← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 97

Sashe 50

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yace." Ba zan baki hanya ba sai kin bani amsar tambayata." Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Babu ruwanka da rashin ibada ta ko kuma kai ne kake bada aljanna." Ya girgiza kai da fadin.'' Ba ni bane amma hakkin kulawa dake yana hannuna mutukar kinyi wasarere da addini da ibadarki to babu shakka nima ina da kamasho "(zunubi) Da gefan ido ta kalleshi har yanzu da sauran jin haushinsa a zuciyarta............Kawai saboda tana so ya kyaleta yasa ta bashi amsa da fadin." Tun asubah nai sallah sai na kwanta okey abinda kake so kaji kenan." Yace." Eh abinda nake so na tabbatar kenan saboda haka kiyi duk wani uzurinki ina jiranki za muyi magana." Hanya ya nuna mata da hannu alamun ta wuce. Ba tace komai ba ta ratse shi ta wuce tana tunanin abinda yake tafe dashi. Wanka tayi ta fito ta shirya tayi komai a kan idonsa, hakika ya shiga tashin hankali sosai amma da yake yana iya sarrafa kansa beyi yunkurin yi mata wani abu saboda ba abunda ya shigo dashi kenan ba. Tana gyara daurin dankwalinta, ya cimma inda take, ta mirror ta ganshi a tsaye a bayanta...........Gyara daurin dankwalin da ba tayi ba kenan ta fara kokarin barin gurin. 'Kungunta ya riko ya dan janyota jikinsa, ta kalleshi da mamakin abinda yake a fuskarta. Dankwalin ya fara kokarin daura mata kawai ta zuba masa ido tana kallon ikon Allah. Sai da ya daura mata tsaf! sannan ya kai ta gaban mirror domin taga ni. Sosai tayi mamakin yanda ya iya daura dankwali kamar mace, daurin yay mata kyau sosai, ta dan saki fuskarta amma bata iya yi masa godiya ba, juyowa tayi kawai taji ta a jikinsa, da yake yana daf da ita. Ya dan rungumeta na second kafin ya cire ta daga jikinsa hannunta ya rike suka samu gurin zama. Yanda yake kula da ita yasa jikinta ya mutu, abinda take bukata kenan dama, wasa take da yatsun hannuwanta tana sauraran maganarsa. "Me yasa baki da sirri? me yasa zaki kira Asp a waya ki kai masa 'korafi akan abunda bai taka kara ya karya ba, Zinatu mai yasa kullum kike daukata a matsayin macuci azzalimi, ko kina tunanin Asp din ya fi ni sonki shiyasa kika fi yarda dashi a kaina, tsayin kwanakin ki a gidan nan mai nayi miki na cutarwa, ko don na gyara miki kuskuranki shine kike ganin kamar ina cutarki." Fashewa tayi da kuka ta daga masa hannu da fadin." Kaga baka da bakin da za kayi min wata magana a yanzu, ka dauko ni daga gaban iyayena kazo kana kuntatawa rayuwata, me yasa kai baka da uzuri a rayuwa, duk abunda na fada ai ba 'karya bane kuma kai ma ka san gaskiya amma kake takewa, Asp kuma da kake magana a kansa dole na kira shi domin na sheda masa abunda ke faruwa, saboda a gurinsa kadai nake samun sassauci." Zuciyarsa ta cunkushe da tsananin bacin rai da takaicin kalamanta, hakan ya nuna masa cewa Asp din ya fishi matsayi a zuciyarta. Yayi namijin kokarin danne masifaffan kishin dake taso masa kafin yace.''Kina nufin Asp din ya fini iya kalamai kenan."? Ba ta iya munafurci da kumbiya-kumbiya ba, wannan dalilin yasa take zaune lafiya, ta kalleshi da fadin." Eh shi baya zagi na duk abunda zanyi yana kokarin nusar dani cikin saukin kai, amma kai kullum cikin aibata ni kake har ka iya fitar da hannu ka tsinka min mari! shin kai kad'ai ne kake da 'yan uwa? nima ba daga sama na fad'o ba." Yace." Wannan ne dalilin da yasa kika kira shi a waya kenan."? "Eh shine dalili." Ya girgiza kai da fadin.'' Okey bari nai miki magana ta 'karshe cewa duk sanda wani sa'bani ya gifta a tsakaninmu ki ka sake kiran sa a waya wallahi tallahi kinji na rantse da Allah sai na kwace wayar hannunki wannan shine hukuncinki." Kallonsa tayi da mamakin furucinsa a tare da ita. Ganin yanda fuskarsa take a murtuke yasa ta gazgata cewa zai aikata abinda ya fada, kawai sai ta dauke kanta daga kansa tana zumbura baki. Ya cigaba da cewa." Tun da muke abotarmu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakanin mu ba sai ta dalilinki, to ina so na sheda miki cewa ke baki isa ki shiga tsakaninmu ba dole na dauki mataki a kanki idan yaso sai kiji dadin kirana da macuci da hujjah."