← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 97

Sashe 69

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kamshin jikinta. Kusa da ita ya zauna ya jifanta da wani irin kallo, ta marairace fuska tana kallonsa kafin tayi masa barka da zuwa. Ya dubi hannun da ya kone! tsigar jikinsa ta tashi, a hankali ya rike hannun ya fara tofa mata addua ya gama ya kalleta cike da kulawa yace." Ke zanyi wa sannu duba da irin tsautsayin da kika samu ta dalili na, tunda kika sheda min hankalina ya tashi ina Allah-Allah na iso gida naga halin da kike ciki, amma abun mamaki sai na sameki cikin koshin lafiya kinyi ado da kwalliya irin wanda nakeso ina mai tabbatar miki da cewar ina alfaharin kasancerki a matsayin matata." Murmushi tayi tare da jin dadin kalamansa, dama kuma babban burinta bai wuce ace ta siye zuciyarsa kaf ya daina ganin ko wace mace a gabansa ba sai ita, ta lura yana da sau'kin kai! kuma ta fahimci ya kamu da tsananin sonta wannan abin alfahari ne a gurinta. ***** Da safe kafin ya fita gurin aiki yake sheda mata tafiyar da za suyi, sam ba tayi tunanin cewa har da ita za'ayi tafiyar ba, sai da taji yana fadin." Za ku kwana biyu a k'auyen domin kisan 'yan uwana suma su sheda ki sosa.'' Sai ta kasa 'boye bacin ranta! ta dan 'bata fuska tana kallonsa. Ya fuskanci ba tayi na'am da tafiyar ba, ransa bai masa dadi ba. Ganin taki yin magana ya sanya ya tashi da niyyar fita. Ta kalleshi a lokacin da yake gyara f-cap din kansa. da kyar tace." Sai ka dawo." A dakile ya amsa ya kama hanyar fita zuciyarsa duk babu dadi, sam bai ji dadin abinda tai masa ba, ya lura har yanzu ba ta k'aunar a halinsa, a ganinsa duk soyayyar da take nuna masa a banza take, mutukar ba zata kaunaci yan uwansa ba. Ya saba kiran wayarta idan ya samu saukin aiki amma a ranar sai ya share ta yana so ya nuna mata kuskuranta B'angaranta kuwa ba wai zuwa 'kauyen ne ba taso ba,cewar da yayi zata zauna tare dasu har na tsayin wasu kwanaki shine abinda ya 'bata mata rai! gaskiya bata tunanin kwana a kauyen 'kafarta-'kafarsa. Da taji shuru bai kira ta ba, sai ta kira shi, ya daga yana shan k'amshi. Murmushi tayi kafin tace." Fushi kake ko darling." Gyaran murya kafin yace." Fushi akan me? a halinki ai ba sabo bane a gurina." A shagwabe tace." Au! mugun hali ne dani."? Yayi shuru bai ce mata komai ba. Ajiyar zuciya ta sauke a sanyaye tace." Kayi hakuri ba wai bana so naje bane naji kayi maganar kwanaki shine bana so." Ya fusata! yace." Kin ga idan ma ba zakije ba kiyi zamanki okey." Kawai ya kashe wayarsa. Ta dinga bin wayar da kallon mamaki! ita fa yanzu kwata-kwata bata bukatar abunda zai shiga tsakaninsu, amma ta fahimci akan 'yan uwansa zai iya cin mutuncin kowa. A'a! abu kamar wasa 'karamar magana na nema ta zama babba! fushi yake da ita sosai! dan koda ya dawo daga gurin aikin bai shiga gurinta ba, ya gama duk abunda yake ya nufi sashensu Uwale, zuciyarsa duk babu dadi. Koda taji shuru bai shigo ba, sai ta yanke shawarar zuwa gurinsa, tunda zuwa yanzu ta san ya dawo, ita sam ba taga abun fushi da 'bacin rai ba, bata gudin 'yan uwansa. halinsu ne kawai abun gudu. Koda