Sashe 68
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dattako. Maimartaban yake sheda masa cewa suna da baki da misali sha biyu jirginsu zai sauka anan filin jirgi na Katsinan. Farin ciki yayi sosai ya dinga godiya tare da adduar Allah ya saukesu lafiya. Sukayi sallama cikin girmama juna. Cike da farin ciki ya kira wayar ta. Fitowarta daga wanka kenan tayi saurin dauka tare da zama gefan gado. Ya sheda mata abunda yake faruwa. Jikinta a sanyaye tace." Me yasa ka sheda musu abunda yake tsakanimu.''? murya na rawa take maganar Yayi shuru yana nazarin maganarta. Tace." Shikkenan na shiga uku ka janyo min bacin ran iyaye na." Ya kwantar da murya da fadin." Ni fa ban fada musu maganar da wata manufa ba, na fada musu ne domin su ta ya ni neman mafita, amma bana fatan ranar da zan shiga tsakaninki da iyayenki." Ta share hawayen saman fuskarta kawai ta kashe wayar saboda kukan da yake kokarin kufce mata. Sake kiran wayar yayi tana kallo tana ringing taki dauka, ita yanzu tashin hankalinta zuwan Mahaifiyarta tasan bacin rai ne zai biyo ba. Babu kuzari a tare da ita ta kimtsa jikinta, ta nemi kujera ta zauna tana duba agogo sha biyu ta gota tasan yanzu mybe sun sauka . Wayarta ta d'auka cike da fargaba ta kira mahaifiyarta. Murya na rawa tace."Mommy ina wuni."?. A dakile ta amsa gaisuwar. Ta daure tace." Kun sauka ne."? Gimbiyar tace." Eh sun sauka dan yanzu suka kira waya, babu ni 'Yar uwata ce sai yayyunki." Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sanyi a zuciyarta tasan SAFAH tana da sanyi rai ba kamar mahaifiyarta ba. Ta katse tunaninta da fadin.'' Kin kyauta abunda ki kayi ZINA kin janyo min zagi da cin mutunci na gode." Ba ta jira amsarta ba, kawai ta kashe wayarta. Ita kam shuru tayi da waya a hannunta gabadaya ta rasa ya za tayi da rayuwarta. SAFAH tare da Hassana da Hussaina da Magajin sarki suka sauka a gidan......Farin cikin ganinsu yasa ta fashe da kuka! ta dinga rungumesu duk ta rasa yanda za tayi saboda jin dadin ganinsu. Magajin Sarki yace." Ki samu nutsuwa haka zuwan mu gidanki baya nufin farin cikin ki. akwai babban dalili ne ya kawo mu gidanki." Ta nemi kan kujera ta zauna jikinta duk a sa'bule. Ya fara yi mata fad'a tare da kawo mata ayoyin al'kur'ani da hadisai duk dai akan abunda ta aikata mara kyau! Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, dukkaninsu kowa ya tofa albarkacin bakinsa mussaman SAFAH da ta dinga yi mata nasiha mai ratsa jiki anan ne ta zubar da hawaye, tana kukan tace." Mammah dan Allah ku gafarce ni wallahi tsautsayi ne da son zuciya insha Allah ba zan sake maimaita abu mai muni irin wannan ba. Hassana tace." To Alhamdulillhi haka muke so muna rokon Allah ya sauke ki lafiya ya kuma inganta duk abunda zaki haifa." Gabadaya suka amsa da "Ameen." Kafin su fara yun'kurin tafiya. Tace." Mammah har zaku tafi ni wallahi na dauka kwana za kuyi." Magajin Sarki ya harareta da fadin." Sai kace mahaukata ko."? Ta 'bata rai da fadin." Aunty Hassana don Allah ku zauna ku kwana mana." Hussaina tace." Baki da hankali ZINA daga zuwa sai mu kwana ke a ganinki hakan yayi dai-dai"? Tace." To meye wallahi babu matsala kuna gani dai kowa da gurinsa to me zai dame ku." SAFAH ta mike tsaye tana gyara yafan mayafinta da murmushi a fuskarta tace." Zinatu rigima kin ga tashi kiyi mana Jagora cikin gidan mu gaisa dasu. ke kanki kin san abinda kike bukata ba mai yuwu wa bane. Cike da rashin dadi ta tashi ta shiga daki domin dauko mayafi, nan Aunty Hussana ta bita dakin ta bata wata leda dake cike da turarukan wuta da humra masu kamshin gaske, sai kuma kaninfari da yawa cikin wata leda a d'aure, tace mata ta jika cikin wani abu tana shan ruwan. Godiya sosai tayi mata kafin su fito daga dakin a tare. Uwale tsohuwa mai dattako! ta kar'be su hannu biyu tana ina a saka ina a sauke dasu.......Da yake basa rabo da abinci ta sanya Hamra'u ta had'a musu abinci wanda zai gamsar dasu. Haka nan suka saki jikinsu suka ci abinci wanda Hamra'u ta sarrafa sosai Allah yai mata baiwar iya sarrafa abinci ko wane iri ne a zahiri suma sun yaba sosai kuma ci sun gamsu. Itama ZINAT din taji dadin yanda aka karramasu ta saki jikinta tamkar akwai sabo a tsakaninsu, har tana jan Hamra'un da hira, wanda hakan ya basu mamaki mutuka, to itama dai Hamra'un saki tayi kamar wani sa'bani bai ta'ba shiga tsakaninsu ba. Tafiyarsu keda wuya ya kira wayarta yana tambayarta. Tace." Ai har sun tafi." Cike da mamaki yace." Sun tafi."