koko mai kurji-kurji cike da jini a ciki. Ya kalleta da fadin." To dai gaki gashi nan yana kallonki sai kiyi masa bayani idan ya amince. Gabanta na bugawa tace." Ubana idan zai yuwu zan bada rago mai koshin lafiya a taimaka min." Shuru gurin yayi bayan k'are maganarta, can kuma bokan ya kama wata girgiza farar kumfa na fitowa daga bakinsa, ya kai minti goma haka kafin ya dawo hayyacinsa duk yayi wuri-wuri sai uban gumi yake. Ya kalleta da fadin.'' Kin ci sa'a yau yana cikin walwala ya kuma amince da maganarki, sauran aikin kuma ya rage naki idan kika kuskure wani to aikin zai dawo kanki. Cike da farin ciki tace." Na gode ranka ya dade zan kuma kiyaye da izinin ku." Yace." Da daddare karfe biyu ki samu bakin kwatami (kazamar kwata) ki yanka ragon da hannun hagu ki nayi kina zagin uwarki da ubanki." Tace." To an gama ranka ya dade.......Ya siffan ta mata kalar ragon da ake bukata sannan ya bata wata laya yace a gurin da ta zubda jinin zata binne. Cike da farin ta dawo gida, kuma hankalinta bai kwanta ba sai da ta tabbatar ta samu kalar ragon da aka bukata. Karfe biyu na dare ta fito babu tsoro babu imani ta fara aiwatar da mummunan kudirinta tana yanka ragon tana zagin uwarta da ubanta.........Ta gama ta haka rami da wukar hannunta ta binne layar....kamar saukar aradu taji wata tsawa! "Tashi ki gusa daga gurin."! a gigice! ta shige gida kafafunta na karkarwa. Koda ta duba gurin da safe wayam! babu alamun anyi wani abu! hankalin ya kwanta ta koma gida da tunanin abinda zai biyo baya. A daran kwanan soyayya sukayi sai dai kuma gari yana waye wa suka tashi da bala'i da masifa! kamar karnuka! ya nayi ta nayi a fusace! ta jefa masa kwalbar turare a goshinsa a take gurin ya kumbura! shima ya fusata ya zazzabga mata maruka ya kama hanya yayi ficewarsa zuciyarsa na wani tafasa! gabadaya hankalinsa yayi kan Hamra'u Koda ya isa ofis din kasa samun nutsuwa yayi ya kasa aikata komai, kawai sai ya nufi ofis din Asp yana sheda masa cewa zai tafi *'Kafur* 'Kauyensu. Asp din yace." Allah yasa dai lafiya domin naga kamar baka hayyacinka. Budar bakinsa yace." Daf yake da ya rabu da Zinatu saboda wasu dalilai. Asp ya tsirawa goshinsa ido da fadin." Kun samu matsala kenan Umaru wai me yasa kake biye mata kuna abu sai kace kananun yara." A fusace! ya daga masa hannu da fadin." Kaga saurara Asp na lura da kai dama tuntuni kai baka san laifin yarinyar nan komai tayi dai-dai ne a gurinka, okey shikkenan ni zan iya rabuwa da ita bani da damuwa kai ka aureta." Asp ya dinga jin maganar nayi masa kuwwa! a kunne hankalinsa yayi masifar tashi! kokarin magana yake amma ya rasa abinda zai ce, yana kallonsa ya fita daga ofis din ya kasa aiwatar da komai. Ya dauki wayarsa ya kira Zinatu, lokacin tana zaune bayan taci kuka ta koshi abin duniya isheta jin ta take kamar a cikin kurkuku bata so ta bude ido ta ganta a cikin gidan, domin hotonansa na da suke kafe a dakin duk tabi ta farfasasu. Fashewa tayi da kuka bayan ta daga wayar. Yace.'' Ki daina kuka Zinat na kira ki ne domin kiyi min bayanin abinda yake tsakaninku. Cikin shashshekar kuka take fadin." Na tsaneshi bana k'aunarsa bashi da adalci. Yace." Me yayi miki na rashin adalci ko dan zai kara aure ki ka tsaneshi."? Shuru tayi ta gaza furta komai in banda ciwon kai babu abunda ke damunta. Ya dinga magana tayi masa shuru, kawai sai ya kashe wayar, ya kira Madam tare da bata umarnin shiga gidan domin ta rarrasheta. 'Bangaransa kuwa hankalinsa bai kwanta ba sai da ya ganshi ya sauka a cikin garin *'Kafur!* tukkuna. Kai tsaye gidan Kawu Ado ya nufa, lokacin dawowarsa kenan daga kasuwa, ganinsa a birkice ya tayar masa da hankali, sai dai kuma da yaji abinda yake tafe dashi hankalinsa ya kwanta, da farin ciki a tare dashi yace." Ai wannan mai sauki ne Umaru, za'a daura auran a yau babu matsala yanzu zamuje tare da kai domin mu tattauna maganar da mahaifin yarinyar domin yaji abinda kake tafe dashi. Yace." Ba damuwa Kawu tashi muje domin a yau din nake san na koma gida." Kusan a tare suka tashi, kai tsaye kuma can gidansu Hamra'un suka nufa. Abu kamar al'mara gari ya dau'ka! jama'a sukayi dafifi! a kofar gidan malam Shafi'i Kawu Ado ya bada kudi aka siyo goro da alawa....Shi kuma angon ya ajiye dubu hamsin kudin sadaki....Limami ya daura aure bayan gabatar da sallar magariba. Cikin gidan kuwa Dayyiba cike da 'yan uwanta da k'awaye da makota kowa da abinda yake fad'a.....Da yawa sunfi gazgata cewa ta shiga ta fita a cikin al'amarin, domin dai kowa ya san wata shida aka sa amma ko wata daya ba a cika ba an daura aure sai kace wasan yara. Hamra'u kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki, hakika babu abunda za tace da