Sashe 49
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dubata, ta shuka masa tsiya idan bata so ba, wani sa'in kuma a lalace zata amsa masa magana, kyaleta kawai yake ya nufi gurin Uwale a can yake zama yaci abinci suyi hira, wanda hakan yay bala'in farantawa Hamra'u rai, cikin zuciyarta ta dinga jin dadin yanda masoyin nata yake mu'amula da ita, a cikin kwanaki wata irin shakuwa sukayi, gabadaya ta siye zuciyarsa da kyawawan halayenta wanda suke mutukar burgeshi, a cikin ransa yake jin ina ma ace Gimbiyarsa ce take da wannan kyawawan halayen. Asp ya kira shi a waya da muryar bacin rai yace." Umaru me yake faruwa ne? yanzu mu kayi waya da mutuniyar a maimakon ta sheda min abunda ya had'a ku kawai sai ta fashe da kuka." Ranshi ya d'an 'baci, a zuciyarsa baya son yawan kiran da Asp din yake mata, ya danne 'bacin ransa da fadin." Ita ce ta kira ka ko kaina ka kira ta."? Yace." Itace ta kira ni, da kyar muka gaisa kafin ta fashe min da kuka." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Asp kuskure tayi na gyara mata shine take fushi dani tsayin kwana uku bata saurarata to akan me zan damu kaina a kanta." Yace." Idan ba damuwa ina so na san kuskuran ko akwai shawarar da zan iya bayarwa." *Ina jin dadin comments dinku *Sai dai ayi hakuri a kar'bi labarin a yanda yake, kada kuce lallai sai anyi muku yanda kuke so, labarin yana dauke da darrusa daban-daban, ku cigaba da bina sannu a hankali domin samun isar da sakon dana d'auko *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/17/22, 14:16 - Binta: *71&72* Ajiyar zuciya ya d'an sauke kafin yace." Laifi tayi min wanda ya cancanta da ko wane irin hukunci, to amma tunda ka bukaci sanin abinda ta aikata ba zan boye maka ba domin kai ma ka taya ni nuna mata kuskuranta." Cikin nutsuwa duk ya sheda masa abinda ta aikata bayan zuwan 'yan uwansa gidan. Girgiza kai kawai yake yana sauraranshi har ya gama yi masa bayani ya sauke ajiyar zuciya yana jimanta al'amarin, ko da yake ba abun mamaki bane yarinyar zata iya aikata abinda yafi haka amma shi bai ji dadin yanda abokin nasa ya fifita 'yan uwansa akanta ba, ita ta sheda masa cewa ya tozartata ya wulakantata a gabansu harda duka da mari wannan dalilin ne yasa hankalinsa ya tashi mutuka! bayan mijinta to shine mutum na biyu wanda aka bawa amanar ta, dole idan wani abu makamancin wannan ya faru yayi kokarin ganin an samu maslaha. Ya dan ja numfashi kafin." Yace." Gaskiya abinda ta aikata bata kyauta ba, domin ita gaskiya duk inda take dole a fada, abokina iyaye sun wuce wasa! dalili kenan da yasa kowane d'a nagari yake kokarin kare mutuncinsu, babu yanda za'ayi kana kallo wani ya ci zarafin iyayenka ka 'kyaleshi, ban ga laifinka ba, amma kuma kamar hukuncin da dauka bai kyautu ba Umaru kada ka manta cewa yarinyar nan amana ce a hannunmu bata da kowa a garin nan face kai da kuma 'yan uwanka, sai kuma ni da iyalina, Umaru duka babu shi a cikin sharadin aure don Allah ka kiyaye ka daina saurin hannu, domin hukuncin duka baya shirya mutum nasiha gami da nunawa mutum kuskuransa shine ke sanya mutum ya shiryu ya kuma gane hanya mai kyau." Murmushin takaici yayi kafin yay kokarin danne b'acin ran dake taso masa yace." Duk naji bayaninka Asp amma me yasa da farko ka nuna kamar ba kasan abinda yake faruwa ba."? Yace." Saboda kawai ina so naji bayani daga bakinka, tabbas abinda ta sheda min gaskiya ne tunda gashi baka 'karya ta ba, ka doke ta a gaban 'yan uwanka wannan ba dai-dai bane." Asp yana da 'kima da mutunci a idonsa, dalili kenan da ya sanya ya kasa d'aukar mataki akansa, amma da babu wannan darajar da tuni sunyi uwaka! ubanka! domin ganin kamar rainin hankalin yayi yawa. Yace." Asp ban doki yarinyar nan ba, ban kuma tozarta a gaban 'yan uwana ba, duk maganganun da ta fada maka akaina ta fadi ne domin ta kare kanta, kuma babu yanda za'ayi ta sheda maka laifinta, ni ne dai mugu! kullum kalmar da take kira na dashi kenan, to bani da damuwa da hakan, amma ina so ka san wani abu, kamar yanda yanzu ka gama magana cewa yarinyar amana ce a hannun mu to babu shakka ba zan zauna na zuba ido ina kallonta tana aikata kuskure na kyaleta ba, dole na nuna mata kuskuran abinda ta aikata kuma ba zan yarda da sakarci da rashin kunya ba." Cikin tsare gira yake maganar har ya gama Asp din na auna maganganunsa kafin yace." Gaskiya ne abokina amma kamar yanda na sheda maka cewa babu duka a sharadin aure to don Allah ka kiy...........Cikin fusata! ya katse shi ta hanyar fadin." Wai shin waye ya fad'a maka dukanta nayi ne? Asp ashe har yanzu ba kasan sharrin mace ba, ni Umaru na san abinda nake kuma ina da ilimin addini dai-dai gwargwado ban doke ta ba kamar yanda kake tsammani face na musulunci, amma kada ka sake yi min maganar duka domin na san abinda ya cancanta." Asp din yay murmushi ganin yanda abokin nasa ya fusata! sai numfarfashi yake masa a kunne! yace." Allah ya huci zuciyar *MAI DAWA."