Sashe 25
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
nuna tamkar ba jininta koda yake inda sabo sun saba da halinta amma dai abunda tayi musu a yanzu ya 'bata musu rai mutu'ka! Sosai suka samu kulawa mai kyau kafin maimartaba ya bukaci zama dasu sai da sukaci abinci suka gabatar da sallar la'asar tukkuna sannan suka sameshi a fada shi kad'ai domin akwai maganar da yake so suyi a tsakaninsu. Gaisuwa suka sake mikawa a gareshi kafin shi da kansa ya mika godiya a garesu akan alkairin da sukayi masa. Asp yace."Ranka ya dade ai babu godiya a tsakaninmu da kai, domin kai uba ne a gurin mu, ka cancanta da abunda yafi haka, bayan hakan kuma kulawar da mukayi akan yarinyar nan hakkinmu ne tunda aikin mu ne kare rayukan al'umma." Ya girgiza kanshi da fadin." Tabbas maganarka haka take Asp amma dole nayi godiya domin samun irinku masu tsoron Allah da kishin 'kasa zaiyi mutukar wahala wannan dalilin yasa na jima ina nazari da tunanin irin alkairin da zanyi muku." Kafin Asp din yayi magana ya riga shi da fadin." Ranka ya dade kada ka damu kanka akan wannan al'amari wallahi ni abunda nayi akan yarinyar nan don Allah nayi bana bukatar komai a gurinka face addua." Murmushi yayi yana sake jin kaunar yaron a cikin zuciyarsa, yace." UMARU kenan addua kam zan cigaba dayi muku har karshen numfashina amma ba kaji bahaushe yana cewa (yaba kyauta tukwici ba) ba don kada nace na baka auran yarinyar nan ka dawo min da kyautata ba to dana baka ita sakamakon alkairin da kayi min." Fadar tayi shuru sakamakon maganar. Kasa d'ago kansa yayi ballanatana ya nuna rashin amincewarsa da kyautar da akayi masa..............Jin beyi magana ba yasa yace." UMARU kodai baka kar'bi wannan kyautar tawa bane."? Asp da sauri yace." Aa haba dai! ranka ya dad'e wane mutum! kyautar mutum ba karamin al'amari bane sosai ni naji dadin wannan al'amari kuma kayi kyautar akan ga'ba domin dama bashi da aure a halin yanzu mungode sosai da wannan karamcin." Fuskarsa cike da annuri yace." Asp ka ari bakinsa kaci masa albasa amma yanayinsa ya nuna kamar beyi na'am da wannan kyautatar tawa ba." Yayi namijin 'ko'karin kawar da damuwarsa kansa ya dago tare da kokarin aro walwala da farin ciki yace." Ranka ya dade farin ciki ne ya hana ni iya magana, tabbas abunda abokina ya fada hakane kayi min kyauta akan ga'ba kuma na kar'ba hannu biyu nagode kwarai da wannan karamcin." Ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Alhamdullihi Allah abin godiya, lallai babu shakka ZINATU tayi dace da miji irin wanda yake da wahalar samu ina rokon Allah ya tabbatar da alkairin dake cikin wannan al'amarin." Gabad'aya suka amsa da "ameen ya Allah." *Free pege zai 'kare a pege 40 masu payment kawai nake da bukata idan kin san na siyan littafin nan za kiyi ba kada kiyi min magana *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* 1/26/22, 18:14 - Buhainat: *GOJE!! _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION ____________________ *1-NANA KHADIJA* *2-YARO DA KUDI* *3-GIMBIYA BALARABA* *4-BABBAN YARO* *5- MASHAHURI* *6- LADIDI KWADAGA* *7-TSANTSAR BUTULCI* *8-SADAUKI OMAR* *9-NIDA YAYA SADAM* *10- 'YAR BANGAR SIYASA* *11-DA WATA A KASA* *12- MADADI* *13-KWARA TABI KWARYA* *14-GA RINTA NAN* *15- MATSALARMU A YAU!