Sashe 37
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai dace ba, kada kiyi mamakin cewa ina can wani gari amma labarin halin da kike ciki zai sameni har lokacin dawowata gida, ki goge number duk wanda kika san cewa ba muharramin ki bane kafin na dawo, sannan ban yarda kije ko'ina ba, akwai securities da zasu sheda min shigarki da kuma fitarki. idan kina da wata Matsala kina iya shedawa Asp domin dashi kadai na yarda bayan shi ban yarda wata magana ta shiga tsakaninki da ma'aikatan gidan nan ba, wannan shine abunda nake so ki rike a ranki kuma kiyi aiki da umarni na." Wani bacin rai ne ya tsaya mata a wuya jin yanda yake mata magana cikin isa da gadara kamar wani ubanta, koda yake tunda aka daura auran iyaye da kakanni ke mata nasiha cewa tabi mijinta sau da kafa domin tunda ta riga ta bar hannun iyayenta to basu da hakki mai karfi a kanta kamar yanda mijinta yake da hakki a kanta, dole ne ta bishi ta kuma bi umarninsa, yi nayi bari na bari wannan sune irin nasihohin da aka dinga yi mata kafin kawo ta dakin mijin nata shi kansa Maimartaba fada yay mata sosai akan biyayyar aure...............Ita kuma sai take ganin kamar wannan shine dalilin da yasa su mazan suke nuna izzah! da gadara! akan matayensu saboda wannan damar da Allah ya basu, gashi dai ita ko kwana daya ba tayi ba a gidan ya fara kafa mata sharud'ai bayan ma baya garin amma yana nuna mata isa da mulki saboda kawai yana wasu tunane- tunane marasa kyau a kanta, Ajiyar zuciya ta sauke tare da kokarin danne bacin ranta tace." To i dan ka gama maganar ka zan kashe wayata.'' Ashe maganar banza take domin tuntuni ya kashe wayarsa ya bar ta da tata a kunne sai kace shashasha. Cire wayar daga kunnanta yayi dai-dai da zubar hawaye da take kokarin dannewa. Ta jefar da wayar saman gado ta dafe kanta da duk hannuwa biyun kukan takaici ne ya kufce mata! Hakika an kassara mata rayuwa tunda har aka had'ata aure da bagidajen namiji wanda bai iya lallashi da lallami mace ba, kullum bakar magana ce take shiga tsakaninsu, ya za'ayi ta iya zaman aure dashi a haka, burin ta a rayuwa ta auri namijin da ya iya soyayya da kula da mace sai gashi ta b'ige da auran bahagon mutum wanda ya rako maza duniya. Ta jima tana share hawayen takaici kafin ta cire kayan jikinta ta nufi bandaki domin watsa ruwa a jikinta. Lokacin da ta fito yayi dai-dai da shigowar Uwale dakin, suna hada ido sai tayi saurin kawar da kanta tana ya mutse fuskarta, kai tsaye dressing mirror ta nufa. Uwale jikinta yay sanyi domin ta lura da irin kallon banzan da tayi mata. Ta nuna kamar ba ta gani ba da 'yar fara'a tace."Sannu yarinyar arziki dama na shigo ne na dubaki sannan na tambayeki ko da akwai abunda ki ke bukata, ga dai abinci can a falo ajiye miki." Uwale tafi minti biyar da gama maganar amma ko kallonta ba tayi ba ballantana ta samu damar bata amsa, sai kawai ta juya jikinta a sanyaye ta bude dakin ta fita tana mamakin rashin tarbiyar yarinyar. Tana fita taja tsaki ta cigaba da shafa mai a fatar jikinta daga shi har kakar tasa haushinsu takeji. A sanyaye ta zauna kan kujera jikinta duk babu karsashi. Hamra'u ta kalleta da fadin." Uwale ya naga kin dawo da jiki a sa'bule."? 'Yar dariya tayi da fadin." Aa ba wani abu ne ai Gimbiyar tayi bacci lokacin dana shiga gurin nata." Cikin rashin so ta bayyana mata abunda ya faru ta k'arasa maganar. Tai 'yar dariya da fadin." Uwale kenan, jikina na bani akwai wani abu da ya faru amma tunda kina boye min shikkenan." Da sauri tace." Ke 'yar nan me zai faru kuma idan ba alkairi ba? ni babu wani abu da yarinyar nan tayi min koda na shiga na sameta tana bacci sai kawai na fito nace idan Allah ya kaimu da safe sai mu gaisa da juna kawai kuma sai ki zargi wani abu." Yanda take magana da son kare Gimbiyar sai ranta ya baci kishi yasa ta ta'be baki tare da mikewa da fadin." Ni zan shiga na kwanta sai da safe." Ta bita da kallon nazari kafin tace."Allah ya tashemu lafiya." Da sauri ta bar gurin ranta a masifar b'ace, Ta rasa gane mai yake damun Uwale, tunda Gimbiyar ta sauka a gidan ta rasa nutsuwarta sai kai kawo take tsakanin kicin da falo da kanta ta shirya mata abinci mai dadi irin na tsofaffin hannu, duk tana zaune tana kallonta tana rawar jiki ta dauki abincin domin ta kai mata, sai gashi kuma ta dawo da jiki a sab'ule, tabbas wani abun ne ya faru amma wai sai take 'boyewa mata kome menene dalilin hakan oho! ita kam tayi alkawari cewa ba 'yar sarauta ba ko wacece ita wallahi tayi rantsuwa cewar ba zata bauta mata ba, tunda dai ba zaman ta take a gidan ba, itama Uwalen itace ta d'orawa kanta wahala amma ita kam duk rintsi ba zata yarda ayi haka da ita ba. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/4/22, 19:16 - Buhainat: *55&56* Kayan bacci masu taushi ta sanya a jikinta, babu wani kuzarin kirki a tattare da ita, ta kwanta kan gado tare da jan bargo ta rufe jikinta. Ido ta rintse bacci kawai ta keso tayi ko ta samu saukin 'bacin ran da ya addabeta a zuciyarta, amma duk yanda taso ta gayyaci baccin yaki zuwa, idonta tar mazai! har yanzu tana tunanin kausasan kalamansa a kanta, a mafarki bata ta'ba tunanin cewa za tayi irin wannan auran ba, duba da yanda ta dinga katantanwa da tarin maza masu mulki da mukamai daban-daban wanda suka mace a soyayyarta. Tabbas maganar Sakina gaskiya ne in da take cewa a lokacin da kake dama ya kamata ka dama, idan ba haka ba, to wanki hula zai kai ka ga dare, yanzu wa gari ya waya gashinan ta 'bige da auran namijin da bata ra'ayinsa...........Idonta a lumshe take wannan tunanin tana kuma hasaso fuskar b'oyayyan masoyinta wanda take jin bala'in sonsa a cikin zuciyarta saboda soyyarsa da kuma iya kalamansa, shi kad'ai ne a yanxu zai kawar mata da b'acin ran dake damunta, amma kuma haka kawai a zuciyarta take jin tsoron kiran wayarsa. zazzafar ajiyar zuciya ta sauke ta dan gyara kwanciya tana takure jikinta guri guda kamar me jin sanyi koda yake hakan nan ta tsinci kanta cikin wannan halin duk sanda za ta kwanta bacci ta dinga juye-juye kenan kafin baccin ya dauketa sai an ja dogon lokaci tukkuna, daga nan kuma sai ta dingi mafarkai barkatai! masu kyau da marasa kyau har sai garin Allah ya waye tukkuna, za ta tashi cikin tsananin sha'awa domin duk yawanci mafarkan akan sex ta keyi alhalin sam bata kwanciya da abun a ranta, wannan dalilin yasa tayi alkawarin cewa duk magungunan matan da Aunty's dinta sukayi mata guzurinsa ba zata sha ko daya ba domin ta riga ta d'ora zarginta kan cewa duk magungunan data dubga dalili, saboda da can ba haka take ba, duk yawan shekarunta bata ta'ba mafarkin wani da namiji ba sai gashi kullum idan ta kwanta sai tayi mafarki gata dumu-dumu da namiji suna sex yana biya mata bukata. Bargon dake rufe a jikinta ta sake gyarawa kafin k'ira ya shigo wayarta dake saman bedside, cike da mamaki ta dauki wayar tana dubawa ashe bata kashe ba ta kwanta. Sunan 'boyayyan masoyi ne yake yawo kan fuskar wayar. Gabanta ya dinga faduwa ta shiga nazari da tunani akan ta daga wayarsa ko kada ta daga..........*"Ki goge duk number wanda ki kasan ba muharramin ki bane kafin na dawo, kada kiyi mamakin cewa duk halin da kike ciki zan samu labari saboda haka ki kiyaye kuma kibi umarnina."* Manganganunsa suka fad'o mata a rai, ta tsirawa fuskar wayar do tana kallo har ta katse. Ya sake kira still dai bata daga ba, sai bin dakin take da kallo tana tunanin ko da akwai wata na'ura da ya daura a dakin domin ganin duk motsinta..............haka kawai take jin tsoron ya kamata da wani laifi mussaman irin wannan ba wai don tana tsoronsa ba, yanda ta lura dashi kamar shima yana zargin ta irin yanda wasu daga cikin jama'ar gari suke mata abunda ta tsana kenan a zarge ta akan fasikanci, wannan shine dalilin da yasa take jin tsoron daga wayar boyayyan masoyin nata.......Sai kawai ta yanke shawarar shiga whasp ta duba ko ya ajiye mata sako. WhatsApp ya shiga domin har yanzu ya kasa yarda da abinda zuciyarsa take raya masa a kan yarinyar zai cigaba da gwadata har sai ya fahimci in da ta dosa. Yaji dadin ganinta a online sai ya tura mata sako kamar haka. _My love me yasa baki daga waya ta ba."_? Ta bashi amsa kamar haka" _Ai ba muyi da kai cewa zaka dinga kiran waya ta ba, idan hakan ma ta kama cewa nayi ka bari ni zan kira ka, to mai zai sanya ka kira ni a irin wannan lokacin."_ Yace." _My love menene a ciki don na kira ki na debe miki kewa, na san da cewa angon naki baya gari shiyasa nake so na debe miki kewarsa._ Emoji ta tura masa na mamakin maganarsa. Yace." _Kin san irin son da nake miki ne yasa nake bin diddigin duk abinda ya shafe ki mijin baya gari yana gurin training ko ba haka bane."?_ Murmushi takaici tayi kafin ta tura masa da amsa. _"Eh hakane maganar ka amma nayi mamakin yanda akayi ka san haka."_ Yace." _Kada kiyi mamaki da sanina halin da kike ciki, ko kin manta nima d'an cikin garin katsina ne, ai shiyasa ban cire tsammanin had'uwa dake a kurkusa ba tunda muna cikin gari daya._ Amsa ta bashi kamar haka.. _"Faruk ina sonka sosai irin wanda ban ta'ba yiwa wani namiji ba, hakika zan so na ganka a zahiri sai dai wannan mijin nawa yana da zafi! kuma ma'aikacin tsaro ne ina jin