← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 97

Sashe 46

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

mata komai ba ya sauka wandonshi yasa ya suturta kanshi kafin ya kunna fitilar dake gefen gadon, dakin ya gauraye da haske..........Idonta a rufe taga alamun haske da sauri ta bude ido ta ganshi ya tsirawa jikinta ido yana kallo........Kamar ta zabga ihu! ta fara jan bed shirt domin rufe jikinta, ya rike bedshirt din still idonsa 'kuri a kanta yarinyar nada dadi abinda yake aiyanawa kenan a ranshi. Alkyabbar ta dake yashe a k'asan gadon tayi saurin d'aukowa ta rufe jikinta ranta gabad'aya ya gama b'aci! da abunda yake, a ganinta wannan wulakanci ne kawai zai kunna fitila domin ya kalli tsaraincinta, tun dai bukatarsa ta biya shikkenan....* Uwar iya kenan!* duk hararar da take zabga masa bai sa ya janye idonsa ba sai da ya ga dama tukkuna ya sauke ajiyar zuciya mai zafin kafin ya yunkura ya tashi ya kama hanyar toilet domin tsabtacce jikinsa. Kallo ta bishi dashi tana ayyana abubuwa da yawa a kanshi, ta kowane bangare ya cika cif! yana kuma sawu na farko a cikin mazan da kowacce mace zata bukata ace mijinta ne, abunda yayi mata a yanzu shiyasa ta gazgata hakan, sakayau! take jin mararta babu wani damuwa, duk tarin sha'awar da take damunta lokaci gudu yay mata magani ta hanyar romancing kad'ai! tana bala'in san irin wannan soyayyar shiyasa ta gaza ha na shi aikatawa, a ganinta hakan ba zai shafi rashin jituwarsu ba, mutukar zai dinga bata kulawa irin wannan zata amince amma ba zata yarda da ya rabata da budurcinta ba, sai ya furta mata kalmar so da bakinsa ta tabbatar da gaskiyar maganarsa, zata iya zama dashi saboda wannan dalilin. Ya fito ya sameta tana ta sa'kawa da kwancewa, ya kalleta da fadin."Ina fatan dai Kin iya wankan tsarki ko."? Cike da mamaki ta kalleshi wace irin magana ce wannan......Cikin gatse tace "Ban iya ba."! Ya girgiza kanshi da fadin." Ban yi mamaki ba." ya fada tare da kokarin barin gurin. Kallon takaici take masa tana mamakin rainin hankalinsa, ko ya d'auka ita din jahila ce." Tsaki mai tsayi taja tana hararar bayanshi lokacin da y ake kokarin sanya jallabiya. Sarai yaji lokacin da take tsakin amma bece mata komai ba ya lura kamar hakan dabi'arta ce. *(Yawan Tsaki ba abun arziki bane ballanatana ga miji, mata don Allah mu kiyaye kada mu bari bakinmu ya saba da jan tsaki)* Cigaba yayi da shirya jikinsa yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin sauya mata munanan d'abi'u Zanin les d'inta ta d'aura ta yafa dankwalin a jikinta ta nufi toilet tana jin wani irin bacin rai da damuwa a cikin ranta, abinda ya faru a tsakaninsu duk ya dameta. Toilet din ya bita lokacin tana tsugune da ruwa a gabanta amma bata fara wankan ba. Tsayuwarsa ya gyara har da rungume hannu a kirji ya zuba mata ido so yake ya gani shin ta iya wankan tsarkin ko bata iya ba. Daburcewa tayi ta dan harareshi da gefen ido da fadin." Wai meye haka zaka sani a gaba kana kallona ko kuma abunda kayi ne be isheka ba."