← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 97

Sashe 43

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zama a gida, ranka ya dade sati daya ya ishe ni." Asp din yace." Okey shikkenan tunda kace haka amma nasan nan gaba da kanka zaka nemi hutun." Dariya kawai yayi sam bai bawa maganar muhimanci ba, a ganinsa babu yanda za'ayi ya dauki hutu na wata saboda wata mace. Cike da wasa da dariya sukayi sallama da commissioner din wanda yayi kokarin danne bacin ransa, domin ya tsani wannan kusancin dake tsakaninsu. Tun a mota Asp din ya kira ta ya sheda mata cewa ta shirya kar'bar angonta gashin suna tare yanzu iso gidan." Gabanta ne ya shiga fad'uwa, ta tashi zaune tana sa'ke-sa'ke, ba wai tsoron haduwa take dashi ba, kawai a jikinta takejin kamar akwai abinda zai faruwa a tsakaninta dashi. Wanka tayi ta cancand'a ado turaruka masu dadin kamshi ta fesa a jikinta. Sai dai tana fitowa falon tayi saurin toshe hancin ta, har yanzu akwai sauran wari da hamamin mutanan 'kauyen. Baraka ta 'kwalawa kira da suke kicin suna aiki.......ta fito da sauri tare da risinawa, har yanzu hannunta na toshe da hancinta tace" Ki san duk dubarar da za kiyi wannan warin ya fitar min a falo." Tana gama maganarta ta koma cikin dakin. Baraka ta dinga bunka turaran wuta sako da loko na falon tana hadawa da air freshener da turaran tsinke, amma ina warin daban kamshin turaran ma daban. Motar tana parking yaran shi, da suke dakon! isowarsa suka mike tare da karnukansu! kafin kice kwabo gurin ya kacame! da bushe-bushe! gami da gangi mai taken sunansa! Fitowarsa daga motar ta sanya karnukan wani irin haushi!! gabad'aya suka cika gurin kafin su zagaye shi sai koke-koke suke suna shanshana rigar jikinsa, da alama sun jima kewarsa........... Gabad'aya jikinsa ne ya rikice! kafin kice kwabo gumi ya fara yanko masa daga kowace kusurwa ta jikinsa! ganin haka ya sanya yaran nashi cigaba da bushe-bushen suna masa kirari irin wanda suke masa. Rigar jikinsa ya fara kokarin cirewa, Asp ya zuba masa ido yana mamakin abinda yake shirin faruwa...........Har singlet din dake ciki be bari ba duk ya cire ya mi'ka masa tare da rigar. Ya kar'ba kawai yana kallon ikon Allah...................Ya kalli gabas! yamma! kudu! a rewa! kafin ya kurma wani irin ihu!!! wanda ya jima beyi irinshi ba, aikuwa gurin gabadaya sai da ya amsa!!! Ihun! sai da ya ziyarci cikin gidajen mutanan dake Barack din, Uwale ta zabura! ta mike tsaye da fadin.'' UMARU ya sauka domin ga alama nan.........Mazan ne suka fara turareniyar fita, su kuma matan suka cigaba da tsumayin shigowarsa. Gabad'aya jikinsa ya bud'e Damtsan hannuwansa suka wani kumbura! jijiyoyi rad'od'o!! Sai wani irin motsi suke. tsigar jikinsa duk ta mike! gumi sai karyo masa yake daga kowace ga'ba ta jikinsa. ihun!! yake kafin ya fara yi wa kanshi kirari kamar haka.............! *" Namiji uban maza!! UMARU! Uban UMARU! d'aga Tanimu, Kandagarki kurmar dutse mugun makaganri sai kure! Naci dubu sai ceto! nayi tawa kuma nayi ta wasu! Ni ne K'adangaran bakin tulu mai maganin wani Takadiri! guguwa! maganin barazana! Namiji a cikin maza! UMARU mai masoya gabas! yamma! kudu! a rewa!!" Yana wani irin nishi yake kirarin tare da dadura! wuka! a kowane sassah na jikinsa.