Sashe 54
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta da fadin.''Marakisiyya fada min ko meye."? Tace." Kullum sai bayan kin fito daga can bagaran maigidanki ita kuma nake ganin gilmawarta a gurin ban san me yake kai ta ba, ranki ya dade ya kamata ki tsawatar mata." Gabadaya yanayin ta ya sauya gabanta banda faduwa babu abunda yake kishi ya rufe mata ido tace." Wai kina nufin Hamra'u ko kuma wa."? Tace." Kwarai ranki ya dade ita nake nufi kullum da safe sai ta shiga sashen." Wani irin gumi ya fara karyo mata mussaman a saman hancinta. Tsaye ta mike ta gyara lifayar dake jikinta, hanyar fita ta nufa ranta a masifar 'bace! Aikuwa a bude ta samu sashen bayan tare suka fito dashi ya rufe har bakin mota ta raka shi sai da ta tabbatar da cewa ya fita daga Barack din sannan ta nufi gurinta , ashe munafurtar ta suke, a'ina yarinyar ta samu key din gurinsa. Ta tura dakin ta shiga ido suka had'a tana tsakiyar gadonsu da sunan tana gyarawa, ganin Gimbiyar yay bala'in gigita ta, mara gaskiya ko a ruwa gumi yake, itama ta san abunda take bata kyautawa amma ta na yin hakan ne domin ta kafa gwamnatin ta. Ta sakko daga gadon da rigar fillo a hannunta, a sanyaye tace." Aunty Ina kwana."? Ba ta amsa ba, ta nufi inda take cikin tafiyar isa da k'ama.! Ta daure ta tsaya domin bata tsammaci cewar hukuncin mari ne zai biyo bayan zuwanta gurin ba kawai taji saukarsa a kumatunta, ta zabura! ta dafe gurin da fadin." Me nayi miki zaki mare ni."? "Ubanki ki kayi min."! tafad'a jikinta na wani irin rawa!! Ta nuna kirjinta da fadin." Ubana fa ki kace."? Tace." Eh don ubanki! waye ya baki ikon shigo min turakar miji."! Ranta ya 'baci! tace." Kada ki kara zagina domin idan ki ka sake zan rama turakar mijinki kuma dama tun kafin kizo gidan nake shigowa ina gyara masa saboda haka ke baki isa ki hana ni shigowa ba." Tace." Ban isa na ha naki shigowa ba.''? kai ta gyada alamar E. Tarin belt din da suke rataye a jikin hanga ta fizgo daya, kawai ta shiga zabga mata a jiki ta ko'ina.................. Wannan shi ake kira ba zato! ba tsammani, Hamra'u da gudu ta fice daga dakin, itama ta bita da gudun tana cigaba da zabga mata blet din da fadin.'' ' Yar iskar yarinya mara kamun kai kawai ni zanyi maganin ki duk sanda na k'ara ganin kafarki a dakin nan sai nayi miki abunda yafi haka." Hamra'u na kukan bakin cikin ta isa sashensu kawai sai ta zube a kujera tana rusa ihu! kafafunta da saman wuyanta shatin belt rad'au! ya fito.. Jin kukanta yasa Uwale fitowa daga daki, hankali a tashe take tambayarta abunda yake faruwa. Kasa yi mata bayanin komai tayi ta tashi ta shige d'aki tana share ha waye.......Wayarta ta dauka ta kira shi...........Ya daure ya bar abunda ke gabansa ya daga wayar, jin alamun kuka a tare da ita ya sanya shi mamaki yace." Hamra'u menene ya faru kike kuka kiyi shuru kiyi min bayani." Da k'yar tai shuru tana sauke ajiyar zuciya ta shiga sheda masa irin cin mutuncin da matarsa tayi mata. Ransa a 'bace a kan me ta dauki belt ta zane ki, ke kina me har zaki zauna ta doke ki." Hanci ta shaka kafin tace." Kawai dan ta same ni a dakin ka ina