Sashe 11
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ya dan ja numfashi, jin yanayinsa yana sauyawa, ya fara kokarin cireta daga jikinsa. Ta dage! harda gyara kwanciya kamar wacce take kan katifa. Mamaki sosai ya rufeshi, tunda yaji tayi shuru kuma numfashinta ya daidaita ya san ta samu sassauci bayan haka kuma jikinta ya daina karkarwa da alamar zazzabin yayi nasa a guri, amma meye amfanin abinda take. Namijin kokari yayi ya cireta daga jikinsa, babu kunya ta zuba masa ido kamar wanda yayi mata laifi. Ya saisaita yanayinsa kafin yace."Sannu kina bukatar magani ko."? Shuru tai na minti biyu kafin ta kalli hannunsa, maganin ne yake kokarin sanya mata a baki. Tasa hannu ta buge kwaryar maganin gabadaya ya zube kasan gurin da jikinsa Cike da takaici da bacin rai yake kallonta, ta 'bata rai da fadin.'' Wane irin magani ne wannan me wari zaka sa min a baki." Ya hadiye b'acin ransa wannan karan bai sassauta murya ba da yanayin maganarsa yace." Ke ki kace jikinki na ciwo maganin karfin jiki ne." Ta'be baki tayi da fadin." Bana bukata." Bece komai ba ya tashi daga gurin tare da jin takaicin abinda tayi. Ta kalleshi da fadin." Ka bani aron wannan rigar ta jikinka na rufe jikina da ita tana da d'umi." Uffan bece mata ba ya bar gurin, minti uku ya dawo da irin rigar a hannunsa. Ya mika mata, ta kalleshi da fadin." Ta jikinka nake so."? Yace."Duk daya ce da wannan din." A yamutse tasa hannu ta kar'ba tana kokarin sawa a jikinta ya bar gurin . Sai kace suddabaru! hankalinta ya gaza kwanciya koda tasa rigar ta kwanta domin jin d'umi kasa nutsuwa tayi ta tashi zaune tana rawar jiki.......Me yasa ta kasa samun abunda takeso a jikin rigar! ita a tunanin kaurin rigar ne ya saukar mata da nutsuwa sai taga akasin haka. "Ba rigar bace mai rigar ne yasa miki nutsuwa da kwanciyar hankali." zuciyarta ce take mata wannan maganar. Da sauri ta k'aryata zuciyarta ta sake rurrufe jikinta da rigar tana korar abinda zuciyarta ke raya mata, babu yanda za'ayi ta amince da cewa wannan gantallalan ne zai zama garkuwa a gareta. Daya daga cikin yaranshi ne ya kawo mata ruwa da asuwaki da abin kari. ganin yanda maigidansu yake bata kulawa ya sanyashi gaisheta, bata amsa ba sai wukalantaccan kallon da take masa shida tarkacen da ya ajiye a gabanta. Girgiza kansa yayi baki a cije! ya bar gurun ba don kar ya dauki mataki akan yarinyar ya samu matsala da maigidansa ba, da sai ya fasa mata baki domin yaji ciwon kallon banza da tayi masa. Har gari yayi haske sosai tana takure cikin rigar har yanzu ta kasa tantance a wane iri yanayi take, Can ta hangoshi yana zuwa inda take, ido kawai ta tsira masa babu kiftawa sosai take mamakin tsananin kamar da yake da jarumi(Barbahs) tana bala'in son jarumin saboda jarumtarsa da iya soyayyarsa idan yana abu a film kamar gaske, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin karyata abinda zuciyarta ke raya mata a kansa. Tsaf yake cikin shirin fita, ya sauya rigar jikinsa doguwar jallabiya ce browan mai gajeran hannu sai ya sanya dogon wadon jens kanshi nannad'e da bakin yadi yayi gammo sosai! idanuwan nan rad'au! da bakin kwalli! kafad'unshi rakwacam! da tarin kayan farauta, har da irin doguwar bindigar nan, hakanan wuyanshi da damtsan hannuwansa wasu irin abubuwa ne a d'aure.! kafafunsa sanye suke da wani irin takalmi mai tarin igiyoyi a jikinsa. Tunda ya tsaya a kanta take kallon kafarshi, mamakin kyawun kafar take, bata ta'ba kallon kafarsa ba sai yau, faratanshi tas babu kazanta sai kananun gashi dake kwance saman yatsun kafar. A tsorace ta dinga sauke ajiyar zuciya tana kokarin kawar da idonta daga kan kafar. taji muryarsa cike da wani irin amo!! "Tashi zaune." Yanda ya fadi maganar babu wasa yasa ta tashi