* *16-RUWAN DARE* *17-GOJE!!* _Littatafai na kenan ga duk mai bukatar karanta daya daga ciki zai samu damar karantawa cikin saukin farashi, wanda zai iya siya nake da bukata, don Allah idan ba siya za kiyi ba kada ki dauki number ta kiyi min magana NAGODE sosai masoya *SHAFIN NA YAU NAKU NE 'YA'YAN ALBARKA.* _DAUGHTER *ZEEY KUMURYA* _MARUBUCIYAR_ *(NEHAL)* *DA* _MAMAN TEDDY *MARUBUCITAR* _LITTAFIN_ *WALI-JAM * *BAFULATAN RUGA* _DA SAURANSU_ Allah ya kara muku basira da haza'ka, NAGODE 'kwarai! Allah yayi muku albarka. ________ LAST FREE PEGE *39&40* A takaice dai basu bar masarautar ba sai da duk suka gaisa da duk wanda ya kamata, sun tafi da mamakin mutumci da dattakon mutanan, hakika kaf famliy din yarinyar nagartattun mutane ne masu hankali da sanin ya kamata, ita kadai ce ta fita zakka a cikinsu, koda yake dama haka Allah yake ikonsa, amma duk da hakan itama ba za'a rasa wani abu mai kyau daga cikin dabi'unta ba. Maimartaba ya basu kyautar dawakai lafiyyayu gami da kayan sarauta kwatankwacin irin wanda yake amfani dasu, mussaman yasa aka kawo masa kayan farauta daban-daban domin ya gwangwajeshi, aikuwa duk cikin kyautukan da yayi musu yafi farin ciki da kayan farautar domin dama yana da bukatarsu, a ganinsa koda zai cika d'aki guda da irinsu ba matsala bace a gurinsa. Wannan karon gabad'aya a kujerar baya suka zauna, sai da sukayi nisa da tafiya sannan Asp ya fara maganar da tuntuni take cin zuciyarsa. Ajiyar zuciya ya sauke ya kalleshi da fadin." Asp kwata-kwata fa ni wannan al'amari be kwanta min a rai ba, kawai dai na amsa masa ne amma bana jin zan kar'bi auran yarinyar nan." Asp ya 'bata fuska da fadin." Kada ka zama k'aramin mutum mana, ko dai har ka manta da wanda kayi magana, ba fa gurin wasan yara mukeje ba, ya za'ayi ka amsa masa cewa ka kar'bi kyautarsa daga baya kuma ka shigo da wata magana'' Kallonsa yayi babu farin ciki a fuskarsa yace." Kunyarsa ce ta sanya na amince na kar'bi kyautarsa amma kai kanka kasan tafiyarmu ba zata zo d'aya da yarinyar nan ba, naji takaici a lokaci da yayi maganar har kake cewa dashi bani da aure alhalin jiyan nan, na nuna maka yarinyar da zan aura a lokacin daka shigo gidana, tabbas ka shigo masa da maganarta ina ganin ba zai k'arfafa maganarsa ba." Yace."UMARU mace hudu Allah ya halasta maka mutu'kar za kayi adalci a tsakaninsu, wannan dalilin yasa lokacin daya fadi maganar na k'arfafa masa gwiwa, haba mutumina ai da kunya a gabansa ka nuna k'yamarka akan jininsa, kayi hakuri da katsalandan din da nayi maka domin ni kaina nasan da cewa yarinyar akwai matsala a tattare da ita, bata da tarbiya ko kadan, to amma hakan ba zai hana a aureta ba tunda wannan matsalar kawai gareta ina ganin idan ta hadu da jajurtacce namiji kamarka to cikin sauki rayuwarta zata sauya. Ya jima yana nazarin maganganun Asp din kafin yace." Kasan Allah a tsarina bani da ra'ayi tara mata amma ina ganin hakan ba zai samu ba, Asp ina jin tsoron auran yarinyar nan ta hana ni kwanciyar hankali, wannan dalilin yasa gabadaya al'amarin be kwanta min a raina ba. Ya dan doki kafadarsa da fadin." Haba mutumina kai da saba gwagwarmaya da maza mai zai sanya lamarin mata ya dinga baka tsoro! wallahi babu wani abun fargaba