gyarawa shikkenan tayi min wannan cin mutuncin." Yace." Kiyi hakuri wannan ba hujja bace, kuma idan na dawo gidan zanji dalilinta nayi miki wannan tozarcin! saboda haka kiyi hakuri insha Allah zanyi maganin abun." Ajiyar zuciya ta sauke da fadin."Shikkenan tunda kace haka Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameen ya Allah kafin ya kashe wayarsa." Sosai ransa ya 'baci da abunda tayi, a ganinsa ai ba wani abu bane, tunda ita ta kasa d'aukar ragamar ayyukansa to bata da hujjar da zata hana wani yayi masa hidima dole ya nuna mata kuskuranta idan bata so wata mace ta kula dashi to tayi gaggawar gyara kuskuranta. Yana ganin kiran wayarta yaki d'auka, ta kira ya kai sau goma amma bai daga ba, hankalinta ya tashi mutuka domin ta tsani ta kira waya a share ta a ganinta da gayya yayi mata hakan. Hawayen takaici ta share kafin ta kira Aunty Zeey sama-sama suka gaisa da juna, ashe kowacce da abunda yake damunta aunty Zeey din ce ta fara yi mata complain akan Madam uwargidanta sai d'ura mata ashar take tare da fadin." Ta asirce Asp din sai abunda tace yake aikatawa. Ta sauke ajiyar zuciya da fadin." Aunt Zeey ni a ganina naki mai sauki ne tunda kishiyarki ce kuma ke kika sameta a gidan, ni kuwa fa wata 'yar iskar yarinya 'yar 'kauye tana cin dunduniyata ban sani ba, ashe kullum tana tare da mijina kamar matarsa tana zuwa sashensa ta hau gadonsa da sunan gyara wannan abu ya 'bata min rai mutuka da gaske." Aunty Zeey din ta dinga kurma ashar kamar bamagujiya tace." Kici uwar shegiya! wallahi kada ki saurara musu gabadaya ki tashi hankalinsa har sai kinji abunda yake tsakaninsu." Ta ciji yatsa da fadin." Aunty Zeey ni kadai na san irin bala'in da za muyi a yau wallahi sai naji dalilin zamanta a gidan nan sannan zai sheda min dalilin da ya ha nashi daukar waya ta." Tace." Yaushe kuwa zai dauki wayarki bayan ta ki rashi ta sheda masa karya da gaskiya.........Kada ki saurara musu wallahi." Zazzafar ajiyar zuciya ta sauke cikin ranta take raya irin dambarwar da zasu buga idan ya dawo gidan. Tsaf ta shirya tayi gayu cikin wata dakkakiyar shadda dinkin sinigal aiki a ko'ina wuya hannu da kasan rigar, ta zuba gold a ko'ina hatta da yatsun k'afa babu wani cikakken kwalliya a fuskarta amma tayi wani bala'in kyau tamkar fure kowane dressing tayi yana kar'bar jikinta.........rufaffen takalmi tasa a kafafunta ta yafa mayafi irin na sarauta kai tsaye sashen nasa ta nufa tana zabga k'amshin turare fuskarta babu walwala ko ta gamin gafara. Bai dawo ba tukkuna ta samu kujera ta zauna tana cika da batsewa sa'i da lokaci tana kallon agogo wani sa'in shida na yamma a gida take masa amma yau har ta gota shiga da ashirin bai shigo ba. Ta mike kai tsaye window ta nufa, tana daga labulan motarsa na shigowa barrack din..............Ta sauke ajiyar zuciya tare da kurawa motar ido har ta isa gurin da aka tanada domin ajiye motoci. Direban shi ne ya bude masa motar kafin ya fito da wasu takardu a hannunsa, ya tsaya suna magana da direban kafin ya bashi hannu sukayi musabaha da juna. Labulan ta saki ta koma ta zauna kan kujera tana tsumayin shigowarsa. 