← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 97

Sashe 29

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsammanci kiran nata ba harkokin gabansa kawai yake, ya manta da ita da lamarinta, shirye-shiryen tafiyarsa training yake, sai dai be manta da adadin kwanakin da suka rage a d'aura auran ba. A daran ranar da zai tafi suke tattauna maganar da Asp yace." UMARU tafiyarka training ba zata hana faruwar komai ba, meye amfanin abotarmu ni zan tsaya maka akan komai kuma zan wakilce ka, sannan kuma ni ne zan bada sadaki domin a gabatar da komai anyi hakan ba daya ba kuma sau biyu rashin hallatarka d'aurin auran ba zai hana ace aure be d'auru ba, saboda haka ka kwantar da hankalinsa insha Allah sai dai kawai ka dawo ka samu amaryarka na jiranka." Cikin zolaya ya 'kare maganar. Murmushi yayi tare da sauke ajiyar zuciya Yace." Nagode sosai mutumina Allah ya saka da alkairi ya kuma bar abota da amana." Ya amsa da ''Ameen ya Allah amma yana da kyau kafin ka tafi ka shedawa mahaifin yarinyar halin da ake ciki koda ta waya ne." Yace."Eh dama ina da tunanin hakan, a daran nan zan kira shi mu tattauna maganar." Ya bashi hannu da fadin."Hakan yayi Allah yasa ayi sa'a." Ya amsa da ameen ya Allah abokina. To koda ya shedawa Maimartaba Omar halin da ake ciki sai shima ya nuna masa cewa hakan ba wani abu bane, kamar yanda Asp din ya tabbatar masa da cewa ana yin hakan ba matsala bace mutukar akwai wakilinsa shikkenan magana takare, ya kuma karfafa masa gwiwa tare dayi masa kyawawan adduo'i. Cikin mutunci da karamci sukayi sallama da juna...........Mutunci da dattakon dattijon yana mutukar burgeshi wannan dalilin ne kadai yasa har ya amince da auran yarinyar, tabbas da babu wannan bega dalilin da zai sashi auran mace mara nutsuwa da tarbiya irinta ba. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 1/31/22, 07:31 - Buhainat: *43&44* *GSR* A daran ranar dai zai yi tafin ya samu Uwale da maganar domin su tattauna, ya sheda mata duk abunda yake faruwa ya kuma tabbatar mata da cewa halin da ake ciki a yanzu saura sati biyu kacal a daura auran, saboda haka ta shedawa duk wanda ya dace acikin 'yan uwa da abokan arziki.........Sosai tayi farin ciki da al'amarin dama shi aure lokaci ne gashi lokacin da ba suyi tsammani ba Allah ya nufa , sai dai kuma bata bar shi ya tashi ba sai da tayi masa maganar Hamra'u da yanda za'ayi da al'amarinta. Yace."Uwale Hamra'u itace za'bi na kuma har yanzu ina sonta, aure na da wannan yarinyar ba zai hana na aureta ba, wannan auran yazo min bagatatan cikin rashin shiri, insha Allahu itama zan aure ta idan na samu nutsuwar da nake bukata. Ta kalleshi da fadin." UMARU idan fa baka auri yarinyar nan ba ka yaudareta sai Allah yayi mata sakayya domin dai kai kanka kasan tuntuni kai take jira kuma da bakinka kayi mata alkawarin aure kasan dole idan ta samu wannan labarin ta shiga damuwa tare da iyayenta don Allah kada ka bani kunya UMARU kada ka raba zumuncin da yake tsakanina da mahaifin yarinyar nan." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Uwale kin san fa komai nufi ne na Allah, mutum kan iya tsara rayuwarsa amma Allah sai ya sauya masa, mahaifin yarinyar nan yafi karfin komai a gurina dalilin kenan da yasa na karbi kyautar da yayi min, na kuma fada miki cewa hakan ba yana nufin na janye auran Hamra'u ba, zan aure ta da yardar Allah saboda haka ki kwantar da hankalinki itama yarinyar ki taushi zuciyarta." Tace."To shikkenan UMARU Allah ya tabbatar da alkairi amma kafin ka tafi ka samu yarinyar ka sheda mata abunda yake faruwa kamar yanda kayi min bayani." Agogon dake hannunsa ya duba, sha d'aya shaura na dare, yace." Ban 'ki maganarki ba, zan sameta mu tattauna maganar ko ba yanzu ba tunda yanzu dai dare yayi watakila tayi bacci." Tace." To shikkenan Allah ya kai ka lafiya ya kuma dawo da kai lafiya." Ya amsa da "Ameen ya Allah." Sallama yayi mata ya nufi wajensa. Da Asubah bayan sun fito daga massalaci suka tsaya suna sake tattauna maganar, Asp din yace."Naga tunda aka fara maganar auran nan ba kayi maganar lefe da sauran abubuwan bukata ba, kasan yarinyar nan fa 'yar rigima ce yana da kyau a rarrasheta ta wannan hanyoyin. Yace."Asp ban san me yasa kake jin tsoro da shakkar yarinyar nan ba, mahaifinta fa kyauta ya bani ita sadaki kawai zan bayar to akan me zan takurawa kaina saboda ina gudan rashin kunyarta." 'Yar dariya yay da fadin." UMARU har yanzu ba'ayi macan da zata tsorata ni ba, kawai dai ina nuna maka yanda za'ayi ka zauna da ita lafiya ne idan kana mata butsu to ba zaku ta'ba samun zaman lafiya da juna ba, maganar lefe kuma abunda ya dace ne koda kyauta aka baka kai kuma sai ka duba cancanta da abunda ya dace." Yace." A yanzu dai bani da kudin had'a mata lefe sai dai idan tazo daga baya nayi mata." Asp din ya dinga kallonsa yana mamakin furuncinsa, wai bashi da kudi bayan irin tarin miliyoyin da yake dasu account ko sati biyu ba'ayi ba daga can abuja mai girma shugaban kasa yayi masa kyautar manyan kudi da dan'kareriyar mota harda gida a garin abujan amma shine yake maganar rashin kudi. Girgiza kansa kawai yayi da fadin." UMARU wato abunda dai kayi ra'ayi shi kake ba'a baka shawara ka d'auka to ai shikkenan." Yanda Asp din yayi maganar da b'acin rai a tare dashi yasa jikinsa sanyi ya bashi hakuri da fadin." Afuwa abokina ba wai naki daukar shawararka bane akwai dalilina na yin hakan, amma na janye domin farin cikin ka, yanzu nawa zan bayar ayi lefen tunda kaga ni yau zan bar gari sannan kuma ban ma san yanda ake hada lefen ba. Yace."Ai magana ta wuce ko sisin ka bazan kar'ba ba, lefe kuma ba za'a fasa ba, zan bawa madam kudi ta shiga kasuwa ta had'a duk abunda ake bukata." Yana gama maganar yayi tafiyarsa. Murmushi kawai yake yana binshi da kallo har ya k'urewa ganinsa, tunda Allah ya had'asu yake nuna masa 'kauna da sadaukarwa Asp ya zame masa dan uwa na jini, yanda yake sonsa da kaunarsa shima haka yake kaunarsa saboda duk wasu alkairai yayi masa kuma duk wani mataki da yake kai yanzu dalilinsa ne da jajurewarsa, hakika bashi da wani abu da zai saka masa dashi face addua. ***** To kamar yanda Asp din yayi wa kansa alk'awari sai da cika, don kudi masu yawa ya fitar aka had'a lefe dasu akwatina goma sha biyu cike da kaya set din gold har uku kuma duk masu nauyi, da yake da akwai