Sashe 48
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
aniyar a cikin zuciyata, domin na jima ina son yarinyar itama tana sona, ba tun yau ba yarinyar take dawainiya dani, ta sadaukar da rayuwarta kaf a kaina, sannan kuma tayi min hallacin da ba zan ta'ba mantawa dashi ba, mutukar na cika dan halak dole na saka mata da alkairi, auranta kad'ai shine sakayyar da ya cancanta nayi mata, saboda haka Kawu kayi hakuri da wannan abu da ya faru hakika banji dadi ba kuma zanyi wa tufkar hanci insha Allah abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba." Kawu Ado yace." To Alhamdulillhi naji dadin wannan magana, kuma nayi farin ciki daka mutuntani tare da sauran 'yan uwanka, haka ya kamata d'a na halak ya kasance duk rintsi kada ya k'yamaci asali da tushen sa domin duk abun da ya zama a duniya bai isa ya canzawa towo suna ba, saboda haka wannan kalaman naka sun faranta min rai mutuka da gaske, Allah yayi maka albarka ya kuma kare ka daga sharrin masu sharri." Ya amsa tare da jin dadin irin adduoin da yake masa. Gabad'ayansu har Uwalen ya tattarasu suka nufi sashen Gimbiyar, da yawa daga cikinsu hakan be musu dadi ba, saboda tsira da mutuncinsu, koda suke 'yan kauye ai mutane ne kamar kowa me zai sanya a dinga k'yamatar su har idan suka zo guri a dinga toshe hanci, wannan shine abinda yafi 'bata musu rai. Suka cika falon taf don wasu ma a tsaitsaye suka tsaya saboda babu gurin zama, ya kallesu da fadin." Ku dan saurari fitowa ta yanzu." suka hada baki gurin amsawa. Koda ya shiga dakin bacci ya same ta tana yi ga airpix a cikin kunnanta wayar kuma na saman kirjinta..........'Karamar riga ce a jikinta mai karamin hannu gabadaya jikinta a waje mussaman cinyoyinta, tsigar jikinsa tana tashi ya 'karasa kusa da ita, ya daidai ta nutsuwarsa, kafin ya fara kiran sunanta. Shuru bata motsa ba bacci take sosai. Yasa hannu ya cire airpix din kafin ya bude muryarsa da kiran sunanta.....*"ZINATU."* Bata motsa ba ballanatana ta san shigowarsa dakin. Ya zauna kusa da ita yana jan kafarta.........Ya jima yana jijjigata kafin ta bude ido da mayen bacci a tare da ita take ganinsa dishi-dishi, ya sake jan kafarta da fadin." Ki tashi wane irin bacci ne haka saboda rashin hankali kuma kin sanya airpix a kunne kina bacci dashi. Ta bude idonta sosai tare da kokarin tashi. Kawar da kanshi yayi sakamakon hango pant d'in ta, rigar da ita gwara babu domin abunda ta rufe kad'an ne a jikinta. Tashi tai ta kama hanyar toilet sassan jikinta na wani irin rawa sakamakon rashin sutturar arziki da babu a jikinta. Ajiyar zuciya ya sauke bayan shigar ta toilet din ya cigaba da dabarar danne k'ulafucinsa. Jin shuru bata fito ba ya tabbar masa da wanka take, tsaki yaja ya tsaya kofar toilet din da fadin. " Malama kiyi ki fito akwai jama'ar da suke jiran ki. Jin abinda yace yasa ta kudiri aniyar 'bata masa rai domin dai ta riga ta san jama'ar basu wuce mutanan k'auye 'yan uwansa masu wari da hamami! Koda ta gama wankan kin fitowa tayi tai zamanta a toilet din tana saka wasikar jaki, tayi hakan ne domin ta bata masa rai bayan haka kuma tana gujewa kanta sha'kar wari! wanda ka iya janyo mata tashin zuciya. Buga kofar yay da karfin gaske! ya bude murya da fadin." Ke! wai ba zaki fito ba ne."'