'Kamshin turaranta ne ya daki hancinsa, ya dan lumshe idonsa kafin ya bude ya saukesu a kanta tana hakimce! 'kafa daya kan d'aya. Abunda yake 'kara rikita shi a kanta gayu da iya ado yana san irin kwalliyar da take masa.......Munanan halayenta ne kawai abun gudu. Yanayin sa ya gyara domin shi din ma bai shigo da wasa ba, ya bude baki yayi sallama cike da karsashi! da kwarin gwiwa! Ta amsa a ciki kamar ba taso. Bai saurareta ba kai tsaye bedroom d'insa ya nufa ba tare da ya kalli inda take zaune ba. Tayi 'kwafa tare da bin bayansa. Yana kokarin cire uniform din jikinsa ta shiga ta same shi, ya kalleta itama ta kalleshi dauke kansa yay yaje ya rataye kayan, toilet yake kokarin shiga maganarta ta katse shi. ." Ina so zanyi magana da kai." Ya juyo ya kalleta na second biyu kafin yace." Ina da uzuri a gabana yanzu sai an jima tukkuna." Wani malolon abu yazo ya tsaya mata a wuya! ko kafin ma tayi wani yunkuri ya shige toilet ya bar ta da b'acin rai! Koda ya fito bai kalli inda take ba ya fara hidimar shirya jikinsa, yana jin ciwon yanda ta bar shi sasakai komai shi yake wa kansa. Ta iske inda yake cikin bala'i! da neman fitina! tace." Kasan abunda ya faru shiyasa kake wani dauke kai saboda rashin gaskiya, to da kai da yarinyar duk zanyi maganinku dan bana shiri da munafiki." Ya kalleta da bacin ran maganarta yace." Eh na san irin rashin mutuncin da ki kayi wa 'yar mutune me ta tsare miki daga gyara kayan ki zaki dauki blet ki doke ta, meye hujjarki ta aikata hakan"? Tana numfarfashi! tace." Saboda ta shigo min turakar miji shiyasa nai mata wannan hukuncin kuma wallahi ko yau ta sake shigowa dakin nan sai naci ubanta."!! Ya ja mata tsaki! tare da kokarin ratse ta ya bar gurin......Tare shi tayi har jikinsu na had'uwa......Murya na rawa tace." Wallahi ba zan yarda da wannan munafurcin ba sai ka fada min tsakaninka da ita domin tun baya yau ba na fahimci akwai wata alaka a tsakaninku." Ya jima yana kallonta da tsananin 'bacin rai a tare dashi yace." Kin ga *ZINA* bana bukatar 'bacin rai a yanzu kada kiyi sanadin da zai janyo mana samun matsala, tsakanina da Hamra'u idan lokaci yayi zaki sani." Tace." Bana jin tsoro ko shakkar 'bacin ranka munafurci ne bana so kawai ka fad'a min abinda yake tsakaninka da ita idan babu wata alaka to wallahi sai ta tattara kayanta ta bar gidan nan domin zamanta bashi da amfani." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Ke baki isa kisa Hamra'u ta fita a gidan ban ba, domin tun kafin ki zo muke zaune da ita, alakar dake tsakanina da ita kuma lokaci ne zai nuna miki."! Ta fashe! da kuka tana dukan kirjinsa da fadin.'' Wallahi na fad'a maka sai dai ka za'ba koni ko ita domin ina zargin wani abu, wallahi kaji na rantse da Allah ba zan hada kishi da ita ba." Tana kuka sosai take maganar tana kuma cigaba da dukan kirjinsa! Gabad'aya jikinsa ya mutu ya dinga kokarin rik'e hannuwanta ta fuzge da karfi! ta kama hanya da sauri ta fice daga dakin tana share hawaye........Gefan gado ya zube tare da dafe kanshi.......Hohoho!! *ZINATU PROBLEM!! *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar