← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 97

Sashe 14

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dabbobi marasa kyau yana ci a cikinsa. K'auri da karni! duk ya cika gurin! dole ta tashi domin sauya gurin zama, domin mutukar tana shak'ar hayaki da kaurin dake tashi agurin zata iya amayar da abinda taci. Ido ya bita dashi! be dauke ba har sai da ta samu guri ta zauna can nesa dasu, inda Allah ya takaita akwai hasken farin wata a gurin. Ta jima a zaune a gurin tana sakawa da kwancewa! sai yanzu ta san ya rayuwa take, ta taso cikin kulawa da gata da komai na jin dadin rayuwa, tunda take bata ta'ba tsammanin cewa akwai ranar da za tayi rayuwa mai muni irin wannan ba! babban tashin hankalinta rayuwa da d'an ta'addah! irin wannan, duk abinda yake a kanta bai janyo masa 'kima da mutunci ba, domin kuwa shine mutum na farko wanda yayi sanadiyar tagayyara rayuwarta, hakika ta tsorota da rayuwa da duniyar ma gabad'aya, A yanzu babban burinta ta samu ku'bta daga cikin wannan dajin, sannan tayi wa kanta al'kawarin ganin ta jefa rayuwarsa cikin kunci da tashin hankali kwantankwacin yanda yayi mata. Saukar wani abu taji saman wuyanta, da sauri tasa hannu ta buge! ta mike tsaye! wata lafceciyar tsutsa ce ta fado daga saman bishiya. Rintse ido! tayi tana kiran sunan Allah! kafin taji zirrrrrr a kan kafarta, tayi tsalle ta matsa gefe tana kallon gurin, ashe gabadaya gurin tsutsutsine suke yawo. Jiki na wani irin rawa ta bar gurin, tana isa inda suke ta iske sunyi shimfida sun gatange gurin da itacuwa tare da rufe gurin da Net! Tsayawa tayi a gurin ta kasa shiga, domin gabad'ayansu mugun haushinsu takeji! daga nesa ta hangoshi ya nufo gurin, d'auke kanta tayi tare da jan tsaki a cikin zuciyarta. Koda ya iso gurin bece mata komai ba, ya kama hannunta! kallonshi tayi kamar za tayi magana sai dai tayi shuru, jan hannunta yayi suka shiga gurin. Guri guda ya zaunar da ita, muryar rarrashi da kwantar da hankali ya aro yace." Ki kwanta anan gurin nayi miki alkawai cewa babu abinda zan bari ya sami rayuwarki." A maimakon hakan ya faranta mata sai kawai taja masa tsaki! ta kawar da kanta tana zumbura baki! Hakan da tayi ya bata masa rai amma sai ya danne! be dauki mataki ba ya fara kokarin barin gurin, ta bude baki da fadin." Mamugunci! insha Allah sai naga karshenka." Maganar ta bashi mamaki mutuka! sai ya juyo da wani irin murmushi a fuskarsa ya nuna kirjinsa da fadin." Me yasa kike so ki kaga bayana."? Ta zabura! da fadin." Saboda kai din azzalimi ne macuci.!! Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta" Saboda kai din azzalimi ne macuci."! to wai shin da take kiransa da wannan sunayen wane irin zalinci yayi mata tun farkon had'uwarsu? Still murmushin ya sake kafin ya furzar da iskar bakinshi, cikin gaggawa ya fita ya bata guri domin yana ji idan ya kara second a gurun zai iya nakastata. Ya jima yana fesar da hayaki kafin ya samu sassauci a zuciyarsa, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke! yana me sake jin sautin muryarta na amsa kuwwa! a kunnanta a cikin kunnuwansa, tunda ya taso lokacin kuruciya da girma gwargwamaya yake da *Maza!