← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 97

Sashe 36

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kafin yaja karamin tsaki yasa wayar gaban aljihun rigarsa ya mike da fadin." Kai matsala ta dakai shiririta haka kawai daga ganin matar mutane kace kana so Adewale kana da son mata wallahi." Yace."Ai sune jin dadin duniyar Oga hahahaha." Ya k'arashe maganar cikin dariya. Girgixa kai kawai yay yana kallonsa da tarin takaicin shirmen da yake yace." Ni zan shiga ciki na huta kafin magriba domin naga alamar yau shirmen naka yafi na kullum." Shima tashi yay da fadin." Nima ina da uzuri yanzu zanje na gabatar sai mun hadu da daddare." Hannu ya daga masa kawai, yana kallonsa yayin da yake kokarin barin gurin. Kansa kawai ya girgiza kafin shima ya bar gurin cike da so ya samu zama a nutse domin samun damar kallon hotonan amaryar tashi a tsanake. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/3/22, 15:49 - Buhainat: _Ina muku tallan group dina mai suna_ *MAR'ATUSSALIHA* *Wanda na bude shi wata shida da suka wuce a lokacin 1k ne kudin register, yanzu saboda yanayi na rayuwa yasa na mayar dashi #500 za kiyi register domin kasancewarki cikin group din, matan aure da zawarawan dake shirin aure da 'yan mata masu shirin aure ku nake da bukatar kuyi rigstar domin k'aruwarmu baki d'aya, akwai sirri da amana a tsakaninmu, duk wata matsalar dake damunki ki sameni ta pravite insha Allah zan baki shawarwari wanda zasu taimaka miki domin gyara kanki da zamantakewar auranki, 'yar uwa kiyi register da group din MAR'ATUSSALIHA Insha Allah zaki samu mafita.......ga duk wacce take da bukatar biyan kudin 0542382124....Binta umar gtbank sai ki tura kudin ta wannan account din ki tura min sheda ta wannan number... 07084653262* *53&54* Pictures din data tura masa a rashin sanin shi ta turawa, sun bambamta da wanda Asp din ya turo masa a yanzu, wanda ta tura masa a yanzu tayi ado sosai sa'banin wanda ta tura masa adon da tayi bai kai na yanzu ba, les din ne dai a jikinta amma kamar yafi na dazu kyau da kudi, riga da siket ne dinkin ya karbi jikinta sosai tai kyau tai ado da gold wuya da hannu sai tai amfani da set din jaka da takalmi da mayafi iri daya, mayafin a gefen kafada ta ajiyeshi, duk jikinta a waje breast dinta sun matse a cikin rigar don har sun dan fito daga sama, kishin hakan ya dinga sukan zuciyarsa ya cigaba da kallon hotonan wanda duk rabinsu ita da 'yan uwanta ne maza da mata sai kuma wanda Asp din ya shiga akayi musu ita dashi, shi kansa Asp din haushi ya bashi ya dinga jin kishinsa a ranshi, ganin yanda ya tsaya daf da ita bayan duk ga tsaraicinta nan a waje a maimakon yay mata magana ta yafa mayafinta tunda dai su 'yan uwan nata basu san abunda ya dace ba, shima sai yabi sahun su suna abunda bai dace ba........'Karamin tsaki yaja ya cigaba da duba hotonan yana kokarin danne abunda ke cin zuciyarsa. hoton ta ida Sakina shine ya dauki hankalinsa, kallon fuskar Sakinar da shigar dake jikinta shi kadai ya nuna masa zahirin ta, duk rashin arzikin dinkin dake jikin Zinat din yafi na ita Sakinar mutunci, domin gabadaya wuyar rigar dake jikin Sakinar net ne nonowanta duk sun fito gashi rigar ta matseta sosai ba mayafin arziki a jikinta sai wani uban gashin doki da tayi ado dashi, gabadaya kamar ba 'yar musulmai ba..........Murmushin dake kan fuskokinsu shine ya nuna masa cewa da akwai kusanci mai kyau a tsakaninisu domin hannuwasu ma a rike yake dana juna.........Gabadaya yarinyar bata kwanta masa a rai ba, ba tare da ya gama kallon hotonan ba, ya kashe wayar ya ajiye saman drowar haushi duk ishe shi. Koda Asp din ya kira shi domin ya shada masa cewa suna jirgi shi da amaryar tasa, sharrin zuciya sai kawai ya tsinci kansa da jin wani iri a ranshi, sai da yayi namijin kokari kafin ya iya yi masa godiya, Asp din yaji muryarsa a dakile, yace."Mutumina ya akayi ne naji ka wani iri."? Ya dan yi gyaran murya da kokarin kawar da abunda yake ransa yace." Normal ba matsala idan kun sauka ka kira ni yanzu ina dan uzuri ne." Yace."Okey to shikkenan ko na baka amaryar ne.''