← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 97

Sashe 8

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

fadin." Alba ka ajiye wannan maganin ka matsa min lemon tsami guda shida." Da sauri yace." An gama ranka ya dade. Ya dan sauke numfashi tare da sake rintse idonsa shi kadai yasan irin ciwon da marar shi ke masa. Alba ya k'araso gurin cike da bin umarni yace." Allah yaja zamaninka ga abinda ka bukata. Ba tare da ya bude ido ba yace." Nagode Alba kuna iya tafiya Allah ya bada sa'a." Suka amsa da ameen kafin su bar gurin sai da sukayi yi masa kirari kamar yanda suka saba. Kimanin minti biyar da tafiyarsu ya tashi da kyar, ya jima yana yamutse-yamutse kafin ya dauki matsatstsan lemon tsamin ya shanye tas, ya ajiye ya koma ya kwanta, yana danne saman cikinsa. Tayi mamaki da gari ya waye be zo ya dubata kamar koda yaushe ba, kawai tashi tayi a bacci ta samu ruwa cikin kwarya da asuwaki sai manya manya ayaba da mangwaro a gabanta. Ta wanke bakinta da fuskarta, dama can ibadah bata dameta ba domin data dameta da duk yanda za tayi sai tayi ta gabatar da sallolin da suke kanta. Yunwar da takeji bata tsammanin Ayaba da mangwaro zasu kawar da ita, taja tsaki tana harare-harare a gurin da babu motsin kowa sai ikon Allah. Jikinta ta duba tayi fututu! fatar jikinta duk ta bushe tayi datti! ta dubi qunar da duk ta bushe tana mata kaikayi, ruwan hawaye ta goge tana tunanin jin dadi da irin rayuwar da take ciki amma lokaci kankanki rayuwa ta juya mata baya. Kullum idan za ta kirashi da *'Barawo* zai kalubanceta kan cewa shi ba *'Barawo!* bane to idan ba haka ba waye silar zuwanta wannan kasurgumin dajin."? Ta girgiza kai cikin qunar zuciya ta kudiri aniyar irin rashin mutuncin da za tayi mata huce takaicinta. Ayaban kadai ta iya ci ta dauki kwaryar ruwan ta shiga tsakanin bishiyu kayanta jikinta ta cire tas ta wanke jikinta, gurin wankan ta jike rigar data zame mata garkuwa, bata damu ba kawai tasa breziyya ta mayar da wandonta ta fito a haka, taja ta tsaya tana dube-dube a gurin. Babu motsin mutum sai kukan tsintsaye da alama yau ma sun fita sun barta a dajin ita kad'ai. Ajiyar zuciya mai zafi ta sauke taja tsumman zanin ta dan daure tsakain cinyoyinta kafin ta nemi saman wani kuttuturun icce ta zauna tana tunanin halin da iyayenta ke ciki na rashinta, ta san mahaifinta sai yafi kowa shiga tashin hankali rashinta a kusa dashi. Ya kai minti arba'in cikin halin ni 'yasu kafin Allah ya sassauta masa, ya mike zaune da kyar! duk da halin da yake ciki hankalinsa na kanta burinshi ya tashi yaje ya duba halin da take ciki. Ya mike babu kuzari a jikinsa, kai tsaye gurin da take ya nufa...................Rintse idonsa yayi da karfi yana Auziya a fili sakamakon ganin da yayi mata ita ba tsirara ba ita mai tufafi domin breziyar dake jikinta bata hanashi ganin kamai ba........"Subahanallah ! Ya jima a tsaye a gurun yana kiran sunan Allah! kafin yayi namijin kokarin bude idonsa yayi ya'ki da shaid'an da kuma zuciyarsa ya durfafeta babu alamun wasa a tare dashi............ *Don Allah idan ba sayan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana abubuwan da yawa Nagode *Ga masu bukatar sadauki Omar 1k za'a tura domin samun damar karantawa littafin tare da Goje! sadauki Omar return* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* katin mov ko airtal. 1/12/22, 20:33 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________
Chapter 8 · 0% Book details