← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 97

Sashe 15

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaza kaiwa! Ganin haka yasa ya kar'bi maganin daga hannunta ya lakato kan yatsansa, ya kalleta da fadin." Kin bani izini."? Shuru tai masa. Ya sassauta murya yayi da sake maimaita maganarsa. Kai kawai ta iya daga wa gabadaya jikinta ya mutu! ya lalubi gurin yana shafa maganin a hankali yana sake kwantar mata da hankali da cewa gurin zai daina ciwo insha Allah! Ido kawai ta lumshe tana jin maganganunsa sama-sama a cikin kunnanta, har ya gama shafa maganin fuskarta ya dan kalla sai yayi sauri ya janye idonsa jin yanayinsa na neman sauyawa, gefe ya matsa tare da sassauta murya ya kirayi sunanta............ *GIMBIYA!* a kasalance ta bude idonta! tana kallonshi , tana masifar son taji ya kira ta da wannan sunan. yace."Sannu ki kwanta ki huta na shafa miki maganin." Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta zame ta kwanta tana tattakure guri daya, Shima ajiyar zuciya ya sauke kafin ya lalubi wani zani mai kauri ta fara k'okarin rufa mata a jiki akayi rashin sa'a gwiwarsa ta zame ya fad'i kanta! fuskarsu ta hadu! da sauri yayi gaggawar rabuwa da jikinta yana bata hakuri! uffan ba tace ba asalima lokacin da hakan ya faru idonta a rufe yake. Ganin tayi shuru ba tace masa komai ba yasa a gaggauce ya fita yana auziyya a zuciyarsa, be san me yasa ba kullum zuciyarsa take kwadaita masa wasu gurare na jikinta, a duk sanda zasu kasance a guri daya yakan rasa nutsuwarsa. Itama anata bangaran hakane, har yanxu idonta a rufe yake ta rasa abinda yake mata dadi! yanda yake sassauta murya yana rarrashinta yakan karya mata garkuwar jiki, tana jin dadin hakan sosai, a rayuwarta tana masifar son namiji wanda ya iya soyayya, bayan haka kuma bata san lusarin namiji tafi son tsayayye shiyasa wasu lokatan yake birgeta domin dik ya tara abubuwan da take bukata. Ajiyar zuciya ta sauke tare da jan zanin daya rufa mata ta rufe gabadaya jikinta harda fuskarta, addua take a zuciyarta Allah ya sa bacci ya dauketa. Cikin ikon Allah kuwa bacci mai nauyi ya dauketa................ Kamar a mafarki! ta dinga jin ihu!!! da hayaniya tare da kukan karnika! da karar wu'ka'ke! a firgice ta tashi tsaye! tana bin gurin da kallo, babu kowa duk sun fice! yanda 'kura! da guguwa! take shigowa har gurin da take shi tabbatar mata da cewa babu lafiya! Fitowarta daga gurin yayi daidai da tashin bomb! gabadaya gurin ya kacame! ya hargitse! da hayaki! da rarrafe ta koma katangaggen gurin ta takure guri daya tana kiran sunan Allah. Ta jima a haka kafin ta dago kanta, still tana jiyo hayaniya da kuwwa! tare da kukan karnika! ga wani irin b'akin hayak'i! da ya turnuke! a gurin! Hannu tasa ta toshe hancinta tare da sake takurewa a guri daya jikinta in banda rawa babu abunda yake, bakinta sai motsi yake adduar yaye masifa takeso tayi amma bata iya ba, sai kawai ta dingi nanata innalillahi da karfin gaske! Hakan ya janyo hankali d'aya d'aga cikin yaran *uban daba* wanda yake shawagi a gurin...........Gurin ya shiga yana zazzare ido! ita kuma ganin b'akuwar fuska yasa ta sake rikicewa! shi kuwa murmushin farin ciki yayi ya nufeta da saurin gaske! Hannunta ya fizgo! ta turje! tana rirrike itaccen dake katange