? Girgixa kai yay da fadin." Aa bar ta kawai zan kira ta an jima idan ta huta." Yanda yake jin haushinta ya san ba zasu wanye lafiya ba, shiyasa ya fadi haka. Wayar ya kashe ya ajiye saman drowr ya tsirawa kasan kafet ido. Alamu sun nuna yana son yarinyar nan, domin da baya sonta ba zai damu kansa har ya dinga kishi a kanta ba. Asp yafi karfin komai a gurinsa, kuma ya sheda cewa ba zai ci amanarsa ba, amma yana mamakin yanda zuciyarsa take raya masa wasu munanan abubuwa akan Asp din wanda yayi imani da cewa hakan ba zata faru ba, auziyya yayi a fili tare da korar shaidan din da yake so lallai sai ya nuna masa aibun abokin nasa. Hadiman ta wato masu yi mata hidima tare da motocin kayan garar da akai mata sune suka fara sauka, duk girman store din sai da yay kadan gurin daukar kayan garar, babu abunda babu na dangin ci da sha, da store din ya cika sai kawai aka jibge ragowar kayan abincin a harabar gidan. Asp sai da ya tabbatar da cewa komai ya kammala amarya na dakinta sannan hankalinsa ya kwanta ya godewa Allah kafin ya kira wayarsa ya sheda masa duk abunda yake faruwa. Yace."Asp nifa ban bukaci komai a gurinsu ba, me zai sanya akawo min abinci ina dashi ai ba wai ina bukata bane." Yace."Al'ada ce kawai kada ka damu ba wai dan ka gaza ko don baka dashi sukayi maka haka ba alkairi ne kawai." Yace."Idan za suyi ai sai ayi dai-dai gwargwado amma ace har mota goma ta kayan abinci me zanyi dasu mybe ma kafin azo kan wani ya lalace kawai ka diba iya wanda kake bukata, sauran kuma zanyi magana da Uwale domin ta bawa wanda ya dace." Yace."Hakan da kayi yayi dai-dai, amma ni kam babu abunda zan dauka acikin wannan kayan, akwai mabukatan da suke nema su ya kamata a rabawa. Yace."Shikkenan tunda kace haka idan akwai masu bukata a bangaran ka sai ka basu duk abunda ya dace." Yace."Okey babu damuwa zan duba insha Allahu. Godiya yayi masa sosai tare da ban gajiya kafin suyi sallama da junansu. Tun bayan fitar Asp din daga gidan, take bin dakin da kallo, duk iya hangenta bata hango abunda zata kushe a dakin ba, daga bedroom din har falon komai na kasar waje ne, kuma tsarin yayi mata babu abunda zata nema komai a kwai wanda zata bukata, toilet biyu d'aya a uwar daki d'aya kuma a falon, sai kicin dake can gefe a dai cikin falon, koda ta duba kicin din shima a shirye yake da komai na bukatar yau da gobe, hakan yayi mata dadi dama bata bukatar wani ya shiga sabgarta a gidan idan ba hadimanta ba. Ta gama duba ko'ina ta koma bedroom din ta zauna gefen gado tare da zabga tagumi, to yanzu fa wata sabuwar rayuwa za tayi tare da wasu sabbanin mutanan da bata san ya hallinsu yake ba, koda yake a shirye take da kowa duk wanda ya bukaci zaman lafiya da ita bata da matsala amma ba zata yarda da raini daga gurin kowa ba ciki kuwa harda wanda yayi dalilin zuwanta gidan. Ajiyar zuciya ta sauke tana tunanin akan irin zaman da za tayi da bagidajen mijin nata. Tsaki taja mai tsayi ta girgiza kai a fili tace." Idan yaso mu zauna lafia zamu zauna idan kuma yazo da tsiya to gidan ya tarar domin ba zan yarda da rainin hankali ba." Kamar dashi take maganar sai girgiza k'afafu take. Kiran wayarsa ne ya katse tunaninta, data duba taga shine sai taki d'aga wayar har sai da ta katse. Uzuri yay mata dan be kawo cewa iskanci ne ya ha nata daga masa waya ba. A karo na biyu sai da ta kusa katsewa ta daga, ciki ciki tai sallama. Be damu da abunda take ba ya amsa mata da fadin." Ya kike? ya kuma hidima da jama'a."? Shuru tai ba tace masa komai ba. Yace."Kin yi shuru ko baki da magana dani."? Ta dan ya mutse fuska da fadin." Umm! yanzu bacci na keji okay sai da safe." Kokarin kashe wayar take yay saurin fadin." Kada ki kashe waya ina da magana dake." Ta fasa kashe wayar da fadin "Ina jin ka." Jim yay kafin yace." Kina ina yanzu."? tambayar da yay mata kenan Tace."Wace irin tambaya ce wannan."? Dan murmushi yay kafin yace." Ke dai ki bani amsar tambayata." Tsaki tayi niyyar ja, sai kuma ta fasa tace."Abokinka ya kamata ka tambaya ai." Yace." Tun dazu nake kiran wayarsa bata shiga shine dalili. Tace." Okey to gani yanzu a cikin gidanka zaune daki." Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Alhamdulillhi dama abunda nake so naji kenan daga bakinki." Numfashi ya sauke kafin ya cigaba da cewa." Da bakin ki yanzu kike sheda min cewa kina cikin gidana zaune a daki a matsayin matata ta sunnah, bana gari anyi komai an gama duk ta dalilin jajurcewar abokina wanda ya tsaya min a cikin al'amara na, Asp hankalinsa bai kwanta ba sai da ya tabbatar da cewa kin zama mallakina bayan haka kuma be samu nutsuwa ba sai da ya tabbatar da cewa ya kawo ki har cikin dakinki ya ajiyeki kamar yanda ki ka sheda min a yanzu. Ina so ki san cewa ni mutum ne mai tsananin kishi akan abuna, duk da ga yanda akayi wannan auran namu cewa bana so bakya so hakan ba zai sa na zuba miki ido kiyi abunda ki ke so ba.........Katse shi tayi ta hanyar fadin." Me kake nufi ne."? Yace ." Alkairi nake nufi dake."? Shuru tai ba tace masa komai ba amma ya fara kai ta karshe........Ya cigaba da cewa." Yanzu sabuwar rayuwa zakiyi domin aure ba wasan yara bane. Ki kiyaye mu'amula da wanda
Chapter 36 · 0% Book details