← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 97

Sashe 30

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ita Aunty Zeey gurin zuwa kai kayan lefen ba, sai kawai ya bukaci mutane biyu daga b'angaran Uwale da wasu daga cikin 'yan uwansa da ita Madam din da Nabila yace suje su kad'ai ya isa. Hakan yayi wa Aunt Zeey din ciwo, domin ita babban burinta ta 'kulla abota da amaryar tunda taji an ce 'yar sarauta ce take san k'awance da ita dama kuma tana kishi akan cewa duk matan abokan mijin nasu kawayen madam ne, wannan dalilin yasa takeso tayi kwace Zinat din domin samun abokiyar shawara. Kasa hakuri tayi da abunda yayi mata ta kira shi a waya tana masa 'korafi akan me yasa zai mata haka, ai itama matarsa ce me yasa komai zai faru Madam ce a kan gaba ita gaskiya ta gaji da wannan abu, da yake yasan halinta sai ya rarrasheta da fadin shi beyi hakan da wata manufa ba, amma tunda ya fahimci tana so tayi abota da amaryar to idan ya dawo zai bata number ta sai su dinga gaisawa, hakan yayi mata dadi sosai tayi masa fatan dawowa lafiya. Babu wanda be yaba da kayan lefen ba, domin 'karshen isa da kasaitar mace kenan, kaya ne da aka kashe iyayen kudi gurin had'awa tun daga kan kayan shafe-shafe har kan under wears babu na Najeria takalma da jakkunansu sunfi kala ashirin, bayan manya manya atamfofi da lesuka da iyayen shaddudi da goyayen riguna na waje da mayafai masu asalin kyau da tsada, fashion na sarkoki kam ba zasu lissafu ba bayan gold din dake cikin akwatinsu set uku, kaya tamkar za'a bude sabon kanti..................Kowa ya yaba da kayan amma ban da ita, bata fito ta nuna hakan a zahiri ba, sai dai har hazar yau da kayan sukayi kwana uku a gidan ba ta duba taga meye a ciki ba, tana kallon dai 'yan uwanta suka d'ibar mata wasu daga ciki zasu bayar a dinka mata, shuru kawai tayi saboda bata so tayi wata magana su samu sa'ba ni da juna, suna ta murna da farin ciki gefe guda kuma suna shirye-shiryen yanda za'a gudanar da shagalin biki, ita dai ido ne nata duk abunda sukayi daidai ne, ta danne komai a ranta taki ta nuna musu zahirin abinda yake cikin zuciyarta. Aunty Zeey sarkin shishshigi da iya waje sai da ta san yanda tayi ta samu shiga a gurinta, ta waya suka k'ulla abota, kullum sai sun gaisa da juna, wani sa'in har ita aunty Zeey din take dan bata labarin wasu abubuwan da suka shafeta da mijinta da kuma kishiyarta.......Tayi ta mamakin al'amarin, wani lokacin idan taji tana zagin Madam da 'ya'yanta ta kanyi mamaki! Tace." Ni kam kinga na zauna da matar amma ban ta'ba ganin mugun halinta ba. 'Kwafa take da fadin." Don ba kishiyarki bace shiyasa amma ki san irin zaman da za kiyi da ita kuma kada ki dinga sakin jiki kina fad'a mata sirinki." Dariya ta kanyi a duk lokacin da sukayi irin wannan maganar ta kanyi mamakin yanda mata suke kishi akan namiji ita kam duk irin so da kaunar da takewa namiji ba zata lalace guri kishi a kansa ba, a ganinta kishin da ake a kansu shine yake sawa suna iskanci yanda ransu yake so, shiyasa ita da namiji babu mutunci. Aunty Zeey ita ta maye gurbin aminiyarta Sakina wacce ta tafi yawan siyasa sai dai duk abunda yake faruwa tana samun labari daga bakin k'awar tata, tana sa ran dawowarta kafin d'aurin auran. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 1/31/22, 07:31 - Buhainat: *45&46* Hamra'u duk irin bayanin da Uwale tayi mata besa ta hakura ba ta kwantar da hankalinta ba, mugun kishin Zinatu take, gabadaya ta kasa samun nutsuwa da kwanciyar hankali, gani take mutukar ya auri 'yar sarauta to maganar auranta dashi zai sha ruwa, da ta gaji da wasiwahsi da zuciyarta sai kawa ta yanke shawarar kiran wayarsa domin taji a matsayinta a gurinsa duk da cewa tunda ya tafi tsayin sati biyu da kwanaki goma be nema ta ba ballantana ya kira wayarta yaji ya take. Sai dai sa'i da lokaci ya kan kira Uwale su gaisa itama ba kullum ba, ita Uwalen ke bata sak'on gaisuwarsa gare ta, gashi kullum kara sonsa take da kishinsa, sam ta tsani wata mace ta kusance shi, gashi daj shine da bakinsa ya furta cewa yana sonta zai aureta amma duk wasu hanyoyi na nuna kauna da so da kulawa baya nuna mata, yanda ta lura kamar yafi bawa aikinsa muhimmanci a kanta. Ta kira wayar tasa gabanta na dan fad'uwa! dalili bata san irin kar'bar da zai yi mata ba. Koda yaga kiran nata beyi mamaki ba, sai da ya fita daga cikin jama'a sannan ya samu sararin amsawa. Murya a sanyaye ta gaisheshi tana langwab'ewa! ya amsa cikin kulawa da fadin." Ina fatan duk kuna nan lafiya aiki ya hana ni samun sukunin kiran wayar ku mu gaisa, ina fata dai kina samun sakon gaisuwata a gurin Uwale."? Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke murya na rawa tace." Eh tana fada min a duk sanda ku kayi waya, amma yaya na me yasa ni ba za ka kira waya ta domin mu gaisa ba sai dai ka bada sa'ko." Rashin abun fad'a yasa yace." Bana samun lokaci ne kullum cikin aiki nake wannan shine dalili amma kada ki damu har yanzu kina nan a cikin zuciyata." Girgiza kanta tayi da fadin." Ina kokwanto akan maganar ka domin na samu labarin duk abunda yake faruwa wanda ka boye min zaka auri 'yar sarauta wannan ne dalilin da yasa kake kokarin ka juya min baya." K'aramin tsaki yaja ya dan girgiza kai da fadin." Idan wannan ne tunaninki to ki daina domin ni ba a haka nake ba, aurena da Zinatu Allah ne ya kaddara! ban ta'ba tunanin had'uwa da ita ba, ballanatana har naji sha'awar auranta a raina, mahaifinta ne ya bani ita dalilin taimakon da nayi mata, babban mutum ne mai mutunci da dattako wannan dalilin yasa na kar'bi auranta domin yafi karfin alfarma a gurina." Cikin jin sassauci sakamakon maganganunsa tace." To shikkenan ni yanzu na kira kane domin naji matsayina a gurinka." Kansa ya dafe cikin rashin san damuwa yace." Wai shin Hamra'u sau nawa ki ke so kin san yaya matsayinki yake a guri na? na fada miki cewa ina sonki kuma ina da bukatar auranki saboda na yaba sa kyawawan halayenki wannan shine babban dalilin daya ja ra'ayi a kan ki, duk wasu kyale-kyale basa burgeni nagarta nake nema, amma duk da wannan bayanin da nayi miki na fahimceki kina kokwanto aikana shin me kike nufi ne."? Dan murmushi tayi kafin ta kwantar da murya da fadin." Kayi hakuri Yayana bana nufin komai sai alkairi, na fahimce ka kuma na amince da maganarka amma don Allah ka dinga nuna min kulawa sannan kuma tun kafin amaryar taka ta shigo gidanka ka sheda mata maganata domin ta san da zamana a zuciyarka." Maganarta ta bashi haushi da mamaki! Yace." Okey kina so ki tsara min yanda zanyi kenan."? Yanda yayi maganar cikin shan mur yasa tayi saurin fadin." Aa ba nufina kenan ba." Yace." Idan ba haka kike nufi ba menene na damun kanki? alamu sun nuna akwai wani abu da yake zuciyarki game da ita Amaryar tawa, kin gane ko bana so ki fito da kishinki tun yanzu yin hakan zai janyo mana samun sa'bani dake, bana son tashin hankali a gidana kiyi kokarin ganin kin kiyaye faruwar wata matsala.'' A sanyaye ta bashi hakuri da fadin'' Zata kiyaye insha Allah, zuciyarsa babu dadi yayi mata sallama ya kashe wayarsa ya koma cikin mutane domin cigaba da abunda yake gabansa. ***** A can masarautar kuwa komai yana tafiya kan tsari wata hatsaniya bata 'kara tashi ba, sosai Ta samu daidaito da zaman lafiya da 'yan uwanta, kowa yana kokarin faranta mata rai, kuma Komai na bukatar rayuwa an tanadar mata har da bayi wanda za taje dasu gidan mijin nata domin su bauta mata maza biyu mata biyu. 'Bangaran gyaran jiki kuwa har gajiya tayi domin kullum da kalar maganin da zata sha, al'amarin da ya janyo mata mugun ciwon mara wanda take kwana dashi ta tashi dashi ga wani ruwa da take zubarwa wanda ta riga ta fahimci ko na menene, haka nan take hakuri domin samun farin cikin mahaifiyarta tasan idan ta bijire to za'a ji kansu abunda bata fata kenan babban burinta ta samu ta rabu da ita lafiya. Ya kasance yau saura sati daya daurin auran Sakina tazo gidan suka rufe kofa suna tattauna maganar, tace." Kawata ni kuwa zan so ganin wannan mutumin da ya samu wannan gara'basa shiyasa fa mutum in yana da dama a hannunsa ya dama tun kafin wankin hula ya kaishi ga dare, don Allah dube ki sankaceciya son kowa kin wanda ya rasa baki da kirar Allah wadai kin tara duk wani abu da ake bukata wanda ya kamata a ce kin kasance matar daya daga cikin shuwagabbanin kasa amma zaki kare a auran wani dan kauye bagidaje mafarauci wanda yake ci a karkashin gwamnati wallahi wannan al'amarin sam beyi min dadi ba." Ido cike da 'kwallah tace." Ya zanyi Sakina dole nayi hakuri nayi biyyaya na zauna da mutumin nan domin hakan shine kwanciyar hankalina wallahi nasan idan na bijire wa wannan al'amarin iyayena suna iya tsine min albarka, Sakina baki ga yanda suke 'kaunarsa ba, haka mutumin yake da masifar kwarjini da shiga zuciyar duk wanda mu'amula ta had'asu........Kai tsaye ni ba zan kushe hallitarsa ba domin kyakykwa ne sosai gashi da kirar maza bashi da makusa fa, domin duk wani abu da mace take nema a gurin namiji ya mallaka hausawa suka juma'ar da za tayi kyau tun daga labara ake ganeta, kin ga dai ban san zahirin sa ba amma jarumtarsa ke nuna min cewa shi din ba rago bane zai iya daukewa mace dukkanin bukatarta, amma hakan besa naji ina sonshi ba, dalili shi ba abokin burmi na bane, naso an kyaleni na za'bi daidai dani na aura amma shi kaf family nasa mutanan k'auye ne matalauta, shima din
Chapter 30 · 0% Book details