? Be tanka mata ba har yanzu idonshi na kanta kuma bashi da niyyar fita. Ta sauke ajiyar zuciya tsaki take so tayi amma tana jin tsoron abinda zai biyo ba, haka nan ba yanda za tayi ta fara watsa ruwa a jikinta kafin ta dauki soso da sabulu. Ganinshi tayi a gabanta. Ta kalleshi kamar ta kurma ihu!! shin wai wane irin takurawa ne wannan. Ruwan dake gabanta ya zubar ya had'a wani duk tana kallonshi, ya 'bata rai da fadin." Ba kiyi dai-dai ba bari na nuna miki." Taji kamar ta gallawa fuskarsa mari! saboda takaici, da 'kyar tace." To dama wa aka haifa da iyawa kowa a duniya ya ko ya." Yace." Kada kiyi min rashin kunya ranki zai 'baci yanzu." Ta kalleshi taga yanda ya 'bata rai! dauke kanta tayi zuciyarta cike da takaici Rigar jikinsa ya cire amma ya bar gajeran wando ya tsuguna kusa da ita da fadin." Kalle ni nan." Saboda babu yanda za tayi yasa ta juya tana kallonshi.........Yace.'' Da farko za kiyi niyyar irin wankan da za kiyi a zucci ko a fili kafin ki ta'ba ruwa, ina so kiyi min niyyar wankan janaba da bakinki." Ta zumbura baki da fadin." Wani abu mukayi gagarimi! wanda lallai sai nayi wankan tsarki."? Ya kalleta da mamaki a tare dashi yace." Okey kin raina abinda ya shiga tsakaninmu kenan."? Shuru tayi tana dauke kanta. Ya girgiza kai da fadin." Akwai karanci ilimin addini a tare dake wankan janaba ya wajaba a kanki dalilin ruwan da kika fitar, ko zakiyi min musu baki fitar da komai ba." Shuru tai ba tace komai ba. Yace." Kinji dad'i har wani ruwa na mussaman ya fita daga jikinki a lokacin nutsuwarki ta dawo daidai wannan shine dalilin da janyo miki wanka domin tsarkake jikinki wajibi ne wannan, maziyi kadai zaki fitar ki wanke abinki kana ki cigaba da ibada da wannan kawai addini ya yarda." Jikinta yay sanyi domin ita tayi tunanin tunda romancing kawai sukayi ba za tayi wankan tsarki ba sai da soso da sabulu............*(Hakan yana faruwa ga ma'aurata masu 'karanci ilmin addini za suyi wassani a tsakaninsu har su gamsuwa amma kuma ba za suyi wankan tsarki ba saboda suna tunanin kamar janaba bata hau kansu ba, wannan ba dai-dai bane mutukar wani abu ya fita kuma an ji dadi an samu gamsuwa to janaba ta wajaba dole idan ana so ibadah ta cika sai an wanke wannan janabar.* *_(Nawaitu gusulul janabati-far'kul hadasul akbari-Wal-asgari_*) Za'a karanta sai uku kafin ta'ba ruwa alwala za'a fara d'aurawa a jika kai jagab da ruwa sai an tabbatar ruwan ya ratsa ko'ina sannan sai a tashi tsaye a fara wanke b'angaran dama a zuba ruwan a ko'ina kafin a tafi b'angaran hagu nan ma haka za'ayi sai an tabbatar da cewa ko'ina ya wanku sannan. Da kanshi yay mata wankan tsaf! besa wani abu a ransa ba ballanatana hankalinsa ya tashi! ita kuwa sai no'kewa take tana jin wani iri da nauyin sa, kawai dan yafi karfinta ne. Tsaf ya kammala ya cire towel ya mika mata, da sauri ta kar'ba ta daura.......Karami ya dauko ya daura mata a saman gashinta da yake ta digar da ruwa. ba tace komai ba ta kama hanyar fita, jikinta duk sanyaye........Zanin les din da dankwalin ya d'auka yabi bayanta dasu a hannunsa.... *SAI ALLAH YA KAI MU MONDAY DA IKONSA *AYI HUTUN K'ARSHEN MAKO LAFIYA* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/14/22, 11:55 - Binta: *67&68* D'aya daga cikin dogwayen rigunanshi ya dauko mata sabuwa ya mika mata da fadin." Kisa a jikinki kafin gari ya waye ko." Kallonshi tayi da fadin." To ka bude min kofa kawai na tafi guri na meye