Sashe 89
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kyautuka na bajinta. duk yawansu da suka zo bikin sunan sai da suka samu alkairi daga gurinta suka tafi cike walwala da farin ciki tare da alkairai masu yawan gaske. 'Dayyiba ta sake bazama! neman asiri wannan karan babu sassauci! ta kudiri mummunar aniya! Ta taki nasara samo zazzafar asiri sai dai kuma yana da had'ari tace taji ta gani zata iya. Sai dai cikin ikon Allah kafin ta isa gida Allah ya mantar da ita sharud'an daka a gindaya mata. Ta firgita sosai! sai ta juya domin komawa gurin bokan. Kafin ma ta isa bukkar taji ana katantanwa! da ita ba'a ajiyeta a ko'ina ba sai a kofar gidanta! Baki a murgude kafa da hannaye a shanye! anan gurin kudaje sukayi mata dabaibaiye yawu na dulala a bakinta. Cikin tashin hankali aka shiga da ita gida ana mamakin al'amarin. Labari ya samu Hamra'u ta dinga kuka ta rikice musu lallai sai taje ta duba mahaifiyarta. Dama yana jin haushinsu yace babu in da za taje. Ya riga ya yanke hukunci duk wanda ya sa baki sai ransa ya 'baci! Zinat ganin abinda yake bai dace ba, ta bullo masa ta bayan gida. Suka dinga sa'insa! a tsakaninsu shi yana nuna mata ikonsa ita kuma tana nuna masa rashin dacewar abinda yake, iyaye sun wuce wasa. Ya fusata! yace." Idan ke kike da iko sai ki bata izini taje." Ya buge rigarsa ya fita daga gidan. Sai kawai ta yanke shawarar shedawa Asp halin da ake ciki. Shima ransa ya 'baci sosai. Yace." Suyi hakuri zai magana dashi. To da kyar ya shawo kansa har ya amince. Ya dinga jin haushi koda ya dawo gidan sabgar gabansa yake bai saurari kowa ba itama bata kulashi saboda ta san duk rintsi ba zai kwanta ba sai ya duba yaronsa. Aikuwa wajen sha daya na dare ya shiga dakin. Cikin alamun bacci ta tashi zaune tana kallonsa. Yace." Kin fara bacci ne."? A dakile ta amsa. Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ya jikin abokina ina fatan zazzabin ya sauka." Tace." Eh yanzu dai babu baccinsa yake tun dazu. Ya kunna wayarsa yana dubashi. Yaron yayi wayo sosai watanshi hudu yanzu kamar dan wata bakwai. Yace." Gobe zaku shirya zuwa *Kafur!* amma a ranar zaku dawo dukkanku." Tace." Har ita Hamra'un."? Yace." Eh har ita domin zamanta a garin sam bai da amfani." Cike da mamaki take kallonsa kafin tace." Ya asalin bashi da amfani bayan iyayenta da duk 'yan uwanta suna garin.' Yace." Mahafiyarta bata da kirki mutuniyar banza ce." Ta dinga kallonsa da mamakin maganarsa. Tace." Wai dan Allah me tayi maka ne ka tsaneta haka."? Tsaki yaja da fadin." Ba lallai sai kinji ba amma bari na baki sako idan kun isa garin ki sheda mata cewa duk wanda ya shafeni yafi 'karfinta kuma duk abinda ta k'ulla yana dawowa kunnena." Tace." Kai waye ya fada maka? dan Allah kada ya yarda da jita-jita na mutane. Yace." Mutumin da ya tabbatar min da gaskiyar al'amarin mutumin arziki ne idan kina bukatar magana dashi sai na had'aku." Tace." Ni ina ruwana dashi kuma! sai dai kai daka yarda da maganarsa. Ya buga mata tsawa! jikinsa na kyarma yace." Ki kiyaye bakinki. domin wannan bawan Allahn ya tsaya miki bayan sahalewar Ubangiji shima yana taka muhimmiyar rayuwa a rayuwarki da tuni kina kwance babu lafiya. Ta dinga kallonsa tana mamakin maganganunsa. Wato aljanunsa ne suke sheda masa duk abinda yake faruwa. To ita kam a duniya me tayi wanda mahaifiyar Hamra'u zata cutar da ita. _Ba kiyi mata komai ba tsabar rashin tsoron Allah ne_ *Wanda suke bukatar ayi musu typing da Azimi su d'aga Hannu *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 5/3/22, 14:51 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *BARKANMU DA SALLAH _*RAHMA IDRIS GA GORON SALLAH NAN *127* Da taimakon Zenat shirye-shiryen tafiya k'auyen *K'afur* ya kammala, sunyi tsaraba daidai gwargwado sai dai shi uban gayyar yace babu in da zashi a cewarsa yana da aiki a gabansa, Hamra'u kamar ta fashe da kuka saboda bacin rai! ta lura dashi ya dauki karan tsana ya dorawa mahaifiyarta ta rasa meye dalili, a fakaice ta dinga share hawaye, tausayinta ya rufe Zinat din, yana shirin fita ta sameshi a dakinsa domin ta nuna masa cewa abinda yake wa yarinyar bai dace ba, iyaye sunfi karfin wulakanci duk d:a nagari ba zai so yaga ana wulakanta iyayensa ba. Tana ta magana yayi shuru bai ce komai shirya jikinsa kawai yake, ya zauna gefan gado yana daure igiyar takalminsa, tace." Magana nake da kai ka share ni abinda kake sam bai dace ba, kuma rik'o bashi da amfani ka dai daure kaje ka duba jikin matar nan yanzu idan kuma rai yayi halinsa mai za kace."