← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 97

Sashe 10

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta amsa da "ameen" tana kokarin tashi, Rakiya tayi sallama, gabadaya suka amsa, Uwale tayi saurin fadin." Yanzu nake maganarki a cikin raina nace har gida zanje na kai miki kudinki." Tace."To ai baki fada min nawa kika sayi atampopin ba." Ta ya mutse fuska da fadin." Gabadaya dubu uku na saya domin dai kema kin san atampopin naki an daina yayin irinsu bayan hakan haka kuma sun jima a ajiye sai warin ajiya suke." Rakiya ta mika hannu da fadin." Ban siyar a hakaba bani na kai inda za'a saya da mutunci." Baki ta bude da fadin." Rakiya ina zaki kai a siya da mutunci bayan nan, kin san dai idan kika kaiwa Delu siyan banza za tayi miki gwara ki tsaya mu sassanta." Taja tsaki da fadin." Ai har gwara Delu a kanki Uwale sai kace kayan sata zaki saya dubu uku duk daya a kasuwa dubu biyu da dari biyar ce, idan sayan mutunci zakiyi ina laifi ki saya dubu biyar gabadaya." Tace." Oh!oh zan dai saya dubu hudu idan kin sallama min a haka." Jim tayi kafin tace."Na siyar miki amma kada ki tsinka min kudi ki bani kudiba cif." Tace."Maganar kike so Rakiya ai a inda ba kasa anan ake gardamar kokawa da ban shirya ba ai ba zan karbi kayanki ba." Rigar jikinta ta daga ta zuge zif din lalitar dake daure a jikinta kudi ta fito dasu, a dukunkune yawanci duk 'yan dari biyu ne, duk sun ya mutse, Hamra'u tasa hannu suka lissafa dubu hudu kudin me kayan ta mika mata da fadin." Gashi maganin karya hallara ki lissafa a gabana na san halinki kada ki dawo kice min basu cika ba." Rakiya ta dangwali yawun bakinta ta fara lissafa kudin ta kalleta da fadin "Sun cika." Tace."To masha Allah idan an samu wasu kayan ina bukata." Tana kokarin fita tace." To shikkenan idan an samu zaki jini." Bayan fitar Rakiya daga gidan itama Uwale kayan dillancinta ta dauka ta fita, ya rage saura ita kadai a gidan, ta jima tana sakawa da kwancewa kafin ta tashi cikin sanyi jiki ta gyara gidan tsaf ta kulle da kwado, gidan Tasallah ta shiga ta bayar da mukkulin kafin ta kama hanyar gidansu, salo-salo take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a ciki........."Hamra'u." da sauri ta juya jin muryar kawarta Zabbah, taja ta tsaya tana wasa da karan dake hannunta har ta karaso gurin da faratin goro da lemon tsami a kanta. Zabbah ta karaso inda take da fadin." Daga ina kike haka naga duk jikin a sanyaye."? Ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Daga gidan yayar mahaifina nake kullum ina zuwa nayi mata aiki kafin ta fita. Zabbah ta fashe da dariya irin ta shakiyanci kafin tace."Hamrau kenan wai kenan kina kamun kafa ko? wallahi kina wahalar da rayuwarki domin kaf cikar karkarar nan banga wata mace da zata ja ra'ayin *GOJE! ba* Tace." To ke Zabbah waye ya fada miki ina kamun kafa da Uwale a matsayin uwa take a gurina laifi ne don naje gidanta." Zabbah ta tabe baki da fadin." Hamra'u bari na fada miki abunda baki sani ba, kaf 'yan matan garinan babu wacce bata san halin da kike ciki akan *GOJE!* ba kowa ya san kece kike sonsa baya sonki kullum sai kinji kinyiwa kakarsa aikace-aikace sai kace baiwa bayan haka ance idan yana gari kece kike masa wankin kayansa ki goge ki wanke masa takalma saboda rashin hankali irin naki kin mayar da kanki yar aiki bayan baki da tabbacin zai aureki. Tace."Zabbah! duk abinda kika fada hakane babu karya ina san UMARU kuma ina rokon Allah yasa ya zama uban 'ya'ya na, bayan haka kuma duk wata bauta da nake masa ra'ayi na duk surutun da jama'a za suyi akan hakan bai dameni ba." Ta girgiza kai da fadin." Shikkenan ai tunda kinyi nisa duk abinda zan fada miki a yanzu ba zaki fahimta ba, saboda haka muna zuba ido muga yanda za'ayi wannan auran. Shuru kawai tayi bata sake magana ba, ita Zabbah ce keta surutu tana bata labarin saurayinta wanda zata aura uffan bata ce ba har suka rabu da juna. Cikin kunci da damuwa ta shiga gidansu, nan ma ta iske wani bacin ran don mahaifiyarta fada ta rufeta dashi sosai tace."Ina ji ina gani kinfi karfina Hamra'u! saboda kulafucin namiji kullum da gari ya waye hankalinki na wani guri kisa kafa ki fita ki barni da aikin gida, kina can kina bauta a wani gurin, to wallahi nagaji ba zan hanaki ba tunda ke ki kasa kanki amma ba zaki kara fita ba sai kin gama min aikin gida." Daki kawai ta shige tana kokarin danne kukan dake kokarin kufce mata, wai shin da wane bala'in za taji? ko'ina babu sassauci, bata samun nutsuwa da kwanciyar hankali sai a gurin Uwale ita kadai ce ke kwantar mata da hankali, amma ita kanta wacce ta haifeta kullum habaici take mata akan wanda ta kwallafawa rai! kowa yana ganin laifinta bayan itama ba ita tayi kanta ba, Allah ne ya halliceta ya sanya mata soyayyar wanda bai san ta nayi ba, dole idan ya dawo ta cire kunya ta sameshi da maganar ko ta san matsayinta.. *Don Allah idan ba sayan littafi zaki ba kada ki dauki number ta Nagode *Ga mai bukatar Sadauki Omar 1k zai tura domin samun damar karanta littafi biyu Goje sadauki Omar return* *#500 via 0542382124......Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari Katin airtal ko Mov 1/12/22, 20:33 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ FREE PEGE *15&16* Sosai ta kwanta jinya sakamakon artabun da sukayi ita dashi, jikinta yayi mugun tsami! ta shar'be! a guri guda da kyar take iya motsa hannu saboda tsabar sanyi da jikinta yayi, al'amarin bai tashi tsananta ba sai da dare ya tsala tukkuna, ta kasa rintsawa gabadaya jikinta ya dauki ciwo! ga wani irin kaikayi da ciwukan jikinta keyi. Kuka ta dinga yi tana jan hanci! ita kam wannan bala'i bata san ina zata kai shi ba. Can cikin baccin daya dan fizgeshi ya dinga jin shashshekar kukanta, zumbur ya mike zaune, dama babu wata tazara a tsakaninsu, ya d'auki fitilar dake gefansa ya kunna yana daga inda yake zaune yake haska gurin da take. Hannu tasa ta kare fuskarta ta sake takure jikinta tana cigaba da zubar da hawayen azabah!. Ya karaso gurin da fitilar a hannunsa, ya dudduba ko'ina babu wani abu. tsugunawa yayi a gabanta yana duba fuskarta, hannu tasa ta doke fitilar ta fadi. a take ta mutu gurin yayi duhu! ya lalubi fitilar yana kokarin gyara batir din, amma ina ta rikice! yayi-yayi ta kama taki, haka ya hakura ya ajiyeta kafin yace." Kukan me kikeyi ko wani guri yana miki ciwo a jikinki."