fahimta a tsakaninsa da matansa babu wacce ta daga hankalinta, sai dai kuma sa'bani ya kusa giftawa a tsakaninsa da yarinyar da zai aura a matsayin ta uku , al'amarin ya dinga bashi mamaki yana tunanin a inda ta samu labarin Zinatu da har take kishi a kanta, ganin yanda ta tashi hankalinta ne yasa ya zauna yayi mata bayani cewa yarinyar da abokinsa zai aura ce, dalilin da yasa ya tsaya akan al'amarin shi abokin nasa baya gari yayi tafiya shiyasa ya tsaya masa akan al'amarin auransa." Wannan bayanin da yayi mata yasa ta kwantar da hankali amma da tayi tunanin ko yaudararta zaiyi. Tun ranar da aka kai wa Uwale kayan lefen domin tasa albarka, Hamra'u ta shiga tashin hankali mai tsananin gaske, domin kasa zaman falon tayi ta shiga daki ta rufe kofa ta dinga rafsa ihu! bakin ciki da bakin kishi kamar ya kasheta. Uwale ta shiga dakin ta sameta cikin mummunan yanayi, ta zauna tana rarrashinta gabadaya itama zuciyarta ta karye da al'amarin anya kuwa UMARU ba yaudararsu yake ba? a tunaninsu duk shine ya fitar da kudi masu nauyi aka had'a lefan, al'amarin dai duka bai musu dadi ba, ace ayi ta abu d'aya sai kace cin k'wan makauniya. Tana kuka tace."Ashe Uwale har dake za'a had'a baki a tozarta ni! me nayi miki kika tsanani har ki ka bada goyon bayan auro wata bayan gani, kin san kuma tsayin shekarun dana dauka ina jiransa, me yasa zaku ci amanata." Hawayen tausayinta ta share kafin tace." Hamra'u ashe duk abunda yake faruwa UMARU be fada miki ba.? Ta girgiza kai da fadin." Ni be fada min komai ba kuma kema ai be kamata ki 'boye min ba, yana da kyau duk abunda yake faruwa ki sanar dani nasan matsayina." Tace."Hamra'u kada ki zarge ni ko kuma kiga laifina akan wannan al'amari, wallahi ni kaina ban san da maganar ba sai ana i gobe zai yi tafiyar nan yake sheda min halin da ake ciki, kuma ya tabbatar min da cewa wannan auran da zaiyi ba zai hana ya aureki ba, al'amarin ne yazo a k'urace shiyasa kuma kinga mahaifin yarinyar nan babban mutum ne wannan shine dalilin da yasa beyi jayayya dashi ba, a yanda na fahimtashi shima Auran zeyi shine saboda ganin mutuncin mahaifin yarinyar saboda haka ki kwantar da hankali UMARU ya tabbatar min da cewa kece za'bin sa kuma zai aureki da ikon Allah." Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sassauci a cikin zuciyarta, idan ta fahimci maganganun Uwale suna nuna mata cewar zai yarinyar ne saboda mahaifinta, ba wai dan yana sonta ba, wannan dalilin shi kad'ai sanya zuciyarta yin sanyi, amma dai duk da hakan ba zata hakura ba sai ta sake jin matsayinta a gurinsa. ****** Tsakanin Madam da Aunty Zeey amaryarta basa shiri sosai fad'a suke da juna, dalilin da yasa ma kenan basa iya haduwa guri daya domin mutukar suka hadu to sai sa'ba ni ya gifta a tsakaninsu, kuma ba kowa ke janyo rikicin ba sai Aunt Zeey maca ce mai bala'in kishi da ganin ido, ta tsani Madam da 'ya'yanta don dai ita ma Madam din a tsaye take shiyasa take shakkarta amma dai duk da haka idan sa'bani ya gifta a tsakaninsu sai sun buga, duk da ita Madam din tana kokarin ganin ta kama girma da mutuncinta. To wannan dalilin yasa Asp din be gayyaci
Chapter 29 · 0% Book details