← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 97

Sashe 16

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

kafafunta, ya kai hannunsa gurin yana shafawa da lumshe ido, janye kafarta tayi da fadin." Allah ya isa!! Ya bude idanuwansa da suka rikice! da zazzafar sha'awarta! "Ni kikewa Allah ya isa."? yafada yana nuna kirjinsa. Ba ta amsa ba, wani irin kallon banza take mai, ya lumshe idonsa ya bude da fadin." Ina sonki saboda kinyi min, ban ta'ba amfani da mace na maimaita ba, amma gani guda da nayi miki naji cewa kece zaki zama mahadin rayuwarta, shekaru sun ja ya kamata ace nima na ajiye k'wai a duniya kece zaki zama uwar 'ya'yana, kinzo hannuna babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake." Maganganunsa suka dinga amsa kuwwa! a kunnanta, ta tsira masa ido tana mamakin furucinsa, kallonsa kawai take ta rasa yanda zata fasaltashi, shi ba mutum ba ba aljan ba. Ya mike tsaye a kanta! saurin kauda kanta tayi gabanta na lugudan duka! Blet din dake daure a kugunsa ya fara kokarin kwancewa, tayi saurin tashi tsaye! dariya ya fashe da ita, kafin ya cire blet din ya jefar dashi ya zame wandon............"Innalillahi- wa'ina ilahi raji'un! abinda ta ambata kenan, ta rintse idonta da karfi! tunda take bata ta'ba ganin tsaraicin namiji ba sai a kansa, yanda yake mara fasali to hakama gabanshi yake tamkar na mahaukacin doki!! Wandon ya mayar jikinsa, yana kyalkyala dariyar hauka kafin ya fizgo kafadarta! fuskarta ya rike a cikin tafin hannunsa, ta rufe idonta gam! bata son kallon mummunar fuskarsa. "Ina fatan kin shirya zama tare dani! masoyiyata nayi miki alkawarin baki dukkan wani jin dadi na duniya! gwarzo ne ni akowane fanni! na tabbata cewa ba za kiyi nadama da kasancewarki a tare dani ba." Zuciyarta ta dinga tashi sakamakon warin bakinsa, fuskarta ta fizge! da karfi ta matsa can gefe tana numfarfashi! yawu ya cika mata baki! yana zuwa gurin da take ta fesa masa yawun a fuskarsa! Ya sanya hannu ya shafo yawun yana lashewa! amma kuma fuskarsa ta rikide da alama yaji haushin abinda tayi masa. Sai da ya lashe yawun tsaf! sannan ya kalleta, ta tsorata da yanayinsa, sai ta sunkuyar da kanta, a kausashe! yace." Wannan shine na farko kuma shine na karshe kada ki sake maimatawa idan ba hakaba zan ladabtar dake. Ta cire tsorosa da fadin." Wawa!! kafara ladaftar da kanka kafin ka ladaftar da wani." "Wawa!! kalmar tayi mai ciwo! sosai a ransa sai kawai ya dingi maimaita kalmar a fili yana zagayeta, ta dinga binsa da kallo duk inda yayi, ya shammaceta yasa mata kafarsa ta fadi a kasan a gurin! turmusheta yayi ya danneta iyakacin karfinsa! bakinta yake kokarin sumbata tana kautar da kai yana bin duk inda ta nufa, be fasa maimaimata maganar ba! suka dunga bugawa! domin duk yanda yaso hada baki da ita ya gagara! ta gumtse bakinta gam!!! sai ya zama kamar mahaukaci sai rawar jiki yake babban burinsa yaji yana shan bakinta.................Ba zato! ba tsammani! yaji saukar kibiya a gadon bayansa!! Ya gantsare! tare da zabga ihu!! a zabure! ya mike tsaye! ya fizge! kibiyar ya jefar jini ya fara tsiyaya! tashin hankali kenan! waige-waige yake a gurin yana mamakin yanda akayi hakan ta faru. Cikin zafin nama! ya mikar da ita tsaye sai numfarfashin wahala take, ya rike hannunta katamau! yana sake dudduba gurin!..................! Wani abu dake daure a hannunsa ya murza! kafin ya kirayi yaran sa! kaf! suka kewayeshi! sai dai ganin jini na tsiyaya a bayanshi ya firgitasu! a garin ya akayi hakan ta faru! Ya akayi ogansu ya bari aka cimmasa irin haka? a tarihin rayuwarsa kaf babu wani mahalukin da ya ta'ba fitar masa da jini sai zuwan wannan matashin saurayin lallai akwai wani abu da yake shirin faruwa! Wani irin nishi! yake yana zazzare idonsa! shi kansa yayi mamakin al'amarin, yana da suddabaru! iri-iri! ya akayi har yaron ya samu damar ganin inda yake tare da samun damar harbinsa da kibiya!! Sai kawai ya fasa ihu!!! ya dubi abunda ke