? Tace."Eh nima wallahi babu yanda banyi dasu ba su kwana amma sun tafi kamar ana korarsu." Ya girgiza kai da rashin jin dadin hakan, yace." Me yasa da zasu tafi baki kira ni kin sheda min ba, sai na bar duk abunda nake nazo mu gaisa." Tayi shuru domin ba tasan me za tace ba. Yace." Laifin duk naki ne Zina kwata-kwata banji dadin tafiyarsu ba naso mun gaisa da juna sosai." Tace." Kayi hakuri amma ai sun gaisa da Uwale har suka ci abinci a gurinta. Yace." Hakan ma yayi amma Uwale daban ni daban." Tace." Hakane kuma." Shuru ya ratsa tsakaninsu kafin tace." Daddare me kake bukatar ci."? Kai tsaye yace." Towon dawa da miyar kuka." Iya gaskiyar sa ya fadi maganar. Amma sai ta kyalkyale da dariya da fadin." Towon dawa! gaskiya ni ban iya ba." Yace." Aikuwa ki koya domin shine favorite d'ina mussaman dumame towo ko wane iri ne ina sonsa. Tace." To shikkenan kada ka damu yau ma da kaina zan maka abincin insha Allah." Yace."Okey da can bake kike ba kenan."? Da sauri ta gyara maganarta tace." Ni ce mana ina nufin yau na mussaman zanyi maka towon da kake so. Yace." Idan da akwai matsala ki zauna ki huta kin san baki da koshin lafiya." Murmushi tayi da fadin." Naji sauki ai ina bukatar samun ladan aure." Murmushi jin dadi yayi yana juyi kan kujerarsa yace." Shikkenan yau da daddare za muyi hira kenan." Tana 'yar dariya tace." Sosai irin wacce ba mu ta'ba yin irinta ba." Yace." Alhamdulillhi na gode Allah da ya bani ke a matsayin matata." Tace." Nima haka amma dai ka yafe min laifi na ko."? Ya gyara zamansa da fadin.'' Na yafe miki kuma da ikon Allah zan d'aga miki ki shiga aljanna Bakya laifi a guri na GIMBIYATA." Tace." Na gode *Mazan Fama!* Allah ya barmu tare." ya amsa da "Ameen wani irin farin ciki na ziyartarsa. Aikuwa kamar yanda tayi masa alkawari, da kanta ta shiga kicin din, ta sanya Marakisiyya ta harhad'a mata komai wanda zata bukata, yau abunda bata ta'ba yi ba zata kwatanta. Ita kad'ai a kicin din tana gwagwarmaya! duk ta jigata, sai gumi take abunka da wanda bai saba ba. Akayi rud'e kalau! aka rufe ruf! sannan aka shiga had'a miya, tayi dubarar silala naman da albasa da kayan 'kamshi amma bai wani dahu sosai ba, ta zuba su daddawa da kayan miyan data murza a gireta, ta zuba uban farin mai tamkar me shirin yin jar miya.........Can rud'en dake rufe ya fara za'bal'bala kafin kice me murfin tukunyar yayo sama talgen ya fara kumfa yana zuba saman gas din, da sauri take k'okarin cire murfin aikuwa ta 'kone a hannu!! baya ta matsa tana ihu!! taje ta kwance famfo tana wanke talgen daya kona ta. kuka ne kawai ba tayi ba fatar hannunta tayi jajawur! ido jawur! ta fita daga kicin. Ta zauna kan kujera tana mayar da numfashi..........A'a abu kamar wasa hannu ya fara tashi! ga wani irin zafi da yake mata......kira ta kwalawa Marakisiyya tace mata maza taje ta k'arasa ita tayi abunda zata iya. Tashi tayi ta shiga d'aki ta kwanta, tana jinyar hannunta. Daf da zai shigo gidan ya kira wayarta, ta daga su gaisa yana tambayarta jikinta, tace." Lafiya amma garin yi maka towo na k'ona hannu. Yace." Subahanallahi garin ya hakan ya faru."? A shagwabe tace." Talgen ne ya dinga zuba naje bude tukunya ya zubo min a hannu." Yaji duk wani iri a jikinsa yace." Sannu my love amma ba sosai bane ko."? Tace."Eh ba sosai ba amma har ya tashi sai ciwo yake min." Yace." Yi hakuri kinji bari yanzu zanzo nai miki addua insha zaki ji sauki." A sanyaye tace." Okey my darling na gode sai ka shigo." kashe wayar yayi yana Allah-Allah ya isa gidan. Wanka tayi ta kimtsa domin bata so ya shigo ya sameta babu ado, tunda tasan yana san haka shiyasa ta mayar da hankali gurin yi masa ado da kwalliya na kece raini. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/9/22, 22:27 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *99&100* Wani sanyi ne ya ziyarceshi yayin da yayi tozali da ita a hakimce tayi ado irin wanda yake bala'in burgeshi, in ban da kamshi babu abunda take........Gabadaya wata irin kasala ta rufeshi tsananin sha'awarta ya sake kamashi, shi dai yana bala'in son