Sashe 81
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da "Ameen ya rabbi ai ba wani abu bane Uwale ban dauki Umar a matsayin aboki ba kamar yanda ki ka fada dan uwana ne! wannan dalilin yasa hankalina ya tashi ganin yanda abubuwa marasa kyau suke faruwa dashi. tabbas akwai abinda yake lullu'be kuma muna rokon Allah yayi mana maganin ko menene. Tace." Insha Allahu kuwa Ai babu abunda yafi karfin Ubangiji kai dai Allah ya saka maka da alkairi." Ya amsa da "Ameen kafin yayi musu sallama ya tafi muhallinsa. Hamra'u tayi zaune a daki tana sakawa da kwancewa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dauki wayarta number sa ta kira. Sai da ta kira sau uku ana hud'un ya daga! kafin ma tayi magana ya buga mata tsawa! dama zuciyar a kusa take ana fagen daga!! Jikinta ya shiga rawa! sai ta manta ma abinda za ta fad'a Yace." Wai shin ke ban ha naki kira na bane? da kaina nace ki bari idan na samu isheshshen lokaci zan kira ki me yake damunki ne."? Hawaye masu zafi suka cika kwarmin idonta! kamar ta kashe wayar sai dai ta daure murya na rawa tace ." Dama zan fada maka cewa Zinatu t.........! jin ta ambaci sunan wacce ya tsana! yasa da gaggawa ya kashe wayarsa ba zai saurari karshen maganar ba ballantana ransa ya 'baci! *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/23/22, 21:09 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *119&120* Kasa daurewa tayi ba'kin cikin abinda yayi mata yasa ta kasa fita falon, nan ta kwanta kan gado kuka mai cin rai ya k'wace mata, ita kam har yanzu ta kasa fahimtar inda ya dosa kullum babu kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu, ba dama tayi masa magana sai ya kyareta! ko ya hantareta! gabad'aya ta kasa shawo kansa a lokacin da ba suyi aure ba ma yafi kulawa da ita, yanzu kuwa da ya cancanta ace ya kula da ita hakan bai samu ba, wannan al'amarin yana bala'in damunta. Haka ta zama mujiya a cikinsu, dan gabad'aya sai ta tsargi kanta ta dinga ja da baya tana wani abu irin abu na marasa gaskiya, Uwale kam tunda ta fahimci cewa ita da uwarta basu da gaskiya sai kawai itama ta shata mata layi, ta daina sakar mata fuska a yanzu babu kyakykyawar mu'amula a tsakaninsu. Tafi mayar da hankalinta kan Zinatu saboda tana tausayawa halin da take ciki, tunda ta dawo take fama yau da lafiya gobe babu sai ya kasance kusan kullum Uwalen tana can sashen nata domin debe mata kewa duk da cewa tana tare dasu Baraka amma kasancewar Uwalen a tare da ita ya faranta mata rai mutuka. sha'kuwa mai kyau ta shiga tsakaninsu. 'Bangaran Hamra'u kuwa abin duniya ya isheta, kullum sai ta zubar da hawayen takaici gidan kaf sun hade mata kai sun mayar da ita saniyar ware babu wanda yake yi da ita, sai ta fara rama a tsaitsaye saboda damuwar da ta sanya a ranta dole itama tabi ayari mutukar tana so tayi rayuwar farin ciki a gidan. Sai ta dingi shiga sashen Gimbiyar, al'amarin da ya basu mamaki mutuka! amma basu nuna mata komai ba, tun bata sakewa dasu har dai ta saba ta daina dari-dari domin ganin ta sauya hali ya sanya Uwalen sassauta mata, wannan ya sanya hankalinta ya kwanta a gidan, ita ta cigaba da yi wa Zinat din d'awainiya har wankin undis wani sa'in ita take wanke mata ta tsafe mata kitson kanta kana ta kitsa mata sabo, idan kafafunta sun dameta da ciwo itake matsa mata. Abun dai har ya soma damun Zinat din saboda bata so wasu daga waje suga abunda yake faruwa su d'ora ayar tambaya a kanta shiyasa tayi wani tunani akan al'amarin. Da fara'a ta shiga ta sameta kan doguwar kujera a kwance tace." Aunty Gimbiya jikin ne ko garin ina fata dai babu abunda ke damunki."? Ta ya mutse fuska da fadin." Kinga wallahi tun safe na tashi da ciwon mara asibiti nake so muje yanzu." Tace." Eh lallai zuwa asibitin yana da muhimmanci bari na shedawa Uwale." Tana kokarin tashi tace." Okey bari na shirya kafin ki dawo." Daki ta nufa tana cire kafa da kyar! ciki wata biyar kacal yayi girma sai suddubaru iri-iri! Uwale tace." To ko na shirya muje tare."