← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 90 OF 97

Sashe 90

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

takaici tayi kafin tace." To ta yaya zata daga wayarka bayan kana tsangwamarta ranar lahira za'a tuhumeka kada ka kira sunana dan wallahi ni ba zaka had'a baki dani ka cuci matarka ba." "Allahu akbar malama sai ki fada min cutar da nayi mata, wai shin mai yasa kike kokarin dora min laifi ne."? Shuru tayi masa takaicinsa duk ya isheta. Yace." Bani Uwale mu gaisa domin ina da Uzuri." Tace." Yawwa dama akwai maganar da zan fada maka." Yace." Wace magana ce."? Ta jima tana tunanin hanyar da zata bi gurin sheda masa halin da ake ciki, da kyar dai tayi shahada ta fara fada masa mawuyacin halin da suka iske mahaifiyar matar tasa a ciki da irin taimakon da tayi mata. Ya gama saurara tsaf har ta kammala, ya ja dogon tsaki da fadin." Wanene ya saki aikata hakan."? Tace." Babu kowa tausayi ta bani wallahi har sai dana zubar mata da hawaye. Yace." Zakiyi wani kukan domin wannan da ki kayi shafar mai ne, abinda nakeso dake yanzu shine maza ku dauko matar nan daga asibiti domin lalurar dake damunta bana asibiti bane. Shuru tai masa domin bata tsammanin aikata abinda ya umarce ta. Yace." Ko ba kiji abinda nace ba."? Jiki a sanyaye tace." Naji.'' Ya kashe wayarsa ransa duk a 'bace! ya tsani kankanba! a lokacin da take shaida masa abinda ta aikata yaji a jikinsa cewa akwai abinda zai faru, aikuwa a daran jikin Dayyiba ya rikice wasu manya manya kuraje suka feso a jikinta! sunyi jawur! sun d'uri ruwa sai kaikaiyi suke mata tana zumduma ihu! Su kam likitocin babu wata damuwa a tare dasu suke gudanar da aikinsu, suka dinga zurkud'a mata karfe suna fashe k'urajen suna matse wani irin ruwa mai wari da kauri da jini babu kyawun gani. Al'amarin ya tsananta sosai gabadaya jikin Dayyiba ya baibaiye da Kuraje babu masaka tsinke, dan koda suka isa asibitin suka iske halin da ake ciki sai da hankalinsu ya tashi. Gaje na goge guntun hawayen fuskarta tace." Hajiya Zinatu kinga yanda abu ya dawo ko shiyasa nace wannan lalurar bana zuwa asibiti bane. Jiki a masifar sanyaye tace." Nima naga alamar hakan saboda haka bari na samu likita muyi magana idan da yuwuwa a bamu sallama muje gida. To shima likitan dai bai yi jayayya ba, domin ansha kawo masa marasa lafiya irin wannan, sukan yi iya bakin kokarinsu akai idan ya gagaresu kawai sallamar mutum suke tare da fadin aje a gwada na hausa. Amma bai basu sallama a ranar ba yace. sai zuwa gobe tukkuna. Aikuwa a daran rai yayi halinsa, Dayyiba ta amsa kiran ubangiji, INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Mutuwar tayi masifar girgizata ba kadan ba, ta dinga kiran sunan Allah a zucci a bayyane. Gari ya kacame! da surutu! kace nace! kowa da abinda yake fada cewa kishiyar Hamra'u ce sanadiyar mutuwar Dayyiba. Da yawa wasu sun yarda da hakan, amma wa'inda basu yarda ba sun fi rinyaje. Ita dai uwar dakin Uwale ta shiga ta kwanta tana kuka, dama sai da mijinta ya gargad'e ta amma taki jin maganarsa. Hawaye take sharewa tare da adduar Allah ya fitar da ita. Har akayi jana'izar Dayyiba tana kwance a daki domin fargaba take taje gidan mutuwar saboda tana gudun abinda zai biyo bayan zuwan nata. Koda ya samu labarin mutuwar matar bai damu ba, a ganinsa mutuwar itace tafi mata alkairi, koda taji sauki ta dawo gida wahala zata sha ayi ta fama da ita dan ba za su ta'ba fahimtar me ya janyo faruwar hakan ba sakamako dai ya bayyana a yanzu alamu sun nuna cewa ta shiga hurumin babban aljanin da baya son wargi. A daran ranar wani mugun zazzabi mai zafin gaske ya rufe ta, ta rufe jikinta a gado tana ta makyarkyata da faduwar gaba, ba komai ne ya janyo mata wannan zazzabin ba sai fargaba da tashin hankalin faruwar al'amarin da take ganin kamar itace silar faruwarsa. *Kada ki karanta min littafi idan baki biya, kada ki siya ki fita dashi, 'Yar uwa kada ki ganshi a group kiyi shearing domin hakkina ne, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne.....0542382124...Binta umar gtbank. idan kati zaki turo sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 5/5/22, 20:52 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *128* *(Rahma Idris) daughter (Zainab Khabir Ishak) da sauran magoya bayan wannan littafi na GOJE ina mai baku hakuri, hakikanin gaskiya na san dole ranku ya 'baci, na rashin samun Update kullum kamar yanda nayi alkawari, Kuyi