ta shiga gurin nasa, Babu shi babu dalilinsa. amma akwai alamun ya dawo yayi wanka sannan ga 'karamar wayarsa nan a saman drowar. Kai tsaye gurinsu Uwale ta nufa domin tana da tabbacin yana can. Abunda taci karo dashi ya kusa tarwatsa mata zuciya, amma sai ta jajurce! tayi kokarin danne mugun kishin da yake taso mata.. tayi musu sallama. Su biyu ne a falon, Uwale na daki domin gabatar da sallar magariba, shima dawowarsa kenan daga massalancin, ya samu Hamra'un ta shirya masa lafiyayyan towon farar shinkafa da miyar kubewa d'anya wacce taji bushashshen kifi da man shanu! Ya dinga shi mata albarka domin yini cur bai ci abinci ba, tun breakfast din safe, b'acin ran da ya fita dashi ya ha nashi cin wani abu. Tana zaune durshan a gabansa bayan ta zuba masa abincin yana ci tana bashi labarai sai dariya yake sai kace mata da miji. A zabure! ta kalli bakin kofar! suka had'a ido, bahaushe yace (Mara gaskiya ko a ruwa gumi yake) duk sai ta daburce! tayi gaggawar matsawa daga kusa dashi, shi kam ko gezau! abincinsa kawai yake ci amma ya amsa sallamar bai dai kalleta ba. Ta zauna kujarar dake kallonsa da fadin.'' Ranka ya dade ashe ka dawo."? Ya dago kansa yana kallonta da mamakin sunansa da ta kira shi, sam bai mayi tunanin za tayi masa magana ba, saboda ya san azabar kishinta. Da yake Namijin duniya ne babu kunya yace." Eh na dawo kina raina yanzu nake maganarki a zuciyata." Taji kamar ta fada masa bakar magana! amma sai tayi shuru kawai tana masa wani irin kallo na tuhuma! Saurin sunkuyar da kansa yayi! duk dadin towon a bakinsa yaji ya fice masa daga rai! Hamra'u kam! simi-simi ta kama hanyar d'akinta! tana ta wani kumbura fuska shigowar Gimbiyar ya 'bata mata rai mutu'ka! domin ta katse mata jin dad'inta. Ya kalleta da fadin." Ya zaki tafi baku gaisa ba. Ya'ke tayi ta juya da fadin." Aunty Gimbiya ina wuni."? Tace." Lafiya lou ina Uwale."? Kafin ma ta bata amsa Uwalen ta fito da carbi a hannunta, ganin Gimbiyar yasa ta washe bakinta, sosai tayi farin cikin ganinta a zaune babban burin ta ace Gimbiyar ta saki jikinta dasu. Hamra'u kasa tsayuwa tayi a gurin da sauri ta shige dakinta, ranta idan yayi dubu ya ba'ci, ita dai tana kishin yanda Uwale ke nuna kauna da kulawa akan Gimbiyar. Cikin mutuncin da girmamawa suka gaisa da juna. Ta kalleta da fadin." Ya jikin naki jiya Ai yake fada min kin 'kone a hannu har nake cewa zan shiga na dubaki Allah bai bani iko ba." Tace." Ai ba sosai na k'one ba, kuma tunda yayi min addua gurin ya bushe ya daina ma zafi." Tace." Duk da haka dai ai kin tsallake tsautsayi! kin ma yi kokari abunda ba ka saba a kansa ba, ai dole ka sha wahala." Murmushi tayi amma ba tace komai ba. Da farin ciki a maganarta tace." Mijinki ya sheda miki gobe za muje 'kauye ko "? Fuska a sake ta amsa " Eh ya fad'a min Allah ya nuna mana goben lafiya." Tace." Ameen ai yana da kyau kema ki saba da dangi shiyasa da yace shi ba zai kwana ba, nace to ya zama dole ke ya barki tare damu domin 'yan uwa su sheda fuskarki ai riga an zama d'aya." Tace." Hakan yayi insha babu matsala ta b'angare na, ina tare daku." Kallonta yayi yana mamakin