* Tun sa'ilin da ya fara ifece-ifecen! Asp din ya fito da wayarsa ya fara masa vedio sosai abun ya bashi sha'awa, ya dinga masa vedio da hotona a lokacin da yake kai kawo a gurin yana ciccije! baki tare da gurzar jikinsa da kaifaffar wu'kar! da ya fizga a jikin yaron shi Alba. Kawu Ado ne ya k'araso gurin da 'kyar ya samu nasarar rike hannunsa, sai ya fara kwantar masa da hankali yana shafa kirjinsa dake cike da gargasa...........Ya dinga sauka a hankali a hankali amma har yanzu numfashinsa bai dai-dai ta ba. Asp yayi serving din duk abunda ya d'auka ya mayar da wayar ajihunsa, in da suke ya nufa, a hankali yasa hannu ya kar'bi kaifaffar wukar dake hannunsa, ya mik'awa Alban tare da bashi umarnin mayar da ita gidanta. Numfashi da huci kawai yake fesarwa gabad'aya hancinsa duk ya bude gumi shar'ban a saman karan hancin, Asp din ya fara kokarin mayar masa da rigarsa, ya daga masa hannu alamun ya bari. Kawu Ado yace." Kyaleshi ya sarara tukkuna ai duk ranar da tsumin ya tashi mu kan rasa gane kanshi Yace." Okey to idan hakane kuwa yana bukatar hutu bari kawai mu shiga dashi cikin gidan." Kawu Adon yace." Hakan shine maslaha. Duk yana jin su tsabar rashin nutsuwa ya ha nashi magana, babu abunda yake bukata a yanzu sai haya'ki walau na Shisha ko na Sigari. Jiki a masifar sanyaye ta saki labulan ta samu gefen gado ta zauna tana jin wani fad'uwar gaba! duk badakalar da take faruwa faru a kan idonta, domin itama tana jin azababben ihun! ta zabura! ta mike tsaye da farko gigicewa tayi ta shiga neman ma'boya domin ba ta manta irin kicimilin wahalar da tasha a daji ba, jin ihun!! yana kara karfi had'e da sambatu yasa ta gazgata cewa shine ya sauka a gidan. Gabanta na wani irin bugawa taje ta zuge window da kyar ta d'age lalube, duk da akwai tazara mai tsayi hakan be ha nata hango cibad'idi'n da yake faruwa a gurin ba. Mamaki take sosai akan al'amarin sa, wane irin mutum ne mai taurin kai wanda wuk'a duk kaifin ta bata yanka shi, haka fa ya dinga yi a daji, ta dinga kuka domin ita a ganinta wannan kaikkafar wukar a take za tayi kisa amma ko gezau! idan yana dadurawa jikinsa har wani tsalle yake, gabadaya yanzu al'amarinsa tsoro yake bata. Asp ne ya shiga dashi dakinsa ko'ina tsaf tsaf kamshi sai tashi yake wannan duk aikin Hamra'u ne, domin tun bayan tafiyarsa ba ta bar aikinta ba, duk bayan kwana uku take shigowa ta gyara ko'ina tasa turare. Ya kalleshi da jajayen idanuwansa da suka rine sakamakon tashin tsumin jikinsa........"Bani Sigari." Ya fada tare da mika masa hannu.......Da yake Asp din ma ya dan busawa sa'i da lokaci shiyasa baya rabo da ita a jikinsa ko a motarsa sai ya shiga laluban jikinsa, babu ko kara d'aya, da sauri ya fita domin duba masa a cikin mota. Kasa hakuri yay ya mike ya fara binkice dakin, *Shisha* ya dauka ya zauna kasan kafet ya fara tada hayaki, Asp ya shigo ya samu dakin ya turnuke bece masa komai ba ya zauna gefansa yana kallonsa. Sai da ya tabbatar da cewar ya sha'ki hayakin ya ishe shi sannan ya ajiye, yana fesar da wanda yay saura a bakinsa. Asp din ya kalleshi da fadin." Yanzu dai na tabbatar da cewar ka samu relief kamar yanda kake bukata." Shuru yay na minti biyu kafin yace." Alhamdulillhi wanka zanyi na huta domin bana tsammamin zama da kowa a yanzu sai Allah ya kaimu gobe." Yace." Hakan yana da kyau, yanda kayi wannan gumurzun nima zan so ka huta ka samu nutsuwa kafin wani abu ya biyo ba......Ya mike tsaye da fadin." Bari na shedawa Gimbiya cewa tazo ta had'a maka ruwan wanka ko."