! Ita dai ba tace masa komai ba, har ya 'karaci fad'ansa ya tashi ya fita bata tanka masa ba. Fitarsa daga dakin da kamar minti biyar Marakisiyya ta shigo, suka gaisa kafin ta sheda mata cewa ta shirya mata abun kari. A ya mutse ta kalleta da fadin." Marakisiyya yanzu bana sha'awar komai sai funkaso saboda haka kije can sashen masu gidan ki basu uzuri na." Tace." Shikkenan an gama ranki shi dade.'' Da sauri ta tashi ta fita domin isar da sa'kon uwar dakin nata. Hamra'u ce ta shirya masa abin kari mai kyau! ta kuma yi ado da kwalliya tamkar wata amarya, bayan ta hada masa komai sai ta zauna a gabansa tana bashi labarai irin na ban dariya, yana break fast din yana sauraranta sosai yake jin dadin abincinta da labaran da take bashi fuskarsa sake sai murmushi yake.........Ita kuwa farin ciki mara misaltuwa ya cika zuciyarta dama babban burinta kenan tasa farin ciki a zuciyarsa ta kuma janye hankalinsa, don dai kada ta wuce gona da iri ne amma da tuni ta bashi abincin a baki. Cikin wannan halin Marakisiyya ta shiga ta samesu. Ita kanta sai da taji wani iri a zuciyarta, haushin Hamra'un ya rufe ta a ganinta hakan kamar bai dace ba. Gabadaya hankalinsu ya koma kanta, daga can gefe ta tsuguna kafin ta fadi abunda yake tafe da ita. Yayi jim! na minti biyu kafin yace." Okey babu damuwa je ki sheda mata cewa za'ayi mata abunda take bukata." Hamra'u ta kalleshi da mamakin furucinsa, idan bata manta ba, a kwanakin baya da bakinsa yake cewa zai dauki mataki akan matar tasa amma shine yanzu ya kar'bi Uzurin ta, to ita dai gaskiya ba za tayi mata bauta ba idan ma tunaninsa kenan. Bayan fitar Marakisiyyar ya kalleta da fadin." Kin ji Uzurin 'yar uwarki ko."? Ta d'anyi murmushi da fadin." Eh naji yaya na." Yace."Kiyi hakuri ki shiga kicin ki mata abunda take bukata kafin komai ya daidaita." Ta d'an sauke munafukar ajiyar zuciya kafin tace." Yaya na ban iya funkaso ba domin wancan lokacin ma Uwale ce tayi mata ni idan nayi lalacewa yake." Yace."Ayya! kinga yanzu kuma Uwale bata jin dadin amma bari na kammala na sheda mata ko zata iya shiga kicin din." Ranta ya 'baci jin maganarsa, wato uzurin matarsa har yafi rashin lafiyar kakarsa......Tai shuru bata sake wata magana ba, da kansa ya dan fahimci wani abu amma bai kawo cewa kishi ne ya ha nata bin umarninsa ba. A kwance ya samu Uwalen tana bacci, baya tsammanin zai tashe ta, don haka sai kawai ya fito daga dakin, ya kama hanyar fita, hankalinsa gabadaya yana kan gimbiyar ganin har sha daya ta gota bata ci abinci ba. Ganin yana kokarin fita yasa da sauri tace."Yaya na akwai fa maganar da nake so mu yi." hannu kawai ya daga mata da fadin." Idan na shigo da daddare zamu tattauna." bai jira amsarta ba ya kama hanya ya fice. Ta ciji yatsa cike da bak'in kishi a zuciyarta ta kwashe kayan karin kicin ta nufa ta wasu irin tunane-tunane a zuciyarta. Shigarsa dakin besa ta dago kai ta kalleshi ba, hankalinta gabadaya yana kan wayarta hira suke da Sakina tana bata labarin irin rayuwar bakin ciki da take a gidan auran nata. Maganarsa ce ta dauki hankalinta ta daga kai ta kalleshi........"Kin tura baiwar ki kina bukatar funkaso ko."? Ta gyada kai alamun E......Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Uwale ba ta jin dadi ita kuma Hamra'u tace bata iya ba me yasa ba zaki sanya hadiman ki suyi miki ba." Ta dan ja numfashi kafin tace." Kawai nafi bukatar na gurin Uwalen yayi min dadi a wancan lokaci amma ko da wasa kada kasa wata banzar bazara k'azama tayi min abinda zan ci domin ban amince da hakan ba." Ya dinga auna maganganun ta a cikin ranshi yace." Wacece banzar bazara kuma."? Ba tare da ta kalleshi ba tace." Kafi ni sanin ta ka fad'a mata cewa duk abubuwan da take aikatawa ina da labari amma idan na tashi yi mata hukunci ba za taji da kyau ba." Maganar ta bashi dariya amma beyi ba, ya kalleta da fadin." Magana muke akan abincin da za kici babu ruwana da banzar bazarar da kike magana ni bukata ta a yanzu kici abinci." Kai tsaye tace." A bani abunda nake bukata mana." Ya kai minti biyu yana kallonta kafin ya juya ya fita, ta bishi da kallon takaici! tsaki taja tana sake jin haushinsa a zuciyarta a ganinta duk shine ya bawa yarinyar dama shiyasa take abunda take so, Marakisiyya duk ta sheda mata abunda ta gani da idonta, za kuma ta dauki mataki a kansu ba'ki d'aya." *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/18/22, 12:31 - Binta: *GJ* *73&74* Yana jin kunyar kiran Asp a waya saboda abunda ya faru a tsakaninsu, yana kuma tunanin yanda za'ayi yarinyar ta samu abunda take bukata, bashi da ra'ayin yawace-yawacen gidan abinci, wannan dalilin yasa yake tunanin kiran abokin nasa koda irin taimakon da zai masa, shi a kankin kansa ya san hakan bai dace ba cewa da abinci da duk abun bukata a gidansa amma ya tafi wani gidan barar abinci, babu shakka ba komai ne ya janyo masa hakan ba face rashin samun nagartaciyyar mace. wacce bata kiyaye cikinta ba ballanatana ta kiyaye nasa da nauyin yake a kanta. Ajiyar zuciya ya sauke ya yanke shawarar kiran Asp din yayi......Suka gaisa da juna kamar wani abu bai faru a tsakaninsu ba, cikinsu kowanne yay kokarin danne abun a ransa. Cike da jin nauyi yake sheda masa Uzurinsa. Asp din yay murmushi da fadin." Haba ai wannan ba'a abun damuwa bane
Chapter 50 · 0% Book details