← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 97

Sashe 64

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi sashen masu gidan, hakan baya rasa nasaba da mutsiyaciyar yarinyar data tsana a rayuwarta. Sabon wanka tayi....... sosai tai gayu tayi cikin kananun 'kaya masu daukar hankali, masifaffun turarukan da take d'aukar hankalinsa dasu tasa a kowane sassah na jikinta, kai tsaye sashen ta nufa zuciyarta cike da wasiwahsi! Idar da sallarsa kenan domin tun daga magaribar har isha'in a gida ya gabatar bai samu shiga massalaci ba dalilin matsanta masa da kafarsa tayi, koda yake yasha magani da sauki akan da. Kamar bata so tayi masa sallama, shima babu yabo babu fallasa ya amsa, yana bin ta da kallo har ta samu saman kujera ta zauna. Shuru tayi tana dan wasa da yatsun hannunta!.....shi kuma bai fasa kallonta ba, da carbi a hannunsa yana ja yana nazarinta. Ta d'ago kai suka had'a ido! bai janye idonsa ba bai kuma ce mata komai ba......Itace dai ta janye idonta sakamakon dafin idanuwansa dake kokarin kassara ta! Da 'kyar ta iya bude baki tace." Ashe ka dawo."? Uffan bece mata ba kawai dai ya zuba mata idonsa dasu yake hukuntata! Ta kalleshi a karo na biyu idonsu ya sake had'uwa.......Wani abu mai yuwar fassaruwa take hange a cikin kwayoyin idanuwansa, gabadaya jikinta ya mutu sai kawai hawaye ya kwace mata! suna zuba tana sa hannu tana sharewa tare da shak'ar hanci! tabbas da tana da iko da sai ta dawo da ciwon jikinta a ganinta ma kamar ta fishi damuwa! Gyaran murya yayi kafin yace." Me kuma nayi miki? zaki sanya ni a gaba kina kuka! ai ni zanyi kuka duba da ta'addancin da ki kayi min." Ta kalleshi hawaye share-share! "Nice 'yar ta'addah."? tafada tana nuna kirjinta. Kansa ya daga da fadin." Eh mana baki da imani! idan ba haka ba mai zai sanya ki farfasa min kwalabe a daki ai kinso ki cutar dani ne." Taja hanci tana goge ragowar hawayen daya rage tace." Okey kai yanzu a ganinka abunda ka aikata shine dai-dai."? Ya ajiye carbin dake hannunsa sosai ya mayar da hankalinsa kanta yace." Me nayi ? ina so kiyi min cikakken bayanin abinda nai miki ko'ina akaje baki da hujja! "Shikkenan tunda haka kace ni bazan yi wata magana da kai ba a yanzu amma ina mai tabbatar maka da cewa wallahi idan baka daina ba nima ba zan fasa ba."! Yace." Idan kuma ta hanyar halak nayi fa? shin ko zaki hana ni aikata sunnah da matata."? Shuru tayi tana kallonsa gabanta in banda faduwa babu abunda yake. Yace." Ki kiyaye domin kishin hauka babu inda zai kai ki, sai halaka hakan kuma da kike bashi zai ha nani abunda nayi niyya ba." Jikinta duk ya mutu da maganarsa, a sanyaye tace." Kayi hakuri." Wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa.......Lallai ya yarda da maganar Uwale da Asp in da suke cewa cikin laluma ake nusar da mutum idan yana aikata kuskure......gashi kuwa yayi amfani da damar bukatarsa ta biya bai ta'ba tsammanin zata bashi hakuri ba, koda yake yabi hanyar da hakan zata kasance! Yace."Na yafe miki Allah yayi miki albarka." Ta amsa da "Ameen Nagode." D'akin yayi shuru na 'yan mintina kafin tace." Kaci abinci."? Yace." Eh naci gurinsu Uwale yanzu kwanciya kawai nake bukata." A hankali ta mike ta iske inda yake zaune.........Hijab din jikinta ta cire kafin ta zauna kusa dashi..........Kallonta kawai yake yana sha'kar kamshin jikinta da yake masifar so!! idonta kuri kan k'afarsa kafin ta kai hannu gurin ciwon! Da sauri ya janye yana ya mutse fuskarsa! Tace."Da zafi ko."? K'amar karamin yaro ya daga kansa! Sai kawai ta taya 'bera 'bari ta janyoshi jikinta kansa ta rungume a kirjinsa tana jijjigashi tare da shafa sumar kanshi kamar k'aramin yaro! Tabbb! ai neman ciwo yayi ya rasa irin wannan soyayya! haka mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki! mutumin da ake rarrashi! domin yayi bacci sai kawai ya 'buge da kusurkusur yana motsi tamkar yaron dake tsananin bukatar nono! haka ya dinga cusa fuskarsa a kirjinta da wayo da dubara ya 'balle bireziyar ya sa'bule! 'karamar rigar dake jikinta........Daga nan labari ya sauya. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/3/22, 22:36 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 4k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *91&92* Wannan ciwon jikin da ya fita dashi ashe sa hannun zazzabi ne. domin koda ya zauna a ofis din kasa katabus! yayi kawai sai ya koma kan doguwar kujera ya kwanta zazzabin na sake k'arfi a jikinsa wani irin bacci mara dadi yana fizgarsa. Shigowar Asp ofis din ne ya zaburar dashi! ya bude jajayen idanuwansa yana kallonsa har ya k'araso gurinsa da wasu takardu a hannunsa. Ganinshi wani iri ya sanyayar masa da jiki da ya shigo da 'kwarin gwiwa sakamakon samun rahoton mutumin da suke ta nema ruwa a jallo. Gefansa ya zauna da fadin." Jarumi wai shin me yake damunka ne tuntuni nake kiran wayarka babu amsa wannan dalilin ya sanya kawai na yanke shawarar zuwa ofis din naka. Ya mike zaune da 'kyar! yana ya mutse fuskarsa yace." Bana jin dadin jikina wallahi zazzabi da ciwon jiki ke damuna." Maganar yake amma shi Asp din hankalinsa yana kan k'afarsa dake kumbure! Cike da al-ajabi yace." Rauni kaji ne babu labari."? Mirmushi takaici yayi yana danne b'acin ran dake taso masa yace.'' Jiya bayan rabuwarmu ina shiga gidan.......duk ya kwashe komai ya fada masa. Ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin yace." Yanzu Zinatu da hankalinta ta aikata wannan d'anyan hukunci. koda yake ko shakka ba nayi da sanya hannun Zainab domin yini sukayi a tare wa yasan irin abunda suka shirya. Ya girgixa kansa da fadin." Kada ka zargi kowa domin yarinyar abunda yafi haka ma zata aikata, na shiga dakina na samu ta tarwatsa min ko'ina wannan shine dalilin da ya sanya na samu rauni a kafata. Yace." To wai shin ma me ya had'a ku ne har hakan ta faru."? Tsaki yaja kafin yace." Bak'in kishi ne da jahilcin dake damunta, tana zargi na dan haka zuciyarta take raya mata, amma ni nasan abunda na aikata ba haram bane domin da niyyar taimako nayi kuma ko'ina hakan na iya faruwa ballanatana a cikin gidana, Asp mutukar naga abunda zai cutar da wani musulmi dan uwana mace ko namiji sai inda karfi na ya kare." Yace." Maganar kake a du'kun'kune ka fayyace min makasudin abunda ya janyo matsalar." Kallonsa yayi na second biyu kafin ya fara warware masa abunda ya faru. Yace." Gaskiya ne baka aikata haramci ba kamar yanda take zarginka, kayi hakan ne da niyyar taimako amma kasan mata idonsa yakan rufe akan kishi basa tunani akan kowa sai a kansu amma meye laifinka dan ka dauki Hamra'u kasa a mota shin so take ka bari ta mutu ko yaya."? Yace." Nima dai haka na gani meye laifina anan? wallahi banyi hakan da wata manufa ba sai da niyyar taimakon musulunci." Yace." Umaru wallahi kwata-kwata bana k'aunar alakar Zainab da Zinatu domin dukkaninsu basu da kirki! maganar dai guda daya ce akwai sanya hannun Zeey dangane da faruwar hakan kuma zanje gidan na sameta." Yace." Aa kada ka yanke hukunci cikin fushi! na fada maka fa cewa.......Koda babu Zainab a cikin rayuwar *ZINA* to zata iya aikata abunda yafi haka wannan shine dalilin da yasa tun kafin muyi aure nake da shakku akanta saboda gudun faruwar matsala irin wannan......Ban auri Hamra'u ba haka tana faruwa to inaga kuma na aure ta."? Yace." Kai dai zaka zage damtse ka tsaya a matsayinka na namiji ka nuna mata bambanci sosai amma naga duk ka wani susuce! wai shin ko tsoronta kakeji ne."? Murmushin takaici yayi kafin yace." Asp mu rufe maganar nan dan Allah! muyi abunda zai yuwu domin ina so na tafi gida na kwanta na huta." Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace." Ai shikkenan tunda ka fadi haka amma ni kam dole na tauna tsakuwa domin aya taji tsoro." Shuru kawai yayi masa yana jin wani irin takaici a ransa.........Wai yana tsoron yarinyar, wannan maganar ta sosa masa rai mutu'ka! shin akwai wata mace da zai ji tsoro a fadin duniya, Uwarsa ce kuma bata raye. Takardun dake hannunsa yake bud'ewa, wata doguwar takarda ya fito da ita da hoto kati daya, mika masa yayi kafin yace." Ka duba hoton sosai ka kuma duba rahoton dake jikin takardar. Saman takardar kawai ya duba yaga an sanya *AMINIYA GIDAN JARIDA KANO STATE* Ya kalleshi da fadin." Wani abu ne yake faruwa a jahar *KANO."?* Yace." Duba dai amma ka fara nazarin hoton mutumin dake hannunka." Ya 'kurawa hoton ido yana ta so ya hasaso kowaye.....ya girgiza kansa da fadin." Bangane waye ba wallahi." Asp din ya kar'bi hoton da fadin........ *UBAN DABA NE."!* A zabure! ya kar'bi hoton yana sake dubawa, kafin kice kwabo gumi ya fara tsatstsafowa a saman goshinsa. Tabbas idan ba wanda yayi masa farin sani ba ba zai ganeshi ba domin duk kammaninsa sun sauya......duk babu wannan 'kasumbar! yana sanye da kayan hausawa riga da wando harda hula sai dai jikinsa lullube yake da wani farin mayafi irin na maza wannan shi ya hana bayyanar nakasar dake tare dashi .........Tabbas shine domin k'wayar idonsa basu sanja ba suna nan yanda suke
Chapter 64 · 0% Book details