Sashe 72
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nayi amma kada ki sake min wannan wasa hankali na ya tashi wallahi." Tace." To ba zan sake ba insha Allah.'' Yace." Uwale ta tashi."? tace." Eh tana kicin tana aiki." Yace." Idan babu damuwa ki kai mata wayar mu gaisa." Tace." To insha Allah bari na kai mata." Cikin jin dadi yace." Allah yayi miki albarka." Ta amsa da "Ameen tana kokarin tashi tsaye. **** Hamra'u da kanta ta shirya abincin ta zuba cikin kwanuka masu kyau ta jera kan tire kafin ta nufi bandaki a gurguje ta shiga wanka. A lokacin ne mahaifiyarta Dayyiba ta samu damar aikata mugun nufin ta. Ko kafin ma Hamra'un ta fito daga bandaki har ta sanya k'aramin d'anta ya dauki tiran dake dauke da abincin sun fita a tare. D'aya da rabi na rana Uwale na aiki a kicin Dayyiba tayi sallama a gidan. Uwale ta amsa ta fito daga kicin din tana mata barka da zuwa, kai tsaye daki suka nufa. Suka fara gaisawa tare da tambayar bayan rabuwa.....Dayyiba tace." Ai da wuri yau na gama abinci nace bari nazo mu gaisa na kuma ga matar Umaru kin san dama ni ban ta'ba ganinta ba." Uwale tace." Allah sarki sannu da kokari Dayyiba har da wahala haka to mun gode sosai." Tana murmushi tace." Babu komai Dambu ne na turara mata na san masu ciki da kwad'ayi watakila yayi mata dadi." Tace." Eh 'kwarai kuwa, bacci takeyi yanzu amma bari na leka na gani ko ta tashi." Lokacin da ta shiga dakin zaune ta sameta a bakin gado tun bayan shigowar Dayyibar ta tashi duk tana jin maganganunsu. Tace." Ashe kin tashi dama mahaifiyar Hamra'u ce tazo ku gaisa ta kuma kawo miki abinci." Tace."Allah sarki amma na gode sosai bari na fito mu gaisa." Ta juya da fadin." To bari na sheda mata." Shuru tayi tana nazarin al'amarin, mahaifiyar Hamra'u? ita sunan yarinyar ma bata kauna ballantana wanda ya danganceta. Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi da k'yar! yunwa sai sasakar cikinta take, abun goge baki ta dauko cikin kayanta. Koda ta fito bata zauna ba tukkuna sai da ta wanko bakinta ta dauro alwala sannan ta dawo dakin. A nutse ta zauna kusa da Uwale ta kalli Dayyibar dake mata wani munafikin kallo tace." Ina wuni fatan mun sameku lafiya."? A firgice ta amsa da fadin." Lafiya lou muke ya mutan gida da can gurin manyan." Tace." Duk suna nan lafiya lou." Daga haka sai ta kawar da kanta tana nazari akan matar kamar mara gaskiya. Uwale ta bud'e kwanunkan abincin da fadin." Dambu ne ko kina sha'awa." Kamshi ya bugi hancinta Dambun ya hadu yaji gyada da zogale ga k'amshin man gyada ziryan yana tashi...........Tunda take sau biyu kacal ta ta'ba cin irin wannan abincin, shima kuma irin na shinkafa bana masara ba , wannan dalilin yasa gabadaya ta rikice yaron dake cikinta ya nuna kwadayinsa akan abincin . Ta kalli Dayyibar da fadin" Na gode sosai." Tana washe baki ta amsa da babu komai dan nayi miki hidima kamar 'yar cikina kike." Murmushi kawai tayi ta kalli Uwale da fadin." Nayi sha'awarsa.". Uwale tasa dariya da fadin.'' Ai dole ni kaina ya bani sha'awa ballanatana ke da kike da lalura." Dayyiba ta dinga dariyar farin ciki tace." Ai kin san Hamra'u ta gwane gurin iya abinci gargajiya dama na turawan kowacce mace tana da baiwa, amma tabbas duk macan da ta iya girki zata samu soyayyar mijinta. Ba ita Zinat din ba har Uwale sai da taji babu dadi da maganar Dayyibar dan kamar maganar tayi kama da habaici. Babu dai wanda yayi magana a cikinsu, ta zuba mata a ma daidaicin plate. tayi bisimillah ta fara ci a nutse ba ta tunanin komai a ranta. Sosai dambun yayi mata dad'i, tas ta cinye wanda yake gabanta. a cikinta tana jin k'oshi amma a bakinta ba ta gaji ba, haka dai tayi kawaici tasha ruwa.Uwale ke tambayarta, tace." A yanzu dai ta koshi sai zuwa an jima tukkuna." Dayyiba mahaifiyar Hamra'u zuciyarta fes! ta fita gidan, babban burinta cikin ya zube ko kuma Gimbiyar ta galabaita. Aikuwa dai jikinta ne ya mutu kasala ta dame ta, sai kawai taje ta kwanta tana ya mutse fuskarta cikinta ne yake hautsinawa zuciyarta na tashi. Minti ashirin da kwanciyarta ta tashi a gigice! sakamakon jin wani irin mahaukacin amai da yake taso mata. Bakin rariya ta gurfana ta dinga sheka aman tana rike kirji! Uwale hankalinta ya tashi ganin mawuyacin halin da Gimbiyar ke ciki. Ta rike ta tana mata sannu a lokacin kanta ya dinga juyawa tayi kwance a gurin tana mayar da numfashi. Uwale tace." Sannu ki daure ki tashi ki koma daki ki kwanta a can kinga nan akwai rana gaki a bakin kwata a kwance." Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, gabadaya ma bata cikin hayyacinta, tana jin yanda cikinta yake kartawa! wannan karan ba amai takeji ba zawo! ne mai karfi yake kokarin kwace mata. Kokarin tashi take domin shiga bandaki abun ya gagara domin gabadaya jikinta ya shika babu kwari! duk yanda taso da ta daure ta kasa ba ta ma san lokacin da zawon ya kwace mata ba, kawai sai tsuuuuuu! ta dinga jin fitarsa kamar an kwance famfo. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! shine abinda Uwale take nanatawa. (Cutar a mai da gudawa!) ya kama 'yar mutane! cutar dake saurin halaka mutum, hankali a tashe ta nufi gidan Tasallah. Suka shigo tare lokacin gudawar sai bin rariya take ita kuma tana kwance a gurin sai matagugu take domin wani masifaffan ciwo cikinta yake mata. Tasallah tayi salati tana sanar da Ubangiji kafin tayi azamar fita, gidanta ta koma da yake akwai magungunan gargajiya da take aje dasu, ta daga karkashin gadon karfenta ta dauko ledar maganar duk tayi kura da dauda! da yanar gizagizo ajikin ledar ta dauka ta fita. Aje ledar tayi a gefe ta taimakawa Uwalen suka fara gyarata, idonta a lumshe yake amma duk tana jin taretaran da suke da ita, ta riga ta mika wuya yanda take jin jiki bata tsammanin zata rayu. Jikinta suka wanke mata lokacin anyi sa'a Gudawar ta tsaigata da zuba. Uwale tayi saurin dauko mata wasu kayan da wando da rigar nono suka sanya mata jikinta mikar da ita sukayi kafafunta suka dinga kyarma! a daddafe suka shiga da ita daki. Uwale ce ta shiga gyara gurin, ita kuma Tasallah sai da ta tsaftace hannuwanta, sannan ta kwance ledar maganin data dauko ta fito dasu a daddaure! daka gani sun jima a ajiye, wuta ta hura kafin ta wanke maganin tas ta zuba a tukunya tasa jar kanwa sannan ta d'ora a wuta. Sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke domin yasha iska. To cikin ikon Allah da hukuncinsa tana shan wannan magani ta samu sassauci ciwon cikin da yake damunta yayi sauki baccin wahala ya d'auketa. Uwale ta kalli Tasallah da fadin." Sai yanzu hankalina ya kwanta Tasallah al'amarin nan ya tsorata ni mutuka." Tace." Dole ne, ni kaina ganin yarinyar a galabaice sai da na firgita kasancewar na san cewa wannan cutar na saurin halaka mutum! Allah yasa akwai ajiyayyun magunguna kinga cikin ikon Allah sunyi amfani " Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Tasallah nifa ina zargin Dayyiba." Shuru tayi tana kallonta da mamakin maganarta. Tace." Tun bayan da yarinyar nan taci Dambun da Dayyibar ta kawo mata shikkenan ta rikice shiyasa nake zargin ko da abunda tayi. Tace." Uwale zato zunubi aka ce koda ya kasance gaskiya ne, ni kuma nafi tunanin ko sauyin cima ne da ruwan sha, kin san hakan na iya janyo faruwar mummunar matsala. Tace." Idan hakane me yasa jiya da taci abincina ta kwana lafiya? ruwa kuma ba irin wannan muke sha yarinyar take sha ba, kafin mijinta ya tafi sai da ya siya mata ruwan roba gashi can a daki kwali guda. gaskiya ina zargin Dayyiba. Tasallah tayi murmushi da fadin." Hakan na iya faruwa amma kada kiyi gaggawar yanke hukunci tukkuna. Shigowar Hamra'u ne ya katse maganar, babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska, ta zauna suka gaisa, kafin ta kalli Uwale da fadin." Ummana ta kawo miki Dambu ko."? Tace." Eh ta kawowa dai Gimbiya." Ta dan 'bata rai da fadin." Ai naki ne kasancewar na san kina son Dambun masara yasa na tashi da wuri nayi miki, ko kafin na fito daga wanka na samu Ummana bata gidan wai ashe anan tazo." Tace." To Na gode sosai Allah yayi miki albarka." Tasallah na 'yar dariya tace." Hamra'u kenan to menene dan kishiyarki taci ai abun burgewa ne " Zumbura bakinta tayi tana ya mutse fuska.......Dukkaninsu babu wanda yaji dadin abinda tayi, kiri-kiri take nuna kishinta a fili. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/15/22, 22:22 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *107&108* Sai gefin magariba ta tashi daga baccin daya d'auketa, jiki babu kuzari ta tashi zaune da sunan Allah a bakinta, shiru tayi tana tunanin irin wuyar da tasha a d'azu, tabbas da kwananta ya 'kare babu wanda ya isa ya hana Allah zartar da Allah ikonsa, sam ba tayi tsammanin cewar zata sake