? Tsaki! taja ta mike tana zumbura baki da gunguni ta bude kofar, suka hada ido, ganin yanda idonsa yayi jawur yasa gabanta fad'uwa, tai saurin ra'be shi ta wuce tana jin shakkar sa a zuciyarta. Ya bita da wani irin kallo kafin ya girgiza kanshi ya bita har dressing mirror din da take zaune. Tana shafa mai tana sauraran maganganunshi. "Duk irin rashin mutuncin da ki kayi wa 'yan uwana na samu labari! ki saurareni da kyau! domin ki kiyaye abunda kan iya kawo rashin jituwa a tsakaninmu, zan iya hakuri da duk abunda za kiyi amma ba zan iya kawar da kaina gurin ganin kinci zarafin iyaye da kakanni na ba, bani da kowa sama dasu, domin su sukayi min duk wani gata har na girma na kai munzali, wallahi na rantse miki da Allah akan su, babu abunda ba zan aikata ba, saboda ni na san kima da mutuncin iyayena, mutukar kina so mu zauna lafiya to dole ki mutunta min su ki kuma darajasu." Ko gezau! duk maganganusa ba su isa su hana ta fadin gaskiya ba, ta kalleshi da fadin.'' Ina so a fada min abunda nai musu wanda ya sanya ka zuwa ka tsaya a kaina kana kalubalanta ai na dauka sai mutum yay laifi za'a tuhumeshi."? Yaga kamar ta raina masa hankali da jan ido yace." Zaki 'karyata maganarsu ne? wanda ya tabbatar min da abinda ki ka 'aikata ba zai miki 'kaharu ba idan yayi miki k'arya yayi wa? ki kiyaye nifa."? jikinsa na tsuma! ya ke maganar. Man shafawa ta dan lakato tana mutsikawa a hannuwanta kafin tace." Sai kaje ka tambayi shi wanda ya fada maka cewa naci mutuncinsu idan sharri nai musu, mai zai sanya su shigo in da nake suna wari! da tsamin hammata."!! Hankalinta kwance take maganar domin bata tsammanin cewa hukuncin mai tsauri zai bi ta kanta ba.........Wani bahagon mari yayi mata da bayan hannunsa, wanda ya sanya ji da ganinta daukewa na wucin gadi. Kai ta sunkuyar kasa tana mamakin al'amarin! ita ya Mara akan wasu gigidadawa!! wani katon bakin ciki yazo ya tsaya mata a wuya. Yana tsaya a kanta yana surfa mata bala'i tare da jajjada mata muhimmacin mutanan da take rainawa har tana fadin duk maganar da ta ga dama a kansu. Ta danne kukan da yake kokarin kufce mata tace." Ko zaka ce 'karya nake sai na fadi gaskiya domin kai kanka wari kake ballanatana su, na fad'a din." Hannu yasa ya gwa'be bakin! zafi ya hanata karasa maganar dake bakinta............Ido ta zuba masa ganin yanda fatar goshinsa duk ta tattare sai wani irin gumi yake kamar ba sanyi safiya ba. Yanda yake rawar jiki yana kai kawo a kanta yasa ta tsorata, babu yanda ta iya haka ta shirya jikinta, ya nuna mata hanyar fita da hannunsa, ba tace komai ba tayi gaba zuciyarta na wani irin zafi! tsaki mai tsayi yaja kafin yabi bayanta. ZINATU ba tayi musu 'karya ba da gaske take tsami da wari suke shima ya san haka ya kuma ji warin a hancinsa amma saboda rashin gaskiya ya take. Rashin gurin zama yasa taja ta tsaya a bakin kofa, ta daure zuciyarta da fadin." Ina kwananku."? Wasu daga ciki sun amsa wasu kuma sukayi mata kallon uku saura kwata *Yo a fad'awa mutumin k'auye iyashege Bata damu da hakan domin ba sune a gabanta ba burinta taje ta amayar da aman da yake taso mata. Jinsa kawai take yana mata bayaninsu da nuna mata muhimmanci su a tare dashi, yawu ya cika mata baki, duk ta rasa yanda za tayi, itama a karan kanta bata san abinda take sai dai don ba yanda za tayi ne. Duk irin dauke kan da take yana lure da ita, ransa idan yay dubu ya baci! ya daure ya cigaba da cewa. " Kada kiyi tunanin don kin fito daga gidan sarauta kinfi wasu kima da daraja! to ina so ki san cewa babu wanda yafi wani a wannan duniyar face wanda yafi bautawa Allah, duk daya muke a gurinsa, kuma shi yayi na burni yayi na kauye, kana kuma shi yayi mai kudi yayi talaka, yayi sarki yayi bafade, mulki talauci arziki duk shi yake bayarwa ga wanda yaso, saboda haka ni 'yan uwana sun fi min komai a duniyar nan don haka ba zan lamunci kici zarafinsu ba, ina so ki rike wannan, ki zauna a matsayinki na matata, suma su zauna a matsayinsu na jinina wannan shine abinda nake so ki rike kuma kiyi aiki dashi." Uffan bata iya cewa ba to yaushe ma ta samu sararin maganar bakinta cike da yawu. Tana kallonsu suka tashi daya bayan daya suka dinga fita, falon ya rage su biyu, harararsa tayi kafin ta bude daki ta shige kai tsaye toilet ta nufa ta zubar da yawun bakinta, tsugunawa tayi zuciyarta na cigaba da hantsilawa......Dole dai sai da tayi aman sannan ta samu sassauci. Tana fitowa ta samu Baraka tana gyara dakin Kan Sofa ta kwanta tana mayar da numfashi tace." Baraka don Allah kiyi kokari a falon nan wannan wari duk ya fice kinji ko." Tace." To ranki ya dade insha Allah bari na gama gyara miki dakin." Kai ta girgiza kafin ta rufe idonta tana kukan zucci! wai dangin mijin da take aure sune kucakai masu warin daud'a daddawa da tsamin hammata! wannan al'amari yana daure mata kai, a mafarki ba ta'ba tsammanin cewa za ta auri d'an 'kauye ba. Hamra'u a ranar da al'amarin ya faru kamar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda farin ciki taji dadin yanda ya nuna mata muhimmancinsu bayan haka kuma tayi farin ciki sosai da maganarsu ta karshe da Kawu Ado, domin kafin su tafi sai da ya jaddada mata cewa ta kwantar da hankalinta UMARU zai aureta da ikon Ubangiji, wannan shine abinda sanya farin cikinta kara nununkuwa. Sosai ta dauki fushi dashi saboda abunda yay mata yayi masifar 'bata mata rai, da farko tayi tunanin zama dashi saboda salon soyayyarsa amma yanda yake kambaba darajar 'yan uwansa yasa duk taji ya fice daga zuciyarta, tunaninta ya za'ayi ta samu namiji wanda yay daidai da rayuwata wanda kuma ya iya love irin nashi. 'Bangaranshi bai damu da shan k'amshin da take masa ba, domun shi a ganinshi bai ga abun 'bacin rai da daukar gaba ba, kuskure tayi wanda ya cancanta da ayi mata gyara akai shiyasa ya tsaya kai da fata ya nuna mata kuskuranta saboda a cikin zuciyarsa ya kudirci zaman lafiya da ita, saboda baya so famliy nasa su tsaneta saboda mugun halinta, shi zai iya jure duk abunda za tayi masa amma ba zai yarda taci zarafin wani nasa ba. Haka suka cigaba da zama tsayin kwanaki uku wata mu'amular arziki bata sake hadasu ba kowa yana gurinshi, sai dai shi da safe yana shiga ya