? kai ta girgiza da fadin." Ki zauna kawai yanzu zamu dawo." Tace." Shikkenan amma yana da kyau kafin ku tafi ki shedawa mijinku koda ta waya ne." Tace." Uwale bana so na kira shi yayi min fad'a ki bari kawai mu tafi." Tace." Aa dole ki fada masa hakkinsa ne." A sanyaye tace." Shikkenan. Cikin tararrabi da jin tsoro ta kira shi, akaci sa'a ya dauka bai kuma yi mata fada ba, su gaisa a mutunce ya tambayeta gida tace." Kowa lafiya lau." Shuru tayi tana nazarin maganar dake bakinta. tuntuni tasan baya kaunar tayi masa maganar matarsa amma ya zama dole ta sheda masa abinda yake faruwa. Yace." Hamrau ko da matsala ne."? Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Dama za muje asibiti ne da Aunty Gimbiya bata jin dadin jikinta." Yaja wani dogon tsaki da fadin." Ba da yawu na ba, kada ki kuskura kije ko'ina." Ta bude baki kenan za tayi magana ya kashe wayarsa! ta tsirawa wayar hannunta ido tana mamakin irin k'iyayyar da yake nunawa matarsa kamar wacce ta kashe masa uwa da uba. A sanyaye ta fito daga dakin ta shedawa Uwale yanda sukayi......Cikin bacin rai! tace." Kamo min wayar tasa muyi magana." Koda ta kira shi yana kallo har ta katse bai dauka ba, ta dinga kira tana katsewa, kwata-kwata yaki dauka. Tace." Wallahi yaki daga wayar na kira ya kai sau bakwai. Murmushin takaici tayi tana girgiza kai! hakika Dayyiba bata kyauta ba ta shiga tsakanin ma'aurata ta sanya musu kiyayyar junansu. Sosai fa take jin jiki dan koda ta shiga dakin da niyyar sauya kaya kasa komai tayi ta sake kwanciya tana kiran sunan Allah, cikinta ne yake mata wani irin ciwo ga wani uban gumi da take shar'bawa! Cikin wannan halin ta shiga ta sameta, bahaushe yace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne! Hamra'u hankalinta ya tashi ganin yanda take murkususu! duk kiyayyar da take mata sai ta nemeta ta rasa hankalinta ya tashi ta rasa wane irin taimako za tayi mata. A hankali tace." Na shigo dan na sauya kaya amma na kasa saboda yanda ciwon cikin nan ya dameni." A sanyaye tace." Sannu yanzu ya za'ayi? Uwale tace." Lallai sai na kira maigidan na sheda masa abinda yake faruwa, to koda na kira shin sai yace kada muje ko'ina." Ta kalleta tana jin wani irin 'bacin a can cikin ranta, rintse idonta tayi tana tunanin yanda za tayi, ta bud'e idon tare da kallonta tace." Kyaleshi kawai miko min wayata gata can saman mirror." Da sauri ta mika mata wayar. ta lalubi number Asp da kyar ta iya sheda masa halin da take ciki. Hankali a tashe yace." Insha Allahu zan turo Likita zai zo ya dubaki yanzu ya baki magani ba sai kunje ko'ina ba tunda muna tare da kwararrun likitoci a cikin gidan. Tace." To shikkenan nagode Allah ya saka da alkairi." Ya amsa da" Ameen ya Allah." kafin ya kashe wayar ya fara laluben number Likitan da yake da tabbaci a kansa. To cikin ikon Allah tana shan magungunan da likitan ya d'ora ta akai ta samu sassauci a take wahalallan bacci ya dauketa, duk ta rame na lokaci guda. Asp yana tashi daga aiki bai nufi ko'ina ba sai gidan abokin nasa hankalinsa gabad'aya yana kan yarinyar, sai da yaje ya dubata sannan hankalinsa ya kwanta mussaman da ya sameta a zaune ta warware tana cin abinci. Ya dubata sosai ya kuma bata shawarwari masu amfani kafin yayi mata sallama ya nufi muhallinsa. A daran ranar ya samu labarin duk abunda yake faruwa. Koda yake ba labari ya samu ba, hotonan Likitan da ya dubata da hoton Asp da shigarsa da fitarsa duk aka tura masa ta WhatsApp bashi da tabbaci akan wanda ya turo masa sa'kon asali ma bashi da number. Hankalinsa ya tashi ainun! Asp ya zame masa kadangaran bakin tulu, baya gari amma yana shigar masa gida ba tare da izininsa ba, garadan maza suna karakaina a cikin gidansa har cikin dakin matarsa. Kansa ya dinga yi masa wani irin ciwo! tunaninsa gabadaya ta tafi gurin ganin ya samu hanyar da warware matsalarsa, yanzu zargin cikin da yake jikin yarinyar yake, Asp ya wuce gona da iri babu abunda ba zai aikata ba. Cikin rashin tunani da gushewar hankali da tsinkaye ya kira Asp din yana wani irin huci! ya fara surfa masa rashin mutunci! Asp din ya fusata! da karfi ya buga tevur din dake gabansa ya mike tsaye da wayar a kunnansa yana fadin." Umaru ni kake kira fasiki! anya kana da hankali kuwa ko dai ka fara shaye-shaye ne."? Shima a fusace! yace." Bana shan komai! hankali kuma bani dashi mutuk'ar akan na zuba maka ido kana abunda kaga kake so, nifa ba bagidaje bane da zaka dinga raina min hankali. kullum kana bibiyar matata a gindi-agindi dole nayi zarginka, kaje ka