← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 97

Sashe 4

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bakinta, suka amsa tare da bin ta da kallo har ta karasa inda suke tsaye. fuskarta kadai zai nuna maka cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tare da ita, ba ita ta haifi Yarinyar ba amma tafi kowa shiga tashin hankali da rashinta. A raunane ta kalleshi da fadin.'' Ranka shi dade har yanzu babu wani labari ko."? Kanshi ya daga da fadin." Babu wani labari Safa watakila ma yarinyar nan bata raye domin duk iya binkice anyi amma ba'a samu wani labari mai dadi ba." Kuka ta fashe dashi, ta nemi guri ta zauna tare da rufe fuskarta da tafikan hannayenta. Ganin tana kuka yasa Aysha da sauri ta kama hanya domun fita bata so duk su lalace a gurin koke-koke domin mutukar tana kallon kukan Safa to itama zata iya taya ta. Karo sukayi da juna, Aysha kanta a kasa yake shiyasa bata ga shigowarta ba, Maijidda ce matar mijinsu, da ya aureta bayan shekara masu yawa da suka wuce. Kasancewar basa shiri da juna yasa tayi saurin kauda kanta ta wuce, ita kuma hamshakiyar ta bita da wani irin kallo kafin ta ta'be bakinta cikin wata irin tafiya ta isa da ta'kama tayi sallama a falon. Shi kad'ai ne ya amsa sallamar Safa har yanzu kuka take yana tsaye ya gaza rarrashinta shima da zai samu yayi kukan da yaji sassauci a zuciyarsa. Wawan kallo takewa Safa kafin tace."Ke a ganinki hakan kauna ce? kullum baki da aiki sai kuka uwar data haifi yarinyar ma har ta fiki dauriya Safara'u kuka bashi ne mafita ba." Safa ta dago kanta tana kallonta da mamakin furucinta, za tayi magana kenan, Yace." Abinda nake ta so su fahinta kenan yanzu ita kanta Ayshan ta gama nata ta fita, na fada masu cewa addua itace abinda ya cancanta. A tausashe tace."Hakane ranka ya dade shiyasa ko kadan ban zubar da hawaye na akan wannan al'amari ba, abinda nayi shi ya cancanta, ya kuma kamata, tun ranar da al'amarin ya far u na sanya almajiran mahaifina suyi saukar al'kur'ani na tsayin sati guda, da izinin Allah yarinyar nan tana hannu nagari za kuma ta dawo gida cikin aminci." Safa ta watsa mata wani irin kallo na zargi kafin ta tashi tare da kama hanyar fita. Sunanta ya kira ta juyo tana kallonsa babu walwala ko ta kwabo a fuskarta. Yace."Kada ki cigaba da wannan kukan bashi da fa'ida ko kadan addu'a zakiyi kinji ko." Ba tace masa komai ba ta fita ta basu guri, kai tsaye sashen Aysha ta nufa, ta sameta tare da babban yaron su wanda suke kiransa da magajin Sarki. Tana shiga ya mike tsaye yana mata barka da zuwa, ta zauna kusa da 'yar uwata kafin ta bashi umarin zama. Ya zauna kasan kafafunsu, a nutse yace." Mommah don Allah ku kwantar da hankalinku bana so naga daya daga cikinku na zubar da hawaye ni nayi imani da Allah da manzon Allah yarinyar nan tana hannu nagari da yardar Allah zata dawo gida cikin koshin lafiya. Aysha bata iya magana ba, Safa tace."Babana ina mamaki idan naji kai da mahaifinka kana maganar mu kwantar da hankalinmu, ta ina hankalinmu zai kwanta? a cikin wannan yanayin yarinyar nan sace ta akayi kuma akwai sanya hannun makusanta bana shakka a cikin maganata." Yace."Hakan tana iya kasancewa amma Mommah kada ki manta fa yarinyar *Zinatu* bata jin maganar kowa kuma a daran