* bai ta'ba sanya mata a cikin al'amuranshi ba, saboda sanin hallayarsu! yana da tausayi mussaman akansu amma baya yarda da raini daga garesu, mace daya ce yake jinta a cikin zuciyarsa, domin duk ta tara abinda yake da bukata, hankali nutsuwa ilimi tarbiya da sauransu, ita kad'ai! yake ji a zuciyarsa zai rayuwa mai tsayi da ita, ya kai ma'kura a gurin iskancin da yarinyar nan take masa, yana tausaya mata amma ya lura ita bata gani ta daukeshi a matsayin macuci! to yana ganin zai fita daga harkata domin ya samu zaman lafiya. tare da gudanar da aikin dake gabanshi. *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin Mov ko airtal 1/21/22, 12:28 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ *MIJINA BAYA IYA GAMSAR DANI* ________________ *_Wannan ba sabon abu bane, da yawa mata suna kuka da hakan cewa duk sanda za suyi rayuwar aure da mijinsu basa samun gamsuwa, matsalar daga shi mijin ne daga zarar ya biya bukatarsa zai tashi, bai damu da damuwar matasa ba, wannan kuskure ne babba! idan kasan baka da cikakkiyar lafiya to kayi hanzarin neman magani domin kana aikata kuskure! mata suna da kawaici da hakuri mussaman a wannan bangaran, duk macan data bud'e baki tafadi wannan maganar to ka tabbata tura ta kai bango! shi aure na mutum biyu ne to kai d'an uwa bai kamata ka ajiye mace a gida don kana ta'kama kana ci da ita ka tauye mata hakkin aure ba, wannan abun shine ginshikin aure domin daga ranar da akace babu shi to matsala ta dinga afkuwa kenan, saboda haka d'an uwa kayi hattara daga ranar daka fahimci cewa ka gaza gurin sauke hakkin matarka, to ka tashi tsaye ka nemi magani, idan kuma kasa taurin kai kace kai lafiyarka lau ba zaka sha magani ba to babu shakka! komai yana iya faruwa..... ke kuma 'yar uwata, kada ki yarda shaid'an ya rimbaceki ki aikata wani mummunan aiki ta sanadiyar wannan matsalar, domin da yawa daga ciki akwai matan da suka famtsama kansu harkar banza, saboda rashin samun kulawa daga mazajensu, akan ki aikata hakan gwara ki rabu da auran ki roki Allah ya baki daidai da rayuwarki_* FREE PEGE *21&22* Hakika baka sanin amfanin mutum a rayuwarka sai ranar da wata musiba ta sameka, ya taimakawa rayuwarta, ita kuma ta daukeshi a matsayin abokin gabarta! tayi masa mummunar fahinta duk da irin taimakon da yake akanta, ni a ganina idan shi din macuci kamar yanda kullum take kiransa ba zata kai labari ba, domin da tuni ya keta mata haddi ya yasar da gawarta a dajin. koda yake kowane dan adam da irin tunaninsa, har yanzu ita tana shakku akansa cewa bashi ne ya sato ta daga gaban iyayenta ba. Kwanciyarta da kamar minti goma mugun k'aikaiyi ya tasheta, ashe tsutsar data sauka kan kafad'arta tana da dafi! kuma ta cijeta a gurin har ya kumbura sai tsuko! yake mata, yatsunta biyar tasa a gurin tana aikin sosawa amma kamar 'kara angiza kaikaiyin take, fatar gurin tayi jajawur! saboda susa duk ta kwaile. Hawaye kawai take tana jan hanci! daga wannan sai wannan! ciwuka a jikinta iri-iri! sosai take kuka tana kiran innalillahi-wa'ina ilaihi raji'un! Ya rage shi kadai a waje yana kai kawo a gurin, har yanzu zuciyarsa taki aminta da gurin, yana ganin kamar idan yaje ya kwanta wata matsalar zata faru! zagaya gurin yake karnukansa na binsa duk inda ya nufa sai koke-koke suke.........Alba ya cimma inda yake tsaye cikin girmamawa yace."Maigida yarinyar nan fa tun dazu ta ishi mutane da kuka." Yace."Me kukayi mata."