? Shuru tayi masa, ya sake maimaita maganarsa, uffan ba tace masa ba. Sai ya yun'kura da niyyar barin gurin tayi saurin rike gefan rigarsa, a rikice tace."Jikina ne duk yake ciwo ko'ina babu dadi." Yanda yaji tana magana a rikice da alamun kuka ya sanya ya gazgata maganarta, bece komai ba ya sake yunk'urin tashi. Ta rike gefan rigarsa da kyau! yaja! taja! sai ya juyo yana kallonta, da k'yar ta mike zaune kafin tace."Kada ka tafi kayi wani abu wallahi zan iya mutuwa." Yana da tsananin tsausayi mussaman akan 'ya mace! sai duk jikinsa ya mutu, ya koma ya tsugana yana dan ganin shatin fuskarta duk tayi wani iri idonta yayi jajawur! fuskar duk ta kumbura!. Be iya tausasa murya ba, amma sai ya tsinci kansa da sassaita muryasa yace."Yi hakuri ki sake min rigar na samo miki magani."! Hanci taja kafin ta sakar mai rigar ya tashi, tabi inuwarsa da kallo tana sauke ajiyar zuciyar wahala. 'Daya daga cikin yaranshi ya umarta daya had'a masa maganin ciwon jiki, da yake duk suna tafe da guzurinsu, ba tare da anja dogon lokaci ba, ya harhad'a komai ya nufi inda take dashi a hannunsa. Samun ta yayi tana rawar d'ari, domin lokacin sanyi asubah ya fara sai zazzabi yake kokarin rufeta, sai datse hakoran bakinta take. Cikin wani irin yanayi ya mika mata maganin da fadin." Kar'bi kisha wannan za kiji sasaauci sannan zaki samu bacci." Kasa kar'ba tayi saboda halin da take ciki kawai ido ta tsirawa fuskarsa hawaye na sharara! jikinta gabadaya yaki tsayuwa a guri daya saboda karkarwa!. Ya ajiye maganin hannunta ya lalubo ya rike a cikin nasa, nan yaji zafi rau!! ya sake shiga damuwa da ya fahimci zazzabi ne a jikinta. Sosai ya zauna a gurun ya kama dukkanin hannunta cikin kokarin sassaita muryarsa da sigar rarrashi yace."Zazzabi ne ko."? Sai ta fashe da kuka! mai karfi! kamar me jiran kiris! da sauri yasa hannu ya rufe mata baki yana girgiza mata kai! Hannunsa ta cire tana me cigaba da janyo kukan dake cin zuciyarta. Kawai sai ya tsinci kansa da janyota jikinsa, ya sata cikin katuwar rigar dake jikinsa, ya san nauyin rigar zai zame mata garkuwa gurin karkarwar da take. Da yake taimako take nema ba tayi wani turjiya ba mussaman da taji ta kan faffadan kirjinsa dake cike da gargasa ga wani irin dumi da ya fara ratsa jikinta, luf tayi ta kwanta sosai tare da sanya hannu a bayansa ta rikeshi kam! tana sauke ajiyar zuciya daki-daki. Sai da ya fara jin saukar numfashinta a hankali sannan ya dan gyara zaman shi, cikin wannan muryar daya aro yace." *GIMBIYA!* Yanda ya kira sunan yayi masifar kassara mata gabobin jikinta. Taji shi sarai! tayi shuru motsin kirki ta kasa mamakin ma take yanda akayi ta saki jikinta a kirjinsa ba tayi tsammanin zata yarda numfashinta da nasa ya hadu ba sai gata a kwance a kirjinsa male-male maimakon taji wari! ko wani abu makamancin haka na fita a jikinsa sai taji akasin haka, jikinshi baya fitar da wari! ko kad'an sai ma wani irin dumi! da takeji na ratsa ta, nutsuwa da kwanciyar hankali na sauka a sassan jikinta. *"GIMBIYA."* Ya sake kiran sunan daya sanya mata a lokacin, koda yake daman Gimbiyar ce shiyasa shima ya ara ya yafa. Dan motsi tayi amma bata amsa ba, kuma bata sakeshi ba,
Chapter 10 · 0% Book details