!* Ayi hakuri na fahimci maganarka naga ranka ya 'baci da wannan al'amari amma bari na bari ka sauka tukkuna sai mu karasa maganar." Yana fesar da wani irin huci! na tsantsar bacin rai da damuwa yace." Ranka ya dade wannan yarinyar bata isa ta shiga tsakanin abotarmu ba domin naga abinda yake shirin faruwa kenan to ba zan yarda da hakan ba tun kafin tafiya tayi nisa zan dauki mataki." Yace." A'a wannan gugar zana kawai kake min kace dai kawai na daina magana a cikin al'amarinka kuma zan kiyaye hakan da ikon Allah." Kashe wayarsa yayi ba tare da ya saurari da amsarsa ba. Wani 'baci rai mai tsanani ya sake rufeshi, wai yau shi Asp ya kashewa waya ta dalilin abinda bai taka kara ya karya ba, tunda suka hadu wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba, sai ta dalilin yarinyar, dama sai da ya tsammaci faruwar hakan, ya rasa mai yasa Asp din baya ganin laifinta, duk abunda zata aikata dai-dai ne a gurinsa, kullum shine mai laifi, ya kasa fahimtar abinda yake kudundune a cikin zuciyarsa abokin nasa, yana zargin kamar sonta yake to idan ba haka ba mai zai sanya ya damu da damuwarta haka? Ya jima da wannan tunanin a cikin ransa kawai yana kokarin kawar dashi ne saboda baya so zuciyarsa ta gazgata zargin da yake can cikin ransa. Kai tsaye sashensa ya nufa yaje ya samu hayakin Shisha ya banka, ya samu relief a zuciyarsa kafin yayi wanka ya fito har yanzu zuciyarsa babu dadi, saboda yanayin garin ana zafi yasa ya shirya cikin 3qutar da t-shirt mai gajeran hannu, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa, yanayin yanda yake taka 'kasa da karfi shi kadai ya isa ya sheda maka cewa shi din jarumi ne a gida da waje. Koda ya shiga sashen nata hadimta ya samu suna kai kawo Baraka na gyare-gyare yayin da Marakisiyya ke kokarin shiga kicin. Sallama yayi suka amsa kafin su tsuguna har kasa su gaishe shi, amsawa yayi bayan ya sassauta fuskarsa, sai da wuce tukkuna kowacce ta tashi domin cigaba da aikinta. Tana zaune a bakin gado da kayan bacci a jikinta, da alamu ba ta jima da tashi a bacci ba tun ba bayan sallar asubah da ta gabatar. Kallo d'aya tai masa gabanta ya fad'i! tai saurin dauketa kanta tana auziyya a cikin zuciyarta........Kayan dake sanye a jikinsa sunyi masa bala'in kyau! kwana biyu gani take yana wani irin kyau! shiyasa ba ta fiye kallonshi ba saboda kada tayi abun kunya. Shima nasa 'bangaran namijin kokari yayi gurin danne zulamarsa domin duk sanda zai tozali da wani bangare na jikinta muguwar sha'awa kan taso masa yanzu ma abunda yake shirin faruwa kenan, ya shiga dakin da karsashi da power! amma ganin ta a haka yana nema yasa ya rasa kuzarinsa. Ya iske inda take kawai yaja tunga ya tsaya a gabanta. K'amshin turaran dake jikinsa ya dinga fizgarta haka kawai taji kamshin ya kwanta mata a rai. Sun jima a haka babu wanda yayi magana, ita hankalinta yana kan wayarta tana tunane-tunane shi kuma ya zuba mata na mujiya yana mata wani irin kallon kurrula. Gabad'aya gabu'bin jikinta suka saki idanuwansa na da wani irin dafi, ko shima ya san da haka wannan shine ba ta sani ba. Shawarwari take da zuciyarta shin ta gaisheshi ko kuma ta tashi ta bashi guri. Tana so ta dauki nasihohin da Asp yake mata a koda yaushe amma tana wani tunani gani take kamar idan ta rusina masa ajin ta zai zube wannan shine abinda take gudu. Da k'yar ta iya bud'e baki tace." Ina kwana."? Bai tsammaci haka daga gare ta ba, dalilin da ya jefa shi mamaki kenan, a cikin kaso d'ari na damuwarsa kashi hamsin ya zube dalilin wannan gaisuwar. Bai amsa ba amma ya sassauta fuskarsa still idonsa na kanta kafin yace." Yanzu ki ka tashi kenan."? Shuru kawai tai masa domin a ganinta wannan ba hurumin sa bane. Ya duba agogon dake daure a hannunsa, 10:30 na safe ya kalleta da fadin." Goma da rabi a halin yanzu ina fatan kinyi sallah." Ba tace masa uffan ba, ta mike tsaye, ya bita da wani mayataccen kallo kayan baccin sunyi mata masifar kyau, lebansa ya dan ciza ya fesar da wani numfashi kafin yayi saurin tare mata hanya don ganin tana kokarin barin gurin. Karo na farko kenan da ta kalleshi. Yanayin kallon da yake mata da yanda k'wayoyin idanuwansa suka rusuna yasa jikinta mutuwa, ta dinga jin wata irin kasala na kokarin rufeta. Hanya take kokarin sanjawa ya sake tare ta, gabadaya ya zuba hannuwansa cikin aljihun 3qutar din dake jikinsa. Cikin bacin rai tace." Wai meye haka ka bani hanya na wuce." Ya girgiza kanshi ido a lumshe