Sashe 78
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
mahaifiyarta domin ta taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwarta. A daran ya dauketa suka kama hanyar gida. gabadaya tunaninsa ya tsaya cak! saboda duniyar ma gabadaya ta rikice masa ya rasa wane irin tunani zai yi, gani yake kamar duk abinda yake mafarki ne. Cikin dakinsa ta kwana, kuma babu wani abu da ya shiga tsakaninsu, to ina kwanciyar hankalin da wata mu'amula zata wanzu babu ma sha'awa a tare dashi. Da sassafe ta fita daga d'akin, lokacin yana toilet yana wanka. fitowar ta akan idon Marakisiyya, al'amarin da ya bata mamaki mutuka! ba tayi kasa a gwiwa ba taje ta sanar da Uwar dakinta abinda idonta ya gane mata. Tace ta tashi ta taje....bayan fitar Marakisiyyar minti goma ta nufi sashen nasa...........Koda ta shiga basu kwashe lafiya ba, dan da abun yayi tsamari ma turo ta yayi ta fadi bakin kofa ya mayar da kofarsa ya rufe, ya cigaba da abinda yake. Ta zauna taci kukanta ta k'oshi, ido jawur! ta fito daga sashen, sai sukayi kicubus da Hamra'un tayi wanka tayi ado sosai sai kamshin turare take.....kallon banza tayi mata kafin taja tsaki ta shige ta bar ta a gurin. Girgiza kanta kawai tayi ta nufi gurin Uwale domin jin k:arshen labarin. Ta sameta a zaune fuskarta akwai alamun damuwa. Suka gaisa sama-sama kowa da abinda ya dameshi a zuciya. Uwalen ce ta fara magana kamar haka......"Zinatu kiyi hakuri kinji ko, na san wannan abun shiryayye ne amma babu komai duk auran da ba'a gina shi ta hanyar Allah da Annabi ba, baya zuwa ko'ina kiyi hakuri da duk abinda za ki gani." Tace."Uwale me yake faruwa ne? naga yarinyar nan Hamra'u sai shige da fice take a gidan, shin yaushe ma ta dawo? kuma naji kina maganar aure, ban san me yasa ba tun jiya muke rigima da mijina na rasa abinda nayi masa." Murmushi takaici tayi kafin ta shiga warware mata abinda yake da akwai, tace." Ni kaina ban sani ba, sai yanzu da ita Hamra'un take sheda min cewa jiya da magariba aka daura auran shi Umar din da kansa yaje garin akayi komai a ka gama to kinji abinda yake faruwa. Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." To saboda kawai zaiyi aure sai ya zama tamkar mahaukaci! gabadaya fa tsakanin jiya da yau ya fice daga hayyacinsa. Tace." Ni kaina yau kwana biyu kenan rabon daya shigo mu gaisa da duk rintsi yakan shigo idan zai fita, sannan kuma idan ya dawo ma zai shigo ya dubani. wannan dalilin yasa nake zargin wani abu akan al'amarin. Tace." Uwale idan da matsala ni zan tattara kayana na tafi gida hankalina sai yafi kwanciya bana san tashin hankali." Ta kwantar da kai da fadin." Kada ki yanke wannan hukuncin Zinatu ki cigaba da hakuri duk abinda mijinki yake baya hayyacinsa. Asiri akayi masa." Ido ta tsira mata tana mamakin maganar ASIRI to waye zai yi musu ASIRI irin wannan. A tare suka shigo falon, duk suka zuba musu ido suna kallo....Ita Hamra'un kicin ta nufa, shi kuma ya zauna kusa da Uwale suna gaisawa. Babu yabo babu fallasa ta amsa sai kallonsa take tana mamakinsa.........Ya dan duba agogon hannunsa da fadin." Uwale sai ki kaji sabon al'amari ko."? Tace." Eh abun ya bani mamaki Umaru ya akayi ka sauya shawara."? Kai tsaye yace." Hakan ne samun kwanciyar hankalina domin bana samun nutsuwa a tare da wacce nake rayuwa da ita. Tace." Wannan maganar sam bata dace ba Umaru me yasa zaka sanja hali zaka kawo rashi zaman lafiya a gidanka." Yace." Uwale ki bar wannan maganar don Allah nifa dama can dole akayi min yanzu ne na auri zabin raina." Ta fusata! zuciyarta na tafasa! tace." Yanzu ma ba'ayi maka dole ba ka *SAKE NI MANA."!* Innalillahi wa'inna ilahi raji'un! abinda Uwale take nanatawa kenan, lallai Dayyiba bata da Imani tana so ta raba sunnar ma'aiki. Ta sake maimaita maganar kamar sabuwar mahaukaciya.....*"KA SAKE!