da al'amarin nan zai faru gabadaya sai da kuka hanata fita amma saboda rashin tarbiya ta tsallake maganarku to me zai sanya hakkinku be bibiyeta ba." Shuru sukayi domin kuwa babu mai bakin magana a cikinsu, abinda ya fada gaskiya ne, yarinyar ta fita zakkah a cikin zuriarsu, sai kuma Allah ya jarabcesu da tsananin sonta, shi kansa maimartaba wato mahaifinta baya son laifinta, ko kad'an duk da ya san abubuwan da take na rashin kyautawa a masarautar duk zafinsa baya iya tsawatar mata, sai 'yan uwanta mata dake gidajen auransu suke tsaye a kanta, wani sa'in su din ma bata saurara musu rashin kunya take musu kuma ta kwana lafiya, babu wanda take shakka sai shi Magajin sarkin, shima a bayan idonsa zaginsa take tana fadin be isa ya hana rayuwar jin dadi tun bayan dawowarta daga kasar waje bayan ta kammala karatunta ta dawo da mugayen dabi'u irin na turawa, duk wanda ya nuna mata kuskure akan abinda take cewa zai shafi masarauta da martabar mahaifinta sai ta d'aura gaba dashi, halin da ake ciki shi kansa Magajin sarkin ba tayi masa magana saboda yana tsawatar mata akan abubuwan da take na rashin tarbiya, jin kade - kade sanya matsatsun kaya bayan baiwar da Allah yayi mata na qira, yawace-yawacen pary cloub club babu inda bata shiga tayi b'arna da kudi da famkama da manya motoci ta fito babu abunda ya dameta. Da yawa mutane ba sayi mata kallon cikakkiyar mace saboda mummunan dabi'unta. Don akwai lokacin da wani babban malami ya nemi ganawa da maimartaba akanta, suka tattauna sosai maimairtaba ya fahimceshi ya san me kaunarsa shine zai zo har gabanshi ya fahimtar dashi abunda ya shige masa duhu, a lokacin ya tashi tsaye a kanta, kuma ya gargadeta kan cewa mutukar bata sanja hali ba to zaiyi mata aure duk wanda yayi ra'ayi, hakan ya tsorarta da ita, tayi sanyi na kwana biyu amma kwanaki suna turawa ta cigaba da abinda take, Gabadaya sai ya dauki al'amarin ya jinginashi a matsayin jarabta, abin na damunsa mutuka amma ya rasa me yasa baya son bacin ran yarinyar, Dan uwanshi, Abbas wanda yake Waziri a gareshi ya bashi shawara kan cewa aurene kadai abinda zai daidaita nutsuwar yarinyar saboda haka shi zai umarci babban yaron sa domin yazo su fahimci juna, maimartaba yaji dadin shawarar dan uwansa. Koda Taufiq ya sameta domin bin umarnin mahaifinsa rufe ido tayi taci masa mutunci harda zagi kamar ba jininta ba, aikuwa ya fusata! ya gaggaura mata mari hade da farfada mata mumunan magana, "Bani da ra'ayi auran mace mara tarbiya irinki umarnin mahaifina nabi har nazo neman auranki saboda haka wallahi ko ba dazi rasa mijin aure ba zan aureki ba shashaha mara hankali kawai " Bata saduda ba tana kuka tana zaginsa, Magajin sarki ya samu labarin abinda tayi wa abokinsa ya shiga har dakinta ya zaneta da belt ya fito yana huci! Gimbiya Aysha na zaune a falo yazo ya wuce ba tace masa komai ba. Washe gari ta hada kayanta kaf ta koma sashen Safa, itama anan din bude mata wuta tayi ta nuna mata kuskuranta, kafin ta bar sashen sai da tayi mata rashin kunya tasa wata baiwa ta daukar mata akwatin kayanta ta nufi sashen Maijidda, a maimakon ta nuna mata kuskuranta, sai ta hau rarrashinta ta nuna mata cewa itake da gaskiya kuma ba zata bari ayi mata auran dole ba, a takaice dai da sanya