da gurin, kuka take tana rokonsa yayi hakuri, ya d'auke fuskarta da mari! da tafkeken hannunsa!! a take hancin ya fashe! ya dinga tsiyayar da jini! nta yake tana turjewa da bashi hakuri cewa bata da laifi itama sato ta sukayi, ya sanya kan k'otar lafceciyar wu'kar dake hannunsa ya dinga bubbuga mata a gwiwa, lokaci guda ta galabaita! ta zube a gurin! d'aukarta yayi ya sa'ba a kafad'a ya fito da ita. kai tsaye mafarkarsu ya nufa da ita a kafad'arsa............. Tashin hankali kenan! lokacin daya hangeta sa'be a kafardar gardi! sai da wukar hannunsa ta subce! ta kusa fad'uwa amma yayi muzzakaracin riketa da kyau a hannunsa!! Wani uban ihu! ya kurma! wanda ya razana! abokan fad'an nasa suka ranta ana kare, amma ina! basu samu nasara ba, sai da ya kama su, ya sanya wata narkekiyar igiya ya daure musu hannuwa da kafafu! Gabad'aya gurin ya hargitse! sakamakon bomb din da ya tashi, yayi sanadiyar kona biyu daga cikin yaran shi, suna kwance magashiyan! rai a hannun Allah...... Duk da cewa sune suka samu nasara amma beso wata matsala ta afku da yaran sa ba.. Ya kallesu gabad'aya kammaninsu ya sauya hatta da fuskokinsu sun rine! da baki! sakamakon tashin bomb din, wannan ce hanya mafi sauki da abokin hamayyar ya samu nasara a kansa! Ya kallesu da fadin." Yayi imani! da cewa idan ya tunkari inda muke da wu'ka ko wani abu makamancin haka ba zai samu nasara akanmu ba, wannan shine dalilin daya sanya shi jefo mana bomb! ba tare da munyi tsammanin hakan ba, to Alhamdullhi duk da hakan be samu nasarar da yake bukata akanmu ba, yanzu kalubalan dake gabanmu tunkarar sansaninsa domin gwabzawa a tsakanimu, babu yanda za'ayi mu tafi mu bar masa wannan yarinyar da yayi nasarar dauke mana ita, duk da cewa tsintar ta mukayi akan hanya bamu san daga ina take ba, hakan ba zai sanya mu bar masa ita ba, duk yanda za'ayi sai mun samu nasara a kansa." Da yawa daga cikinsu sun tausaya mata, amma wasu sun kalubalanci maganarsa! bai ta'ba sanya kara sun tsallake ba, amma da alama akwai wa'inda za suyi masa tawaye a cikinsu. Ya dinga kallonsu yana nazarin yanayinsu, yace." Babu wanda zan tursasa! cewa ya take min baya! a cikunku. zan iya tunkarar sansanin ni kadai! ba tare da kowa ba! saboda haka wanda yake ganin zai bi bayana bisimillah." Yana gama maganarsa sai yayi gaba, wasu suka bi bayan shi da sauran karnukan! dake raye, wasu kuma suka tsaya suna surutai da mai da magana a tsakaninsu! *Free pege ya kusa karewa a daure a biya kudin karatu don Allah idan kin san ba siyan littafin nan zaki ba kada ki dauki number ta kiyi min magana* *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari. katin airtal ko mov. 1/21/22, 12:28 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ FREE PEGE *23&24* *Biyu da rabi na sulusin dare!* Cikin firgitaccan yanayi ta tashi zaune tana kiran sunan Allah! hakan ya janyo farkawarsa dama can bashi da nauyin bacci, zaune ya tashi kafin ya rike hannunta dake wani irin rawa, yace."Menene Aysha."