? Ya kalleta babu sukuni a fuskarsa yace." Da zata mutu da yafi alkairi." Gabanta na faduwa ta dinga kallonsa tana mamakin furuncinsa. Tsaye ya mi'ke da wayoyinsa a hannunsa. "Ni zan fita." ya fada babu wata damuwa a tare dashi. Ta mike da fadin." Gaskiya ka sauya halinka dan wallahi abinda kakewa yarinyar nan ba daidai bane.'' Ya fusata! ya nunata da tsaya da fadin." Wai shin ke kike auranta ne ko kuwa? kada fa kiyi min rashin kunya dan zan 'bata miki rai nace ban zanje ba duk abinda za'ayi aje ayi." Ganin yanda yake magana a hasale! yasa ba ta sake cewa komai ba ta fice daga d'akin ranta a masifar 'bace. Yanayin halin da suka samu 'Dayyiba ya firgitasu, gabad'aya kammaninta sun jirkice ta rame tayi ba'ki'kirin ba ta san ma wanda yake kanta ba. Hamra'u dai fashewa tayi da kuka tana kiran innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! wane irin ciwo ne wannan. Gaje 'yar uwa ce ga Dayyiba itace kuma take jinyarta, nan take sheda musu cewa an kaita asibiti amma har yanzu an kasa gano abinda ke damunta ganin haka yasa suka dawo gida suke na hausa. Ta jima tana jajanta al'amarin kafin ta sauke zazzafar ajiyar zuciya, tasa hannu ta goge hawaye daya sakko a saman fuskarta, ido ta tsira mata, tana kwance kamar jikakken tsumma! sai gwalantu take yawu da majina na dulala, k'udaje na bin jikinta 'Yar uwarta na kore mata da mafici. A sanyaye tace." Allah ya sawwa'ke amma wane irin asibiti ku ka kaita."? Tace." Na gwamnati ne." Ta girgiza kai da fadin." Ba wai na raina na gwamanatin ba, idan babu damuwa yanzu a shirya ta sai mu kaita na kudi idan kun amince insha Allah zanyi komai." Gaje ta share hawaye da fadin." Wallahi da har mun hakura domin munfi gazgata cewa wannan ciwon ba na asibiti bane amma ba za muqi ba, bari Mijinta ya shigo sai a sheda masa. Tace." To shikkenan babu damuwa. Uwale da tunda suke maganar ba tace komai ba sai yanzu tace." To Allah dai ya sawwake ya bata lafiya. Gabadaya suka amsa da ameen." Ta juya ta kalli Hamra'u dake share hawaye tace." kiyi hakuri addua zaki mata ki daina kuka da sanya damuwa a ranki insha Allah zan tsaya muku daga abinda ya sawwaka daga gareni. Ta rike hannunta da fadin "Na gode sosai Allah ya saka miki da alkairi, abinda nai miki ki yafe min." Ta rungumeta da fadin." Baki min komai ba Hamra'u zaman tare ne, idan ma kinyi min na yafe miki Allah ya yafe mana baki daya." Uwale da Gaje suka amsa da "Ameen cikin yanayi na alhini da damuwa. To koda Malam Shafi'i yaji maganar bai yi jayayya ba, lokaci guda ya amince domin gabadayansu hankalinsu ya tashi da al'amarin. Babban asibiti suka nufa da ita, duk irin shige da ficen da ya kamata ayi a kanta anyi a take a lokacin ta kar'bi account din asibitin ta turawa Magajin Sarki dan uwanta domin ya tura musu zunzurutun kudin da suka bukata kimanin dubu dari takwas da hamsin. Shi kansa Magajin sarkin sai da ya jajanta al'amarin kuma ya tausayawa matar, saboda haka ba tare da bata lokaci ba, ya tura kudin, aikuwa manya likitoci suka tsaya a kanta domin bata taimakon gaggawa. Sai da komai ya kammala sannan ita da Uwale sukayi musu sallama direba ya daukesu suka nufi masaukinsu, Uwale ta shiga hidimar dora abinci, ita kuwa wanka tayi ta kwanta tana hutawa, amma fa har yanzu akwai fargaba da damuwa a tattare da ita, tana da tsananin tausayi shiyasa duk lokacin da ta tuna halin da mahaifiyar Hamra'u ke ciki sai hankalinta ya tashi. Kiran wayarsa ne ya tayar da ita, da lalube ta janyo wayar tana dubawa. kamar ta ajiye wayar domin har yanzu tana jin haushin tsawar da ya buga mata sai kace wata 'yar cikinsa Ta dauki wayar tare da daidaita yanayin maganarta. "Barka da yamma." shine ya gaisheta. Ta amsa da fadin."Barkanmu dai ya aiki."? Yace." Alhamdullhi fatan kun sauka lafiya." A takaice tace."Lafiya lau." Yace." Ina yaro na."? jim tayi kafin tace." Tun bayan zuwanmu Kawu Ado ya turo aka daukeshi yana dai can gidansa. Yace." Naji dadin hakan.". Shuru ya ratsa na second biyu, ta daure tace "Baka tambayi mai jiki ba." Yace." Ai nayi ta kiran wayar Hamra'un bata dauka ba." Murmushin