← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 97

Sashe 73

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wata rayuwar ba, duba da irin siradin data tsallake, a mai da gudawa ba karamin cuta bane, yanzu ma gabad'aya bata jin dadin jikinta, duk yayi laushi akwai bukatar karin ruwa a tare da ita. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta fara kokarin sauka daga gadon, kira ya shigo wayarta dake saman gadon, ta dauka tana dubawa, a kalla ya kira yafi sau ashirin tana bacci, tausayinsa ya rufe ta, tasan yana can a dame kamar yanda take a takure! ko kuma jikinsa ne yake fada masa cewa akwai matsala. Ta daga wayar cike da so taji muryarsa, network yayi tsiya dan sai magana take masa amma shi ba yaji.....Ta kashe wayar ta sake kira anan ma ba babu biyan bukata, kamar zata fashe da kuka ta ajiye wayar takaici duk ya isheta. Uwale ta shigo dakin, ganinta a zaune yasa ta sauke ajiyar zuciya tace." Kin tashi ko ya jikin naki."? Tayi kokarin danne damuwarta ta amsa da fadin." Naji sauki sosai na gode." Tace." Haba ai babu godiya a tsakaninmu Gimbiya Allah dai ya kiyaye gaba." Ta amsa da "Ameen ya Allah." A sanyaye tace." Amma don Allah ina neman alfarma a gurin ki." Cike da mamaki take kallon matar wace irin alfarma ce."? Tace."Don Allah kada ki fad'awa mijinki abunda ya faru kinji ko."? Murmushi kawai tayi kafin tace." Insha Allah kada ki damu ba zan fad'a masa ba." Tace." To na gode sosai.'' Har ta juya zata fita daga dakin ta dakatar da ita....."Ina bukatar nayi wanka jikina bana jin dadinsa." Tace." Ai dole! amma kiyi hakuri ayi sallah tukkuna bari na dora miki ruwan zafi sai ki gasa jikinki." Tace." To shikkenan hakan yayi." Uwale ta fita daga dakin tana godiya ga Allah ganin yanda ya gajarta musu wahala. Cikin ikon Allah ta na yin wanka jikinta ya warware ta zauna taci abinci zuciyarta fes domin ba tayi tunanin cewa wai abincin da taci dazu ne ya janyo mata matsala ba, itama tafi tunanin cewa ko sauyin yanayin gari da sauransu. Ta kalli Uwale da fadin." Ina so nayi waya amma gidan nan bashi da network yana bada matsala." Tace." To yanzu ya za'ayi kin ga yanayin gidajen namu ginin da ne babu tsayin katanga a daki ga zurfi. Tace." Zan fita waje ko Allah zai sa a dace." Tace." To shikkenan babu damuwa. Can wani fili ta nufa, duk da dare ne hakan bai hana gane ta ba, ido yayi caaa! a kanta, yara da manya masu wuce wa. Ita dai bata damu ba bukatar ta, ta samu wayar masoyinta. Bugu daya ta shiga ya daga, abun mamaki tar taji muryarsa babu gargada. Ajiyar zuciya mai sanyi ta sauke kafin tace " Darling ya kake? ina fatan kana cikin koshin lafiya." Yace." Kin san hakan ba zata samu ba, ZINAT me yasa baki d'aga wayata akan lokaci ba." Tace." Ba laifi na bane network ne babu a garin, nima na damu da kai sosai wannan dalilin yasa na fito waje wani fili duk dan naji muryarka." Yace." Yanzu kina nufin ba'a cikin gida kike ba."? Tace." Eh ai cikin gidan na fad'a maka babu network mai kyau. Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ki koma gida bana san tsayuwar ki a gurin nan." Tace." Haba babu fa abunda zai faru duk ga jama'a nan suna kai kawo a gurin." Ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin wani abu a ransa, jiya kwana yayi yana munanan mafarkai a kanta, amma yasan babu wani mahalukin da ya isa ya cutar da ita face Allah ya mayar masa da sharrin kansa. Hamra'u da k'awarta Zabbah suka hangota a tsaye da waya a kunne. Hamra'u tace." Zabbah ga mutsiyaciyar can." Zabbah ta kalli gurin da fadin." To me ya fito da ita a wannan daran ita ba 'yar gari ba." Tace." Waya ta take na san kuma da masoyina take, yau sai naci mutuncinta in yaso duk abinda zai faru ya faru." Zabbah ta rike hannunta da fadin." Hamra'u kada fa ki aikata abunda zai janyo miki matsala ki bi komai a sannu a hankali." Ta fizge hannunta da fadin." Zabbah ni kad'ai na san irin b'akin cikin da wannan matar ta k'unsa min, ai magana ta 'kare tunda manya sun shiga maganar har an tsayar da ranar daurin aure." Hannunta ta fizge ta durfafi gurin da Gimbiyar take tsaye....Zabbah ta rufa mata baya. Tace." Darling zan shiga na kwanta sai da safe." Daga d'aya b'angaran yace." Okey Allah ya tashe mu lafiya amma ki mika min gaisuwa gurin babyna kafin mu had'u." Tana murmushi tace." Zai ji da kyau! amma shima yayi kewarka sosai. Yace." Haka nake so ai duk sanda muka had'u zamu gaisa sosai ki bashi hakuri." Cikin shagwaba tace." 'Daya babyn naka ma yana bukatarka fa." Ya lumshe ido tsigar jikinsa na tashi! ya gane abinda take nufi shiyasa gabadaya kasala ta rufeshi yana bala'in son yanayin shagwabarta. Yace." Wannan babyn yayi min laifi ki sheda masa cewa idan muka had'u zan hukuntashi da kyau."! Ta fashe da dariya da fadin." Ba ruwana amma na yarda duk sanda kuka ka had'u kayi masa hukuncin da ya dace." Yana sake release a kujera yace." Zan kuwa cire masa kai shine hukuncin da zanyi." Maganar ta bata kunya sosai tana 'yar dariya tace." Ni dai sai da safe." Yace." Dole ki gudu mana kin san halin da ki ka jefa ni ciki kuwa."? A sanyaye tace." Kayi hakuri gobe ka dauki azimi." Yace." Azimin dole kada kiyi tsammanin gani na gobe kuma idan nazo komai rigimarki tare zamu tafi." Tace." Ai gobe ne bikin idan kazo sai mu tafi shikkenan." Yace."Okey Allah ya kaimu amma mybe shigowar dare zanyi. Tace." To idan hakane kawai ka bari sai jibi da wuri sai ka shig.......maganar ta katse sakamakon zuwansu Hamra'u gurun. Ta kashe wayar tana kallonsu. A wulakance tace." Munafukar Allah ta ala to duk asirin da kuke Allah ya karya alkadarinki, ina so ki san cewa baki isa ki hana abinda Allah ya hukunta ba." Cike da mamakin maganarta tace." Ke wannan wace irin magana ce."? Da yatsa ta nuna ta kamar zata tsone mata ido tace." Hamra'u ta UMARU ce shekara da shekaru ina nufin ke baki isa ki shiga tsakanin masoya ba." Sai abun ya bata dariya amma ba tayi ba ta dake ta sha kunu da fadin." Kin san ni nafi karfin kiyi min rashin kunya ko."? Aikuwa sai ta fusata! ta sake nuna ta da hannu da fadin." Ke asuwa kuma? ko kin dauka kina da mutunci a garin nan, to bari kiji dake da kare! baku da maraba domin bama 'kaunarki, kuma ki kwana da shirin wata shida kacal ya rage a daura min aure da mijinki sai kiyi duk abinda za kiyi." Ranta ya 'baci sosai da irin fitsarar da yarinyar take mata, kawai sai ta girgiza kai ta kama hanya domin barin gurun.......Tace." Matar cushe bata daraja."!! A fusace! ta juyo ta wanke fuskarta da mari wanda sanya ta ganin gilmawar taurari! ta dafe gurin cikin kad'uwa da mamaki take kallonta. Ta nuna ta da hannu tana so tayi magana, amma tsabar b'acin rai ya ha nata furta komai, kawai ta girgiza kai a gaggauce ta bar gurin, zuciyarta kamar ta fashe saboda tsananin bacin rai! Zabbah ta kalleta da fadin." Ko babu komai kin sha mari! wallahi Hamra'u baki da wayo har yanzu." Ido jawur! take kallonta kafin tace." Kin san Allah Zabbah! sai na rama mari na don kutumar ubanta tazo cikin garinmu ta mare ni, wallahi ba zan yarda ba." Fizge hannunta tayi ta nufi cikin gidan. Zabbah ta bita da kallon takaici tana girgiza kai kwata-kwata Hamra'u bata da wayo wallahi, kishi hauka take, ai idan itace ba zata fito da kishinta a fili kowa ya fahimta ba, amma ita duk inda ta zauna maganar kenan, tayi ta zagin Gimbiyar Kai tsaye da ta shiga gidan kanta ta nufa gadan-gadan! mari ta kai mata, tayi saurin kaucewa ta mari iska!! ta tsaya tana numfarfashi idonta cike da ruwan hawaye take fadin." Wallahi baki isa ki mare ni na kyale ki ba, sai na rama." Ta sake mika hannu da niyyar marin ta, kafin tayi aune! taji saukar wani lafiyayyan marin a fuskarta! Uwale hankali a tashe! ta shiga tsakaninsu tana tambayar ba'asi. Gimbiyar ranta a 'bace tayi mata bayanin duk abinda yake faruwa. Uwale ta kalli Hamra'u da fuskar bacin rai tace." Amma wallahi kinji kunya Hamra'u kin 'bata wayonki ban ta'ba tunanin haka zuciyarki take ba sai yau." Sai kawai ta fashe da kuka takaici biyu ya dameta, na farko tasha marika masu zafi daga gurin Gimbiyar, gashi bata samu sararin ramawa ba ana fada mata bakar magana, dama ba tun yau ba ta gane cewa Uwalen tafi kaunar Gimbiyar a kanta. Bakin ciki da takaici ya ha nata magana kawai ta kada kanta ta kama hanyar fita tana share hawaye. Zabbah dake tsaye a tsakar gida tabi bayanta tana rarrashinta.....''Yanzu idan Umar din yaji abinda ki kayi wa matarsa kina tsammanin zai kalleki da mutunci? Hamra'u shifa yaki dan zamba ne me yasa zaki 'bata rawar ki da tsalle." Ta daga mata hannu da fadin." Kin ga Zabbah na gaji da jin wannan maganar taki, domin ta kunan hagu take fita, kin san Allah sai na saubata matar nan! sai ta gwammace kida da karatu." Zabbah tace." Yawwa to dama tuntuni ta wannan hanyar ki ka biyo yafi sauki idan kin bi ta karkashin kasa babu wanda zai fahimce ki, amma kin zauna kina hauka haba Hamra'u! Mugun tsaki taja mai tsayi fuuuuuuu! ta shiga gidansu ba tare da tayi mata sallama ba, girgiza kanta tayi itama ta kama hanyar gidansu cike da mamakin al'amarin. Malam Shafi'i yana dawowa Dayyiba ta shirya masa karya da gaskiya cewa yana da kyau yaje har gidan Uwalen ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro domin ba zai yuwu ace 'yar uwar tasa tana fifita wata a kan jininsa ba. Aikuwa ya dauki zugar matarsa domin ransa ya baci da jin abinda 'yar uwarshi ciki daya tayi wato tana fifita wata a kan 'yarsa Har gida yaje ya sameta ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, sai kumfar baki yake yana sakin kausasan maganganu wanda duk wani
Chapter 73 · 0% Book details