? Sai kawai ta fashe da wani irin kuka ta rungumeshi tana girgiza kai da fadin." Zinat ce ranka ya dade yarinyar nan na cikin mugun yanayi Allah ya nunan hakan a mafarkina." Sake rungumeta yayi a jikinsa cikin sigar rarrashi yace."Aysha mafarki ba gaskiya bane kada ki gazgata abinda ki ka gani, bana tsammanin cewa mafarkinki zai tabbata, jikina yafi bani cewa yarinyar nan tana a raye kuma daf take da ta dawo garemu da ikon Allah." Kallonshi tayi hawaye na tsere a saman fuskarta tace.''Ranka ya dade koda Allah ya nufa yarinyar nan ta dawo gida bai zama lallai a sameta da cikakkiyar lafiya ba ka san dai yanda duniyar nan ta lalace da rashin gaskiya wannan shine babban tashin hankalina." Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kada ki fadi haka Aysha! zuciyarki ta dinga halarto miki alkairi akan yarinyar nan! adduarki a gareta karbabbiya ce a gurin Allah, kada ki yarda zuciyarki ta yarda da wannan mafarki ki dauka cewa k'anzon kurege ne, a yanzu abinda zakiyi ki faranta min shine ki tashi kije ki dauro alwala ki gabatar da nafila a gaban ubangiji kana ki mika masa kukanki." Ta sauke ajiyar zuciya da jin sassauci acikin zuciyarta, a hankali ta zame jikinta daga nasa ta sauka daga gadon ta nufi toilet domin daura alwala. Tana fitowa shima ya tashi ya shiga ya daura alwalar ya fito, lokacin har ta tayar da sallar, jallabiya da gajeran wando ya sanja kana ya gyara dadduma shima ya tayar da tashi sallar. ****** Tun bayan daya sa'ba ta a kafad'a suke buga artabu a tsakanisu, rikon tsauri! yayi mata yana gudu tare da tsallake manya-manyan dutsina da ita a kafadarsa! tayi duk wani kokari gurin ganin ta ceci kanta abun yaci tura! domin mutumin mugun basamude! ne wanda cizo da yakushi basa shigarsa! dukansa take tana cizo duk ta dauke masa fata amma ko ajikinsa, ya riketa katamau! yana gudu! burinsa kawai ya kaita gaban ogansa ya san hakan zai faranta masa rai. Hakan ne ya kasance kuwa, Ogan nasu yana cikin bacin rai! mai tsanani sakamakon rashin samun nasara! bai ta'ba fuskantar irin hakan ba sai a wannan lokacin, kai kawo kawai yake gurin ya rasa abinda yake masa dadi! ............Amma zuwan babban yaron sa da yarinyar ya faranta masa rai! mutuka, sai kawai ya kwashe da wata 'yar iskar dariya kafin yayi wani irin tsalle! da juyi na jin dadi, ya zuba mata kwala-kwalan idanuwansa! Bakinsa kawai yake lasa, jikinsa na wani irin tsuma! komai na yarinyar yayi cif da cif! bata da makusa, cikakkiyar mace irin wacce ya jima bai kwanta da irinta ba! Gurin ya tsit! gabad'aya yaransa sun zagayeta motsin kirki ta kasa, kanta ne ma yake juyawa a gurin, dishi-dishi! take kallonsa har ya karaso inda take zube! Ya tsugana kusa da ita, sai tayi saurin janye jikinta, ya sha kunu; tare da matsawa jikinta, ta sake janyewa tana watsa masa mugun kallo! Mahaukaciyar dariya yayi! ya cigaba da lasar lebansa, yana bin sassan jikinta da wani irin kallo na tsantsar sha'awa! Hannu ya kai jikinta, a zabure! ta fitar da hannu ta bashi kyakykyawan mari a fuskarsa! ko gezau! beyi ba sai dai yaransa da suka zabura! sukayi kanta! Ya daga musu hannu da basu umarnin matsawa baya. Suka matsa can nesa suka bar shi da ita, zaman dirshan yayi a gabanta ya mika mata tafkekiyar fuskarsa dake cike da kasumba! yace. " Idan hakan yana miki dadi ki sake aikatawa." Ya fada yana sake tura mata fuskar. Tsaki mai tsayi taja! ta matsa nesa dashi! ya rarrafa kan gwiwarsa ya cimma inda take! kafafunta dake daure da takalmi ya tsirawa ido, babu abunda yafi tafiya dashi irin shara'ban
Chapter 15 · 0% Book details