furuncinta. D'auke kanta tayi dan tunda suke maganarsu bata kalleshi ba saboda masifar haushinsa da take ji. Uwale sarkin hira da labarai na ban dariya ta dinga bata labarai irin na da! ta dinga dariya tana mamakin kokari irin na mutan da! ace Mace ta haihu amma unguwar zoma ta fita yawan nama! ita abun ma dariya ya dinga bata. Ganin kamar sun manta dashi a gurin yasa ya tashi domin zuwa ya kwanta a gajiya yake tilis! Ta kalleshi da fadin." Ya zaka tashi kuma."? Yace." Eh mana to zaman me zanyi kun manta dani kuna hira bakwa sani a ciki zanje na kwanta ne." Dariya tayi irin ta tsaffi! kafin tace." To ai gwara ka kwanta ko ka tashi da wuri nima nafiso muyi sammako." Yana kokarin fita yace." Uwale ai ke yau bana tsammanin zaki iya bacci ." Ta fashe da dariya da fadin." Me zai hana zanyi wanda ya sawwa'ka dai ai dole nayi zumudi UMARU wata da watanni ba tare da 'yan uwa ba." Da al'ajabi ta k'arasa maganar. Girgiza kansa kawai yayi kafin yace.'' Sai da safe kenan ya kalleta bata da niyyar tashi su tafi......."A nan zaki kwana ne."? Ya jefa mata tambayar hannunsa na rike da handle domin bude kofar. A nutse ta mik'e ta kalli Uwalen da fadin." Sai Allah ya kaimu." Ta amsa da "To Allah ya tashe mu lafiya Alla ya bamu alkairi." Kusan a tare suka amsa kafin ya bude kofar ya fita ta bi bayansa. Kowa sashensa ya nufa, bata tsammanin bin sa domin yanda zuciyarta take a tunzure! bata tsammanin zasu wanye lafiya. munufiki ne har yanzu akwai abunda yake 'boye mata. Wanka tayi ta sanya kayan bacci tayi kwanciyarta tana tunanin irin hukuncin da za tayi masa cikin ruwan sanyi, abu d'aya za tai masa ya shiga damuwa! shine ta hana shi kanta wannan shine babban tashin hankalinsa, tabbas zai kawo kansa anan za ta fanshe in yaso yaje gurin yarinyar ta bashi kanta, tunda yana zuwa yaci abincinta a boye. Washe gari da wuri ta gama shirinta sosai ta had'a musu tsaraba cikin baggo, sai da ta shirya tsaf sannan ta zauna domin karyawa. Lokacin ya shigao cikin farar shadda kar! wando da riga iya gwiwa da wani irin tsadaddan aiki a wuyan rigar da hannu. yayi kyau sosai rashin sanya hula shine yai masa cikas, da alama bashi da ra'ayi ta sosai. Ta kalleshi ta 'kara kallo, yana da kyau sosai sai yanzu take tantancewa dole mata su rikice a kansa, itama tana masifar sonsa saboda yana da baiwar da ba kowane namiji ne ke dashi ba. Abinda take rayawa a kansa shima irinsa ne a zuciyarsa, duk kwanan duniya 'kara sonta da kaunarta yake a zuciyarsa. Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta gaishe shi a sanyaye. Babu y abo babu fallasa ya amsa yana gyara agogon sarkar dake hannunsa, yace." Har kin shirya kenan."? Shuru tai masa bata ce komai ba. ta cigaba da kurbar tea din dake gabanta. Saboda neman magana sai ya kai hannu yana so ya dauke cup din. Ta kalleshi da fadin." Ya haka kuma."? Yace." So nake na sha." Murmushi kawai tayi ta sakar masa cup din.....ya dauka ya kai bakinsa dai-dai bakinta ya shanye tas! Ta yunk'ura ta tashi daga gurin. Ya bi bayanta da kallo a lokacin da take kokarin shiga dakin, yawu ya had'iye ya lumshe idonsa!
Chapter 69 · 0% Book details