daure hannunsa yana wasu irin surutai! ya sake murza abun! yana sambatu! gurun yayi tsit! babu mai kwakwkwaran motsi a cikinsu, domin sun shiga rud'ani da faruwan wannan al'amarin!! Sautin muryarsa ne kawai yake tashi a gurin, yana wasu irin maganganu!..............Can kuma sai haushin karnkuna! ya maye gurbin maganarsa, Tsit! yayi gabansa na wani irin fad'uwa!! Hankalinsu ya kai kololowa gurin tashi!! duk suna tsaye sun kasa tabuka! komai ya zabura! da karfi yace."Tsayuwar me kuke ba zaku ba zama ba har sai ya cimma na." Da sauri suka rarrabu a cikin dajin suna neman inda yake.. Yana tsaye! a gurin sai kace dasashe! har yanzu kuma hannuta yana rike a hannunsa ya rike tamau!! Haushin karnukan! suka cigaba da kusantowa inda yake! da saurin gaske ya fara kokarin janta tana turjewa! kawai sai ya dauketa ya sa a kafad'a, ya riketa da kyau! da niyyar neman mafaka! taku daya yayi yaji saukar wata kibiyar! ya gantsare! tare da sakin ihu!! amma duk da haka bai sauketa ba. *"Ni ne GOJE!!! mugun! makangari sai kuree! Ni cinkun! naci garina kuma ni ke zuwa garin wasu yaki!! kandagarki kurmar dutse! mugun makangari sai kureee!* Sautin maganarsa ya cika dajin gami da kunnuwansu. Ya juya gabas kudu yamma arewa! domin hasashen inda maganar ke fitowa, bashi da tabbacin gurin, kawai sai ya umarci sauran wa'inda ke tare dashi cewa su tashi bomb a kowanne sassa na gurin! Hakan ne kuwa ya faru tashin bomb! sukayi a gurin kowane sassa a dajin ya rikice! da hayaki! wannan damar ya samu yayi dirar mikiya! a gabansa! alokacin da yake kokarin neman mafaka. Kallon kallo aka fara! Zinat kam ganinsa ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta shiga godewa Allah!!! Ido ya tsirawa! hannunta dake cikin nasa. wata kibiyar kishi ta sokeshi! cikin hargagi! yace."Sakar mata hannu ko na sheka da kai barzahu"!! Ya tsira masa jajayen idonsa kafin ya fashe! da dariya ya sake rike hannunta da kyau! Yace." Kai ne dan iskan da kake ganin ka isa kayi gogaggaya dani ko.! Yace" Eh ni ne UMARU! kuma ni zan kawo karshen ta'addancinka."!!! Kaifaffar wu'kar dake rataye a jikinsa ya cire ba tare da zato! ba ya datse! masa hannu wanda yake rike da nata! hannun tun daga kafada har kan yatsu ya fadi a gurin yana wutsil-wutsil, jini kuwa sai tsartuwa yake! ya durkushe! a gurin, yana wani irin ihu!!!!!! Kafin kice kwabo! kaf! kowa ya hallara a gurin, ganin ogansu a durkushe! babu hannu ga jini na zuba ya zaburar dasu! sukayi kansa! sai yayi gaggawar soka wu'ka a wuyan ogan nasu!!! *Uban daba!* ya sake rikicewa! domin bai shirya mutuwa ba, da hannu yayi wa yaran sa alama cewa su ajiye makaman dake hannunsa, sukayi yanda ya umarcesu! Ajiye makamansu keda wuya suka fara jin jiniya alamun jami'an tsaro sun shigo gurin!!!! *Uban daba!* hankalinsa ya sake tashi, babu shakka ya san ya shiga hannun hukuma k'aryarsa ta kare! sai kawai yayi kwance-kwance ya shammaceshi! wani wawan duka ya sakar masa a gwiwarsa!. dukan ya shigeshi! sosai yayi taga-taga! zai fadi wannan damar ya samu ya k'wace! daga hannunsa a sukwane! ya bar gurin cikin wani irin gudu na ceton rai! sauran yaransa suka rufa masa baya...........! Zubewa yayi k'asan gurin ransa a masifar bace! kwata-kwata bai so hakan ta faru ba, amma ba komai tunda har ya samu nasar raba shi da hannunsa guda, watarana zai samu babbar nasara a kansa! Tsinin bindiga! yaji a saman kansa! da sauri ya bude idonsa sai kawai yayi arba da zaratan! sojoji da 'yan sanda! sun zagaye shi kowanne ya saita shi da bindigar dake hannunsa.........."Babban cikinsu shine yayi magana ."You under arrest."! Hannuwansa ya daga sama cikin bin umarni, suka d'aura masa zabgegiyar tsar'ka! kafa da hannu suka sa key suka kulle, kafin su mikar dashi tsaye....! *#500 via 0542382124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* dala dari katin airtal ko mov. 1/21/22, 12:30 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________
Chapter 16 · 0% Book details