Sashe 32
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya samu damar kira na da *Matar ladan noma* to ka fada masa cewa koda na shigo gidansa yayi kokarin samun zaman lafiya dani, idan ba haka ba wallahi sai na hana shi kwanciyar hankali domin auranshi kaddara ne a tare dani, domin ni nafi karfinsa ni ba matar k'ananun yara bace." Maganganunta sun bashi haushi da dariya amma bai yarda yayi dariyar ba ya danne cikin taushin murya yace." ZINATU wai me yasa ki ke haka ne? me kika dauki duniya? ita fa mace duk isa da kasaitarta gidan mijinta shine mutuncinta, duk da bakya san abokina amma bai cancanci haka daga gurinki ba, na tabbata cewa kece kika tunzurashi har ya kira ki da wannan kalmar *Matar ladan noma* wanda ni kaina nasan ya fad'a ne domin ya 'bata miki rai amma matan da za'a kira da irin wannan sunan kwata-kwata bakya cikinsu, ina mai tabbatar miki da cewa abokina yana sonki, abunda yasa ki ka kasa gane kansa wannan dabi'un naki marasa kyau! shi mutum ne wanda baya son raini ko kadan, yana da zafi! shiyasa bana so kije gidansa da wannan dabi'un naki, don Allah kiyi hakuri ki dauka cewa auransa alkairi ne ki zauna lafiya dashi da 'yan uwansa." Baki ta ta'be da fadin.'' Asp ni ba zan yarda da wannan maganganun naka ba, kawai kana so ka tsara ni ne idan ba haka ba yaushe zaka zo kana fada min cewa yana sona ai da yana sona ba zai so bacin rai na ba, sannan duk abunda nace ina so sai yayi min amma tsakanina dashi kullum ba'kar magana kafada masa cewa a shirye nake idan ya bukaci ya zauna lafiya dani kansa, idan kuma tashin hankali yake bukata ashirye nake." Da sauri ya tare ta da fadin." Mugun ji da mugun gani Allah ya tsare mu, bama neman tashin hankali kullum alkairi muke nema ZINAT Abokina zuma ne (ga zaki ga harbi) duk da ban dade tare dashi ba amma na karanci halayyansa tsaf, yana da saukin kai ga wanda ya fahimceshi baya san tashin hankali zaku jima wani sa'bani bai shiga tsakaninku ba, mutukar ka kiyaye abunda zai kawo muku samun sab'anin, ina so ki rike wannan don Allah na ro'ke ki, ki zauna lafiya dashi kada ki bari shaid'an ya samu nasara a kanki. Murmushin takaici tayi kafin tace." Ranka ya dad'e na rasa me yasa kake tsoron wannan abokin naka kullum kai kenan gurin yi masa campaign kana kare shi to ni duk abunda zaka fada a kansa ba zai sanya naji tsoronsa ba, ka fada masa cewa nafi karfin wannan b'akin kwallin da yake rambad'awa a idanuwansa, kuma be isa ya firgitani ba." Dariya yayi kafin ya girgiza kai da fadin." Kinga mu bar wannan maganar tunda kin kasa fahintata, yanzu wane shirye-shirye kike yi game da hidimar biki."? Baki ta ta'be ta yatsine fuska da fadin." Wane irin shirye-shirye sai kace wacce za tayi auran so, ni babu wani shiri da nake kuma bana bukatar komai daga gurinku. Yace." A haba dai gimbiya koda ba auran so bane yana da kyau ki d'an yi gyare-gyare domin ki fita daban a cikin mutane kasancewarki amarya, wannan hakkinki ne, ki fadi ko nawa kike bukata sai na tura miki yanzu." Dariyar takaici tayi kafin tace." Ranka ya dade na fada maka fa duk campaign din da za kayi masa wallahi baku isa ku sayi soyyayata ba, ka fada masa cewa har yanzu bai kai wannan matsayin ba,har yaushe yayi arzikin da zai zo yayi wa mutane tutiya dashi." Asp ransa ya b'aci da jin maganarta, Yace." Wai ke mai yasa kike hakane? ina yi miki kallon mai ilimi amma kina aikata aiki irin na jahilai, Zinatu girman kai da izzah duk ba dabi'u ne marasa kyau! don Allah ki daina sannan ki daina daukar kanki daban da mutane dukkaninmu Allah ne ya hallice mu, shine kuma yayi mai kudi da talaka kuma shi yake bada mulki ga wanda yaso ya kuma hana wanda yaso, kada kiyi mamaki Allah zai iya musayan miki rayuwa, ki zama mak'askanciya wannan kadan kenan daga irin hukuncinsa, ki gane duniya dan Allah." Shuru tayi da alama nasiharsa ta shige ta. Ya sauke numfashi da fadin ." Kin san Allah duk wannan kai da kawon da na keyi akan wannan al'amari UMARU be sani ba, amma magana kadan sai kice ina masa campaign ai ba sai munyi campaign ba tunda an riga an bamu kyauta wane campaign za muyi." Cikin zolaya ya 'karashe maganar. Ta kuwa fusata! da fadin." Ina ganin mutuncinka fa kada ka 'kara yi min irin wannan wasan." Ya tsagaita dariyar da yake da fadin." Na daina ranki ya dade yanzu ake hukuma ce sai da rarrashi duk da an bamu kyauta muna godiya domin mun san ba karan mu ne ya kai tsaiko ba, dami a kala muka tsinta." Ya mutse fuska tayi da fadin." Shikkenan ni zan kashe wayar sai an jima." Yace." Ai bamu gama ba. A k'agauce tace." Saura me kuma Asp idan kun kwantar da hankalinku saura 'yan kwana ki aka kawo muku ni." Yace." Ni da kaina ma zanzo na dauke ki tunda kin san mutumin naki baya gari yana gurin training ni ya bar wa wuka da nama." Shuru tayi ba tace uffan ba. Yace."Yanzu nawa kike bukata."