tana kallon fuskarsa, babu fara'a yace." Zanja ragamar yara na wani aiki a cikin dajin nan, ina so ki kula da kyau! kada kiyi kuskuran barin gurin nan! ki kiyaye! mutukar kina so ki cigaba da rayuwa a duniya. Kuka tasa tana kallonsa da fadin." Me yasa ba zaka tafi dani ba, saboda tsabar mugunta shine zaka had'a kan yaranka ku tafi ku barni ni kad'ai! bayan ka san dajin bashi da kyau komai yana iya faruwa da rayuwata." Yace." Nan gurin yana da tsaro bayan haka kuma gurin da zamu shiga yana da had'ari shiyasa na yanke shawarar barin ki anan sai yafi miki kwanciyar hankali." Ta girgiza kai tana shakar hanci tace."Aa nifa ba zan zauna ba wallahi ko kun tafi sai na biyo bayanku." Yanda tayi maganar babu alamun wasa a tare da iya yasa yaji shakkar tafiya ya barta. Ya kalleta a lokacin da take kokarin mi'kewa. "Na fad'a miki abinda yake da akwai kina kuka ko."? Hannu ta d'aga masa da fadin." Nifa ba zan zauna ni kadai a wannan gurin ba." Tana gama maganarta ta kama tana tafiya babu takalmi a kafarta, ga kanta babu dankwali." "Ki tsaya nan nace."! Cikin tsawa yayi maganar. taja ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Yaja tsaki tare da komawa baya, takalmi ya lalobo mata tare da wani farin yadi. Ya karasa inda take da fadin." Kar'bi wannan ki rufe jikinki dashi." ba tayi musu ba ta kar'ba, ta lullube jikinta har kasa. Ya bata takalmi ta tsuguna tana kokarin sawa, ganin tana 'bata masa lokaci yasa ya tsuguna da kansa ya d'aura mata takalmin sosai yanda duk wuya ba zai fita a kafar ba. Hannunta ya rike a cikin nasa suka nufi inda ayarin jama'arsa suke tsayuwar jiransa, ganinsa tare da ita ya basu mamaki! amma babu wanda yayi magana a cikinsu, yayi gaba suka rufa masa baya. karnuka wasu a gaba wasu a baya, sai kuma bushe-bushe da gangi! da ya cika dajin! *Free pege ya kusa 'karewa a hanzarta biyan kudin karatu.* *0542382124...Binta umar gtbank* a tura sheda ta wannan number...... 07084653262 *Ayi kokari a duba wannan _Mijina baya bani_ kulawa bayan kafin muyi aure yana bani kulawa da duk wata soyayya ___________ *Watakila kece kika janyo faruwar hakan, na farko dai namiji yana da bukatar kulawa, ta kowane fanni, watakila kafin kuyi aure ke din 'yar gayu ce mai tsafta, bakya rabo da kwalliya kamshin turare ako da yaushe, sai bayan auranki kuma ki mayar da kanki jakar mata, da kuruciyar da komai ki shiririce wanka ma sai kiyi kwana biyu ko uku ba kiyi ba mussaman a cikin wannan lokacin, sai kiyi kwaskwarima ki shafa mai akan dauda kina tsamin hammata! to me zai hana namiji bai kyamace ki ba, babu mummunar mace, kuma komai shekarunki mutukar kina da miji to kada ki zauna a lalace domin hakan zai janyo miki bacin rai mai tsanani mussaman idan kina da abokiyar zama to zaki zama koma baya ta kowane fanni, tsafta jigo ne a cikin zamantakewar aure don haka ki kula da wannan abubuwan.* *1- Wanka sau biyu a rana* *-2 yawan aske sassan dake fitar da gashi a jikinki* *4-Zama cikin kamshin turare mai sanyi da sanyaya zuciya* *3-Kitso duk bayan sati ko kwana goma kuma kafin ayi kitson a wanke kan* *5-Wanke baki sau biyu ko uku mussaman idan zaki kwanta* *6- Taraiyaya da iya kalami mai dadi a lokacin da kike tare da mijinki* *7-Sauya kalolin abinci masu inganci* *8- Sanya kaya na mussaman domin zuwa turaka* *9- Shagwaba wata abace mai muhimmanci* *10- Banda yawan dariya mara ma'ana a gaban miji murmushi zaki yawaita yi masa kina sarrafa kwayar idonki a kansa kina bashi labarai masu dadi.* _Mutukar kin kula da wannan to zaki kama mijinki a hannu kuma zai baki kulawa ta mussaman_ *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* Dala dari Katin Airtal ko Mov 1/12/22, 20:33 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________