* ni idan ka cika dan halak ne kai." Jikinta har karkarwa yake ta mike tsaye tana so taje gurin da yake zaune. Ya mike a zabure! da fadin" Kada ki kuskura kizo nan sai kakkarya miki 'kafafu." yana gwada yanda zaiyi da hannunsa.......Ba ta tsorata ba ta 'karasa da fadin." Gani dama tun jiya kake duka na ka karya ni kaga abinda zai faru." Ya daga hannu da niyyar zabga mata mari Uwale ta rike hannun tana kuka take fadin." Wannan wane irin tashin hankali ne Umaru anya ba za kayi wa kanka fad'a ba." Hawaye masu zafi suna gudana a saman fuskarta tace." Uwale ki kyaleshi ya aikata abinda yayi niyya dama ai ba yau bane farko. Tace." Aa ba za'ayi haka ba Zinatu kiyi hakuri ki koma gurinki insha Allah komai zai daidaita." Hanci ta shaka kafin ta girgiza kanta ta juya da sassarfa ta fita daga falon. Ya koma yana zauna yana wani irin nishi, sai gumi yake kamar wanda yayi 'yar tsere......Hamra'u dake tsaye da fulas din shayi a hannunta ranta ya 'baci ganin abinda takeso bai faru ba, jikinta a sanyaye taje ta ajiye fulas din kan daining ta koma kicin domin fito da sauran kayan breakfast din. Ta shiga sashenta ta sanya Baraka ta hada mata kayanta gida zasu tafi . Ta zaune gefan gado jikinta sai rawa yake ta nemi number Asp murya a dashe suka gaisa, tace." Zan tafi gidanmu ranka ya dade bahaushe yace." Ta inda aka hau ta nan ake sauka." Da sauri yace." Zinatu idan na isa dake kada ki kuskura kije ko'ina kinji abinda nace miki ko."? Kashe wayarta tayi bata tsammanin zata tsaya jiran wani abu. Wanka tayi a gurguje! ta shirya, ta umarci hadimanta suka shirya.......Direban dake dawainiya da gidan ya daukesu a mota suka dauki hanyar *KANO* Minti ashirin da tafiyarsu Asp ya shiga gidan, kai tsaye sashenta ya nufa........ya tarar ko'ina a rufe! hankalinsa a tashe ya nemi number wayarta a kashe. Hannu na rawa ya kira abokin nasa yana ganin kiran yaki d'auka idan akwai wanda ya tsana a duniya yake jin haushinsa Asp din ne. Yayi ta kiran wayarsa yaki dagawa, sai ya hakura ya shiga har gurin Uwale suka gaisa, anan ne ta san da cewar Zinat din bata gidan. Tafi Asp din shiga tashin hankali, lallai babu shakka a wannan karan dole ta tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/22/22, 07:32 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *115&116* Suna shirin tashi daga aiki mai girma Commissioner ya same shi a ofis, cikin girmamawa ya mika masa hannu suka gaisa kafin." Yace." Tunda naga mai girma da kansa to na san babban al'amari ne." Murmushi yayi kafin yace." K'warai kuwa Umaru wani aiki ne ya taso sai naga da cewar kaja tawaga ma'ana ka zama jagora a tafiyar." Yace." Insha Allah zan bayar da gudummawata. Wata takarda ya fito da ita yana masa bayani cewa za suje *ran gadi* Zamfara saboda rashin kwanciyar hankalin da suke fama dashi.....za su hadu da jami'an tsaron garin domin kawo karshen ta'addancin da yake faruwa. gwamnatin garin tare da jami'an tsaron can suka bukaci wannan taimakon daga gurinsu domin suna sa ran idan ya shiga cikin al'amarin za'a samu maslaha." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.'' Ranka ya dade babu matsala yaushe ne tafiyar."? Yace." Idan Allah ya kaimu gobe amma da Asubah zaku dauki hanya." Yace." To Allah ya kaimu lafiya, amma me yasa ba'a za'ayi tafiyar da Asp ba."? Girgiza kansa yayi da fadin." Akwai dalili shi akwai muhimman ayyukan da zamu gabatar tare dashi." Ya mika masa hannu da fadin." Allah yasa mu dace." Ya amsa da ameen ya rabbi. Sallama sukayi cikin mutunci da girmama juna. tun lokacin da Commissioner ya fahimci cewa Umar din ba irin mutanan da ake nuna su da yatsa bane ya kiyaye abinda zai kawo musu samun matsala domin ya fahimci cewar Umar din yana da babban matsayi a government house bayan haka kuma manya 'kasa suna ji dashi, domin shi kansa shugaban k'asa yana alfahari dashi saboda yana taka muhimmiyar rawa gurin dakile harkokin ta'addanci a kasa baki daya. A maimakon ya kira Asp ya sheda masa abinda yake faruwa sai kawai yaja bakinsa yayi shuru haka kawai yake jin wani irin haushinsa da kiyayyarsa a zuciyarsa duk wanda ya danganci yarinyar haushinsa yake ji. Asp ya samu labari a bakin Commissioner dole sai da sa hannunsa komai zai tafi dai-dai, koda yaga abokin nasa ne zai jagoranci tafiyar sai yayi mamaki mutuka amma bai nuna a fuskarsa ba saboda baya so wani ya fahimci cewa akwai sa'bani a tsakaninsu. Ya isa gida cikin tarin gajiya da damuwa da rashin walwala duniyar gabadaya tayi masa zafi ya rasa wane irin tunani zai yi. Ya samu Uwale ta had'a kayanta tsaf tana jiran shigowarsa, ganinsa sai kawai ta fashe da kuka! kariris! Hankalinsa ya tashi ainun! domin ko kadan baya kaunar damuwarta. Ya rungumeta a jikinsa yana rarrashinta, amma fafur! taki tayi shuru! ya kalli Hamra'u da tayi tsuru-tsuru! alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ita, yace." Me yake faruwa ne shin me kukayi mata."? Tace." Wallahi nima ban