amfanin kwana na a dakinka." ? Da mamaki a tare dashi yace." Kece kike ganin kamar kwanan ki anan bashi da amfani amma ni ina mai tabbatar miki da cewar kwananki a dakina zai janyo miki samun lada a gurin Allah, wannan shine abinda nake miki sha'awa. Shuru tayi tana auna maganarsa, yanda ta fahimta kamar yana so suyi zaman lafiya ga yanayin yanda yake kawo mata 'kauli da ba'adi Allah yace Annabi yace ba da son ranta ba ta kar'bi rigar ta ajiye a gefanta, shi kuma bed din ya hau yana gyara bedshirt din daya cukurkude. Breziyyar ta dake saman gadon ya mika mata, tayi saurin kar'ba tare da dauke kanta. Bacci ne a idonsa saboda haka yana gama gyara shimfidar gadon ya kwanta tare da rufe jikinsa da bargo, rufe idonsa yay yana addua a cikin zuciyarsa. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke, jiki babu kuzari ta dauki rigar tasa a jikinta ba tare da ta mayar da breziyyar ba pant d'inta dama yana toilet anan ta cire ta ajiye saboda ya riga ya b'aci dole sai an wanke. Can nesa dashi ta kwanta da yake blanket din mai girma ne ya ishe su rufa ba tare da wani ya takurawa dan uwansa ba. Ya bude idonsa ya hangeta a can nesa dashi ta juya masa baya bece mata komai ba ya mayar da idonsa ya rufe yana sauke ajiyar zuciya...........Ya riga ta bacci saboda yanayin gajiyar dake tattare dashi, ta dinga jin saukar numfashisa cikin nutsuwa hakan ya sake tabbatar mata da cewa bacci mai nauyi ya daukeshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta gyara kwanciyarta idonta ta rufe tana addua a cikin zuciyarta cikin ikon Allah itama baccin ya d'auketa. Da asubah shi ya tashe ta bayan ya shirya zuwa massalaci, sai da ya tabbatar ta tashi tukkuna ya fita. Tana idar da sallah, ta nemi kayanta ta mayar jikinta, ba ta jirayi dawowarsa ba ta kama hanyar sashenta. Su Kawu Ado A massalacin suka same shi saboda haka ana idar da sallah, gabadaya sai suka nufi gidan a tare kowanne cikin walwala da farin ciki, kai tsaye sashen Uwale suka nufa domin gaisawa a tsanake. Sai da yayi musabaha da kowannesu ya dinga tambayarsu iyalinsu da sauran 'yan uwa da basu samu damar zuwa ba, Kawu Ado yace." Kowa lafiya lau UMARU suna maka fatan alkari. Cike da jin dadi yace." Nagode sosai Kawu amma zaku dan kwana biyu kafin ku tafi ko." Yace." Aa yau zamu tafi saboda dukkaninmu muna da ayyuka, muna jiran rana ta fito tukkuna." Yace." To babu laifi Kawu hakan yayi, Nagode kwarai da wannan karamacin." Yace." Babu komai Umaru amma ina da muhimiyyar maganar da nake so mu tattauna a tsakaninmu." Ba tare da ya Kawo komai a ranshi ba yace." To babu damuwa Kawu Allah yasa alkairi ne." Yana murmushi yace." Alkairi ne da ikon Allah." Uwale ce ta fara fitowa daga dakin kafin sauran matan su biyo bayanta............Ganinsa a zaune yasa farin ciki ya rufesu. Samun guri sukayi suka zazzauna kafin a fara gaishe-gaishe. Sosai yaji dadin ganin yan uwansa maza da mata ya dinga biyewa shirmansu yana dariya da yake a cikinsu akwai wanda wasa yake a tsakaninsu sai tsokanarsa suke yana biye musu suna dariya. Hamra'u ce ta shirya musu abun karyawa har kala biyu, tazo ta sheda musu cewa ta kammala.Kawu Ado ya dinga sanya mata albarka da irin dawaniyyar da
Chapter 46 · 0% Book details