? Yana yar dariya ya kare maganar. Kallonshi kawai yay yana mamakin furucinsa, shima Asp din be sake wata magana ba, ya kama hanyar fita yana amsa kiran da akayi masa a waya. Duk da ya damu yin wankan amma sai ya kasa tashi domin yaje yayi, kawai ya zauna jiran zuwan yarinyar kamar yanda Asp din yace, amma shi a jikinshi yana ganin kamar hakan ba zai yiwu ba, kawai dai ya biyewa san zuciyarsa ne. *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/11/22, 06:44 - Binta: *GSUR* *63&64* *ROMANTIC Da 'kyar da jibin goshi Asp din ta shawo kanta har ta yarda da zuwa sashen angon nata.........Asp din ya cigaba da kwantar da murya yana rarrashinta tare da bata tabbacin cewa shi angon nata ne yake bukatarta a kusa dashi yana kuma da kyau taje ta kula dashi kamar yanda sauran mata suke yi. Ta kalleshi cikin rashin walwala tace." Ai shi ya kamata yazo guri na bani zan kai kaina ba, kamar yanda ka fada idan ya damu dani to ya tako kafarsa yazo inda nake." Ya 'bata rai da fadin." Zinatu idan baki min wannan alfarmar ba to babu shakka zamu 'bata zanyi fushi dake irin wanda ban ta'ba yi ba, Zinatu kwata-kwata bana sonki da wannan dabi'un kullum so nake ki zama mace ta gari, bayan haka kuma shima nai masa magana akan abunda yake aikatawa ya kar'bi laifinsa domin da bakina da nasa yayi min alkawarin gyara kuskuransa, saboda haka kema ki ajiye duk wata kiyayya da kike masa ki zauna lafiya dashi. Jikinta ne yayi sanyi ganin yanda ransa ya ba'ci! Tabbas mutumin ya cancanta da komai saboda mutumci da kuma hallacinsa, wannan dalilin ne ya sanya ta amince da Uzurinsa amma ba dan ranta yaso ba. Tunda suka doshi sashen gabanta yake wani irin faduwa ta rasa meye dalili. Suka tsaya bakin kofar ya kalleta da fadin." Bisimillah ki shiga yana ciki ni dama munyi sallama dashi zan wuce gida yanzu." Shuru kawai tai tana kallonsa. Had'e fuskarsa yayi don kada ta kawo wasa yasa hannu ya bude mata kofar falon, da hannu yayi mata alamar ta shiga. Wata irin ajiyar zuciya ta sauke! kafin ta dan girgiza kai, saboda gudun bacin ransa zata shiga a ganinta ai shi ya kamata ace yazo gurinta, amma Asp yafi karfin alfarma a gurinta. Tana shiga ya mayar da kofar ya rufe.........Ta tsaya bakin kofar falon tana bin ko'ina da kallo, shuru kamar baya ciki ko'ina tsaf-tsaf! kamshi mai dadi sai tashi yake. Ta jima a tsaye a bakin kofar falon tana sa'kawa da kwancewa kafin ta yanke shawarar da zuciyarta take ba ta. Tana kokarin bude kofar domin fita, gyaran muryarsa ya dakatar da ita. Kasa juyowa tayi ballanatana taga halin da yake ciki. Asp din ne ya kira shi a waya yace ya fito falo ga amaryarsa ya kawo masa, beyi kasa a gwiwa ba ya fito sai kuma ya hange ta ita kadai tana kokarin fita. Murmushi kawai yay yanzu ya fahimci manufar abokin nashi. Kai tsaye gurin da take ya nufa, yana isa yasa hannunsa a kafad'arta. Gabanta ya fadi tare da tashin
Chapter 43 · 0% Book details