hannun Maijidda komai ya lalace! itace kuma ke daure mata gindi tana iskanci iya son ranta. To wannan dalilin yasa ita Ayshan take ganin harda sa hannunsa dana matarsa gurin lalacewar yarinyar, amma tun sanda al'amarin ya faru ya dauki laifi ya dora mata, kullum idan zai budi baki magana daya yake fada *(Tarihi ne zai maimata kansa)* tana jin bala'in haushin wannan magana, ta san a lokotan baya tayi sharafi amma abinda tayi be kai wanda ita yarinyar keyi ba, dalili iyayenta da tayi rashinsu a halin yanzu a tsaye suke a kanta, abunda tayi be kai wanda 'yar cikinta keyi a yanzu ba, ita dashi suka san hakan, amma idan ya tashi magana saboda rashin gaskiya a gaban kowa fadi yake abinda yarinyar take gado ne don haka itace sila akan faruwar al'amarin. Ta kalli Safa bayan fitar yaron nasu, tace."Duk ranar da Maijidda ta sake magana al'amarin nan sai tayi data sani domin duk irin abinda take aikatawa ina fahinta na gane itace ke zugashi yana daukar laifin yana dorawa a kaina." Safa ta girgiza kai da fadin." Eh ba zan hana ki ba ni kaina zan tayaki cin mutuncinta domin ta kai ni bango abin mamaki kuma har yanzu laifinmu yake gani, akan hakan ta shigo ta sameni cikin halin damuwa tana min maganar banza ya goya mata baya, ta kaini karshe duk sanda ta sake min katsalandan a gabanshi zan taka mata burki sai dai duk abinda zai faru ya faru." Tace."Safa ba zaki iya dasu ba, ki kyaleni ita dashi duk zanyi maganinsu, nagaji da wannan abun zanyi magani." Zuciyarta tayi sanyi da jin furucinta, ba tun yau ba, ta san halin Aysha ba kanwar lasa bace da sannu za tayi maganinsu gabad'aya. ********* Lokacin data farka garin yayi duhu, kuma bai kunna fitila ba tun bayan daya gabatar da sallahr isha'i sai ya kishingida a gefenta, saboda ita ya sanya bai jagoranci yaran sa farauta ba, sai kawai ya turasu daga shi sai ita ya rage a gurin, sai kuma kukan 'kananun dabbobin dake tashi. Cike da tsananin tsoro! da firgici! ta mike zaune tana lalube a gurun, masifaffan tsoro ne da ita, rarrafe ta fara ko'ina zata oho! yana kokarin tashi zaune ta afko kansa, fuskokinsu suka hadu, bakinta ya hadu da nasa, lokaci guda numfashinsu ya had'u! da sauri ta kautar da fuskarta, ta danne kirjinsa da hannu tana kokarin barin jikinsa, ba tare da wata manufa ba ya zuba dukka hannuwansa kan kwankwansonta, gefe guda ya ajiyeta, ta sake yunk'urin barin gurin domin kan ciyayi a ajiyeta tana kuma jin tsoron wani mugun k'waron ya cijeta, kafarta daya ya rike, can kasan makoshi yace." Ki samu nutsuwa."! kafarta ta fizge, da rarrafen ta lalubi daddumar ta zauna tana ya mutse fuskarta, gabadaya cinyoyinta sun dauki kaikaiyi da azabar zafi. Fitila ya kunna yana kallonta, sai yamutse ya mutse take, mikewa yayi ta kalleshi, yana kokarin barin gurin, da sauri tace." Ina zakaje."? Bai juyo ba domun ji yayi tambayar tayi kama data rainin hankali sai kace uwarsa tana masa magana gatse-gatse! Ya cigaba da tafiyarsa ba tare da ya amsa maganarta ba, kallonsa ta dinga yi tana mamakin girman jikinsa dogo mai garin jiki yana yanayi da jarumin kasar hindu *( Parbahs bahubali)* idonta a hanyar da yabi gabanta sai faduwa yake, can taji wani irin kukan dabbah! a bayanta, a zabure! ta juya tana zare ido! jin
Chapter 4 · 0% Book details