? Da sauri yace."Wallahi maigida babu abunda mukayi mata kawai dai munji tana kuka shine nace bari na sheda maka." Ya girgiza kansa da fadin." Jeka gani nan zuwa." da sauri ya juya ya tafi. D'azu ta 'bata masa rai! ya hakura ya shanye amma baya tsammanin yanzu zata kawo masa shiririta ya saurara mata. Ya sameta sai gursheken kuka take gabad'aya ta cire rigar dake jikinta sai breziya sai soshe-soshe take. Ganinta a haka ya 'bata masa rai! rashin kamun kanta yana bashi haushi, idan ba hakaba ta san da cewa ita kadai ce mace a cikinsu mai yasa ba zata suturta kanta ba, kullum shike k'okarin ganin ya suturta ta a matsayinsa na namiji amma ita a cikin maza! saboda rashin sanin darajar kai take bude tsaraicinta. Tsaki mai karfi yaja ya juya yana kallon gurin da ya yaransa ke zazzaune! akwai tazara a tsakanin inda take, baya kuma tsammanin zasu hangeta saboda kafin ya fita sai da ya katangeta. Murya a sama! yace."Mayar da rigarki." ido gaja-gaja da hawaye! ta kalleshi, ya murtuke fuska! ko alama bata bashi tausayi ba, ya bude mata dukkanin idanuwansa! umarni ya sake bata, a dashe tace." Ka daina yi min tsawa! ko ka san abinda yake damuna."? Yace"Babu abunda ke damunki sai hauka! da gidadanci! idan ba haka mai zai sanya ki cire riga cikin maza." Wani abu mai nauyi ya tsaya mata a wuya! wai ace wannan gantalallan ne yake kiranta da mahaukaciya. Nauyin abunda ya tsaya mata a wuya ya hana ta magana sai uban hawayen dake tsere a saman fuskarta, abu biyu ne suka dameta a halin yanzu. "Mtswwww! tsaki mai tsayi yaja kafin ya fita da gurin, ya dawo da fitila a hannunsa sai da ya rage karfinta sannan ya tunkari inda take. Ta sake takure jikinta tana kallonsa yana dube-dube a gurin, rigar ya mika mata da fadin." Kar'bi kisa ko kuma yanzu nayi abinda ba kiyi tsammaninsa ba." Ta tsira masa ido! da jin shakkar maganarsa, ganin babu alamun wasa a fuskarsa yasa tasa hannu ta kar'bi rigar amma bata sanya ba, ta rike kawai a hannunta tana cigaba da sosa gurin dake mata ciwo. Ya haskata da fadin." Cire hannuki a gurin! da sauri ta cire! tsigar jikinsa ta tashi! ganin yanda gurin yayi jawur! har da kumburi! zuciyar musulunci, duk sai jikinsa yayi sanyi haka kawai baya so wani abu ya cutar da ita, burinsa bai wuce ya kaita gaban iyayenta lafiya lou ba. Sassauta murya yayi yace."Sannu yaushe hakan ya faru."? a maimakon ta bashi amsar tambayarsa sai kawai ta sake rurucewa da kuka!! Yatsansa yasa saman bakinsa da fadin." Shiiiiii." kukan bashi da amfani kiyi shuru zan taimaka miki." Ba tayi shuru ba kuma bata daina kallonsa ba, yace."Kina bukatar hakan ko."? Kamar wata sakarai ta daga mai kai! Yace."To ki zama jaruma! ki daina yawan kuka bashi da fa'idah."! Taji kamar ta kai masa duka! ta'ina zata iya daure wannan azabar! Fita yayi da kamar minti biyar ya dawo da magani a hannunsa. yayi zaman ra'kuma a gabanta cikin muryar da ya saba rarrashinta ya mi'ka mata maganin da fadin." Jarumata! kar'bi maganin ki shafa a gurun zai daina miki ciwo." Maganin ta kar'ba ta lakato a yatsanta, can bayan kafad'arta gurin ciwon yake ta daga hannu sosai tana kokarin shafawa hannunta ya
Chapter 14 · 0% Book details