da tsoro a cikin al'amarinsu daga zarar ka gane hallayarsu shikkenan zaka zauna dasu lafiya saboda ka cire shakku akan hakan mutumina ba tun yau ba nasha fada maka cewa mace hud'u ce ta dace da kai haba *jan wuya* kada ka bani kunya mana." Dariya ya d'anyi ya bashi hannu suka tafa kafin ya girgiza kanshi da fadin." Asp ba zaka gane ba ne amma shikkenan kawai mu bar maganar Allah ya tabbatar da alkairi." Yace." Yauwa abunda nakeso naji kace kenan abokina insha Allahu za kayi fari ciki da wannan al'amari. To har bayan magariba ZINATU na tare da aunty Maijidda komai anan ta gabatar wanka cin abinci da sauransu, hankalinta da tunaninta gabadaya baya kan uwar da ta haifeta ba ballantana kuma wani, hakan yayiwa ita Maijiddan dadi dama babban burinta ta cusa bakin ciki a zuciyar Safah domin itace abokiyar gabarta tun sanda ta fahimci cewa gimbiya Ayshan tayi mata nisa, sai ta mayar bakin kishinta kan Safara'u wacce ita kuma ta mayar da ita shashasha domin duk abunda take na rashin hankali bata biye mata su taru su lalace gabadaya. Ta dinga bugar cikinta tana bata labarin abubuwan da suka faru, da rayuwar ta a dajin gami da irin wahalhalun da tasha, da labarin zamanta a gidan Asp babu abunda ta rage, sai dai koda wasa bata fada mata irin namijin kokari da kulawar da yayi akanta ba, duk abinda zata a fad'a a kansa sharri ne, har da k'azafin fyad'e kamar yanda tayi masa a gurin Asp, gabad'aya suka had'u suna zaginsa, Aunty Maijiddan ita ke fadin." Zata shedawa maimartaba komai domin abi mata hakkinta, hakan yayi mata dadi a ranta domin ta san mahaifin nata yana saurarar maganar auntyn nata. B'angaran Gimbiya Aysha kuwa ganin har bayan isha'i yarinyar bata shigo ba, sai ta kalli sauran yaran nata dake zaune a gabanta tace." Wannan zaman da kuke bashi da amfani domin dai kune kuka damu da yarinyar nan amma ita bata damu daku ba, da ta damu daku to da yanzu ta nemi inda kuke saboda haka ku tashi ku tafi gidajenku hakan shi yafi ku rabu da ita da mugun halinta, sannan kada wacce tayi yunkurin kiran wayarta ku 'kyaleta taje tayi rayuwa da wacce ta za'ba a madadi na da kuma ku." Cikin rashin jin dadin abinda 'yar uwar tasu tayi kowacce ta tafi gidanta da bacin ran abun a cikin ranta. Da yake aunty Maijiddan ce da girki a daran ta zauna tana shirya masa k'arya da gaskiya har da cewa ya dauki mataki mai tsauri a kan yaron domin yarinyar ta sheda mata cewa a yayin zamansu a dajin ya keta mata haddi." Duk cikin maganganunta wannan ce kadai ta dauki hankalinsa, hankalinsa ya tashi da jin maganar saboda ya san hakan na iya faruwa idan shad'en ya ratsa, to amma wannan maganar ba zata sanya ya janye manufarsa ta alkairi ba, kamar hakan ma shine rufin asirinsu, duk da hakan zai tuntubi yaran domin tabbatar da gaskiyar magana. Washe gari da safe kafin ya zauna a fada ya nufi b'angaran matayen nasa domin dubasu, gabadaya ya samesu ba yanda ya saba ganinsu ba, Safah dai tayi kokarin kawar da damuwarta har ya dan zauna sukayi hira, bangaran Gimbiya Aysha kam rigima suka tafka irin wacce sukayi shekara da shekaru ba suyi irinta ba. Cikin tsananin 'bacin rai yace."Aysha yau ni kike nunawa da yatsa akan wani dalili naki na banza da wofi shin wai me Maijidda tayi miki kika dauki