hakuri nima ba sa'an raina ba, haka Allah ya tsara min ina cikin jarabawarsa a halin yanzu bani da nutsuwar typing, abubuwa da yawa sun dameni, wannan shine cikar mumuni, dole rayuwa ta tafi da jarabawa, muna rokon Allah ya jarabce mu da irin wacce za mu iya dauka *KUYI HAKURI KU SANYA NI CIKIN ADDUARKU Da zazzabi ta kwana ta tashi, jiki ram! duk ta fyade tayi wata irin rama ido yayi zuru-zuru! Uwale hankalinta ya tashi, ita ta dinga dawainiya da ita kafin Umar din ya sauka a garin. Ganin halin da take ciki ya sanya jikinsa sanyi, ya umarce da ta shirya maza suje asibiti likita ya dubata, kafin ya dawo daga gidan mutuwar, domin yana so su kama hanyar gida a ranar. Uwale tace." Daka bari ayi sadakar uku mana." Kansa kawai ya girgiza ya sanya takalmansa ya fita da sauri. Kai tsaye gidan mutuwar ya nufa. Duk da yana jin haushin mai mutuwar sai da ya tausayawa iyalinta. ya shiga har cikin gidan yayi musu gaisuwa, jama'a sukayi caa! a kansa, sai ya dinga jin kunya da nauyi abinda ya faru yasan da yawa daga ciki akwai abinda suke tunani a kansa da matarsa. Sai da ya fita daga gidan kana ya samu yaro ya umarceshi daya kira masa Hamra'un sosai yarinyar ta bashi tausayi . Ta fito ta sameshi yana waya. tsayuwa tayi jikin bango( garu) tana kallonsa itama duk ta rame abinka da mai k'aramin ciki fargaba da laulayi sun sanyata a gaba. Cikin kulawa ya kalleta da fadin." Ya karin hakuri."? Wasu hawaye masu zafi suka kwace mata. Ya girgiza kansa da fadin." Kiyi shuru ki daina kuka addua zaki cigaba dayi mata. Ta share hawayen fuskarta tana sauke ajiyar zuciya. Yace." Jikin naki da sauki ko."? Kanta kawai ta iya dagawa. Minti biyu yana kallonta kafin yace." 'Yar uwarki ma babu lafiya sakamakon abinda ya faru ina fata dai kinyi mata kyakykyawar fahimta akan lamarin. Taja hanci kanta a sunkuye tace." Wallahi bana zargin aunty Zinat domin da kyakykyawar niyya a zuciyarta, kawai dai lokacinta ne yayi, suma mutanan dake zarginta dan basu san wacece ita bane. Ya jima yana kallonta kafin yace." Naji dadin hakan sannan ina fatan suma sauran mutanan dake zarginta su gane gaskiya. Shuru tayi ba tace komai ba. Hannu yasa cikin aljihu ya dauko kudi da yawa ya bata da fadin ." Ayi sadaka insha Allah ranar adduar bakwai zan dawo sai mu tafi tare. Tace." Zaku tafi ne yau."? Kai ya daga yana duba agogon dake daure a hannunsa. Jikinta duk ya mutu jin cewar zasu tafi. Ya kalleta tare da d'an girgiza kansa hakurin dai ya sake bata kafin yayi mata sallama ya fice daga soran gidan. A tsaitsaye ya gaisa da Kawunansa kafin ya isa gidan ta shirya tsaf tana zaune gefan gado tare da kokon fura da nono a hannunta, tunda tayi wanka da ruwan dumi taji sassauci. Uwale dai cewa tayi sai ranar adduar bakwai idan yazo sai su tafi domin yanzu tana iya tafiya surutu ya biyo baya, abinka da kauye. Sai da sukaje asibiti aka dubata kafin su dauki hanyar gida, ita dashi babu mai magana, sai yaronsu dake wasa da gwalantu a kwance a bayan mota. Sai wajan biyar da rabi suka isa gidan. Da kanshi ya bude mata motar ta fito jikinta duk yayi tsami! kafafuwanta ma rawa suke da kyar take tafiya, ya bita da kallo kafin ya girgiza kai ya sunkuya ya dauko d'ansa yasa a kafada ya bi bayanta dashi. Zaune a gefan gado ya sameta ta hada ta gumi hawaye na zuba saman fuskarta. Ya dora mata yaron a jikinta dan kuka yake alamar yana bukatar nono. Nonon ta fito dashi tasa masa a baki ya kama yana tsotsa. Kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya ita dashi. Yace." Naga kin sanya damuwa a ranki har da ciwo hakan da kike zai janyo miki wata damuwar. domin ita wannan matar lokacinta ne yayi, nasan kuma kin san da cewa mutuwa dole ce, baki da laifi tunda ke taimako ki kayi, Allah kuma da zuciya yake hisabi. Taja hanci tana girgiza kanta tace." Wallahi nayi dana sanin zuwa garin nan, domin da nasan abinda zai faru da ban daga hankalina ba, ashe tsautsayi ne yake kira na." Yace." Babu wani tsautsayi ko kinje ko baki je ba lokacinta ne yayi zata mutu saboda haka ki cire wata fargaba daga ranki. Shuru tayi ba tace komai ba, Ganin haka yasa ya nufi toilet domin wanke jikinsa shi kansa da fargaba da damuwa ya wuni ga wata irin yunwa da take damunsa. Washe garin ranar da ta dawo Aunty Zeey tazo, sosai taji dadin zuwanta, suka dinga hira, har ta gaza boye mata abinda ke damunta ta sheda mata, ita kanta aunty Zeey din sai da jikinta
Chapter 90 · 0% Book details