? babu wasa yayi maganar. Itama cikin rashin wasa tace." Bana bukatar ko kwabon ku." Murmushi yay da fadin."Shikkenan tunda kin ce haka mu dai mun fita hakki dan kada watarana ayi mana gori." Cikin takaicinsa tace." Sai an jima kace ina gaishe da da k'awata." Ba ta jira jin abinda zai ce ba ta kashe wayarta tana jan tsaki, gabadayansu haushinsu takeji, magana d'aya da yayi itace ta tsaya mata a rai..........Inda yake cewa duk wannan abubuwan da yake abokin nasa bai sani ba, ita ai ta dauka shine ya wakiltashi kafin yayi tafiyar yazo ya kafa masa gwamnati a gurinta, tsaki mai tsayi taja kafin ta nufi toilet da bacin ran hakan a cikin ranta. Cikin baccin da ya fara daukarsa yaji alamun kira ya shigo wayarsa. Hannu yasa yana laluban drowar da wayar ke kai. Murmushi yay ganin mutumin shi ke kira. Yasa wayar a kunnashi tare da sallama a bakinshi. Daga daya bangaran Asp din ya amsa da fadin." Jarumi ya na jika wani iri ne ina fata dai lafiya."? Ya bude murya sosai da fadin." Lafiya lou wallahi bacci ne ya fara daukana kiran wayarka ya tashe ni." Yace."Okey yau kun dan samu hutu kenan." Hamma! yayi kafin yace." Eh amma hutun duka na two hours shine dalilin da yasa na kwanta domin na rage baccin dake idona. Yace."Hakan yana da kyau mutumina, shin kana waya mutuniyar kuwa."? Murmushi yay wanda ya tsaya iyakar fatar bakinsa ya fahimci wacce yake nufi shiyasa yayi murmushin takaici. Asp yace." Tunda naji wannan murmshin naka na san baka d'auki shawarata ba, UMARU na fada maka fa dole a wannan ga'bar kai ka sauka kabi yarinyar a sannu a hankali kafin ta shigo gidanka, idan ta shigo shine zaka nuna mata kai ne a sama da ita, har yanzu ka kasa gane hallayar 'ya'ya mata, wallahi da ka dauki shawarata da tuntuni yarinyar nan ta bada kai bori ya hau, na fada maka tana bukatar rarrashi da nuna kulawa mybe *Ilove you* wannan ka kasa fad'a mata wanda ni nayi imanin da cewa abinda take bukata kenan." Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Asp wannan yarinyar fa bahaguwace! kai ne har yanzu baka fahimta ba kake ganin nuna kulawa ko kuma *I love you* zasu sanya ta daina rashin mutunc! a haka take, haka Allah ya halliceta zan iya karyar mata da kaina domin samun soyayyarta ta dizgani girmana ya zube a banza a wofi, ni bana wahalar da kaina a in da na san ba zan samu biyan bukata ba. Yace." Kai ne dai kake ganin haka, amma ni nayi imanin cewa kabi wannan matakin wallahi sai ka sameta a hannu kuma ka gwada ka gani." 'Yar dariya yay da fadin." To shikkenan zanyi kokarin ganin nayi abinda kace duk yanda mukayi da ita za kaji." Yace."Yawwa haka nake so na ji yanzu nima muka gama waya da ita na kira ta domin jin abunda take bukata na hidimar biki, tace bata bukatar komai daga gurinku kuma tace lallai na sheda maka cewa duk irin campaign din daka turo ni gurinta to ba zaka samu abunda kake so ba. Dariya ya fashe da ita, ya dinga yi yana girgiza kai ya ma kasa magana saboda yanda dariyar taci karfinsa. Asp shima yana dariyar yace." Ai ban ta'ba ganin rigimmiyar yarinya irin wannan ba, amma na fahimci nasiha tana ratsa ta wannan ma makami ne wanda ya cancanta ka rike hannu bibbiyu. Dakatar da dariyar yayi da fadin." Asp maganar nan ta bani dariya da haushi wallahi amma dai dariyar tafi yawa, lokacin da tace maka kana yi min campaign sai kace mata kai din ubangidana ne kafi karfin kayi min fadanci ko wani aiki, amma na san da wuya ka iya mayar mata da martani. Yace."Ni da nake kokarin ganin an raya sunnah ma'aiki SAW yaushe zan dagula al'amarin ai duk abunda tace dai-dai ne, amma ina kokarin ganin na nusar da ita idan tayi wani shirman." Yace." Nagode sosai abokina, yanzu a wace matsaya kuka tsaya."? Yace." Tunda tace bata bukatar komai namu shikkenan, amma na fada mata cewa kada daga baya tazo da wata magana. Yace." Kwarai kuwa tunda an fita hakkinta wannan shine sharadi." Yace." To kaji yanda mu kayi da ita insha Allahu kuma za'a gabatar da komai cikin tsari amma ya kake gani? shin a ranar da aka daura auran za'a daukota ko kuma sai washe garin ranar."? 'Dan 'bata fuska yayi da fadin.'' Aa ana d'aurawa ka d'auko ta, bana tsammanin ma mahaifinta zai bari ta sake kwana a gidan mutukar an d'aura auran." Yace." Okey to shikkenan hakan dama shine tsari mai kyau, insha Allah zanyi kokarin hakan ya tabbata." Yace." Godiya nake abokina Allah ya kara zumunci ya kuma bar abotar mu." Ya amsa da "Amen ya rabb mutumina ka wuce aboki a gurina a matsayin dan uwa kake a gurina." Cikin wani irin farin ciki yace." Haka kake