← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 97

Sashe 22

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dawo my dear nagaji ne shiyasa ban leka gurinku ba, ina so nayi wanka na huta tukkuna." Cike da kulawa tace." Sannu ya aikin? bari na had'a ma ruwan wanka ko."? yana kokarin cire rigar daga jikinshi yace." Godiya nake Allah yayi miki albarka." Cike da jin dadi ta amsa, kafin da sauri ta kama hanyar dakinsa, ido ya bita dashi har ta shiga dakin ya girgiza kai a fili yace." Wannan itace matar aure mai cikakkiyar tarbiya nutsuwa sanin ya kamata yayi imani ko zuria ya had'a da wannan yarinyar ba zaiyi kaico ba. Ta fito falon ta sameshi daga shi sai vest wacce ta matse shi da gajeran wando domin ya cire gabadaya kayan jikinsa, da sauri ta sunkuyar da kanta kunyar had'a ido take dashi, ganin haka yasa yayi murmushi ya tashi ya bar gurin, da sauri ta dauki inform din ta kai masa daki ta rataye masa kafin ta bude wardrobe ta dauko masa 'kananun kayan shan iska, ta ajiye saman gado da sauri ta fita daga dakin. tana jin wata annushuwa a cikin ranta, yau ta d'an fara ganin alamun sonta acikin 'kwayar idanuwansa.... *Free pege zai 'kare a pege 40 ga masu bukatar wannan littafin suyi payment domin karanta littafin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, kada mugunta!/hassada!/ ganin k'yashi! ya hana ku biya, ku jira na sata ku karanta, wallahi tallahi hakkin wani masifa ne! bala'i ne! muyi kokarin nesanta kanmu da haram! duk kankantarta!* *#500 via....0542382124.....Binta Umar gtbank, idan kati zaki tura kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.......07084653262....Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number.... 22796074090....Dala dari katin airtal ko mov* 1/25/22, 11:27 - Bu hainat: *GOJE!! _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *MANAZARTA WRITER'S* *ASSOCIATION _______________ *35&36* Cikin 'kananun kayan data ajiye masa ya shirya jikinsa tsaf, ya fesa turaranshi mai sanyi da sanyayya rai, ya kimtsa tsaf dashi, kai tsaye b'angaran nasu ya nufa cikin yanayin tafiyarsa ta gwarazan maza! Uwale kawai ya samu a falon ta zubawa tv ido tana kallo, ya shiga da sallama a bakinsa tayi saurin kallon bakin kofar ganinsa yasa ta sauke ajiyar zuciya ta amsa sallamar tare da maida hankalinta kansa har ya k'araso inda take zaune. Tibin ya d'an kalla kafin ya zauna kusa da ita da fadin." Kallo kike ne."? Ta gyara zama da fadin." Gashinan dai Ina kallonsu da ido amma bana fahintar komai, yanzu nake cewa Hamra'u ta kai min tashar Arewa 24 nafi fahimtarsu duk da cewa su din ma wani sa'in suna da abun haushi." Ba tare da yace komai ba ya dauki romot ya canza tasha sunnah tv ya kai dai-dai lokacin da marigayi malam Ahmadu B.u.k yake tambihi akan hadisan Annabi Muhammad (SAW) tace." Allah ya jikan wannan malami yayi wa addinin Allah hidima." Yace."K'warai kuwa ba iyalinsa ne kadai sukayi rashi ba duk duniya ne muna rokon Allah ya jadadda rahama a gareshi." Cikin alhini ta amsa da ''ameen ya Allah." Gurin yayi shuru gabadaya hankalinsu na gurin sauraran malamin, har Hamrau ta 'karaso gurin kafin tace."Yayana na kawo maka abinci nan ne."? Hankalinsa na gurin malamin yace." Eh ki kawo min nan." Da sauri taje ta shiryo masa abincin a tire ta ajiye masa a gabansa, kasan kafet ya sauka ya tankwashe kafafunsa, yana kokarin bude kwanakun abincin tayi saurin zuwa ta bude cikin nutsuwa ta zuba masa towon farar shinkafa tas dashi lailaye a leda da miyar zogale wacce taji kayan hadi tayi kyau sosai sai kamshi ne yake tashi, ya kalleta da murmushi a fuskarsa yace."My dear wannan miyar wace kala ce.''? Tana kokarin magana Uwale tace."Miyar zogale ce, ni nayi sha'awarta nace a maimakon taushe tayi mana ko baka so ne."? Girgiza kai yayi da fadin." Ai ko bana so tilas naci domin farin cikin ku, na san kuma miyar za tayi min dadi kamar yanda nake bukata." Hamra'u farin ciki ya lullubeta, murmushi tayi ta tashi daga gurin taje ta samu kujera ta zauna. A nutse yake cin abincin yana yaba nutsuwa da nagartar yarinyar, duk inda ake tunanin mace ta kai, komai Allah yayi mata nutsuwa tarbiya uwa uba iya girki na zamani dana gargajiya, tunda yake cin abincinta bai taba cin karo da kuskure ba, komai yana masa dai-dai wannan dalilin yasa yake zagewa ya cika cikinsa ba tare da wata fargaba ba, ya cinye wanda tasa masa tas ya 'kara wani yaji dadin miyar sosai da sosai. Koda ya kammala cin abincin, sai ta kwashe kayan ta nufi kicin dasu domin wankewa........Ajiyar zuciya ya sauke bayan barin ta gurin, ya janye idonsa daga hanyar da tabi, Uwale ta kalleshi da fadin." UMARU ni kuwa ina labarin wannan yarinyar."? "Wace yarinya kenan."? Yafada idonshi a tsaye a kanta. Tace." Yarinyar da ka taimaka mata wacce ake maganar 'yar sarkin kano ce." 'Bata fuska yayi da fadin'' Tana nan Lafiya." daga haka sai yayi shuru da bakinsa. 'Yar dariya tayi irin ta tsaffi ta dauki goro ta gutsira kafin tace."Haka kawai nake maka sha'awar auranta" Ya kalleta da mamakin jin furuncinta, da kyar yace."Me yasa kike min sha'awar auranta bayan duk ga 'yan mata nan masu hankali da tarbiya'' Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To UMARU kaine ai kamar mara lafiya duk macan da akayi magana maganarta sai ka 'bata ranka abinda yasa nayi maka maganar yarinyar domin naji abinda yake zuciyarka na d'auka ko akwai alakar soyayya a tsakaninku." Girgiza kansa yayi da fad'in" Babu kuma ki cire hakan a ranki, halin da ake ciki a yanzu shine ina binkice akan yarinyar da zan aura." Fuskarta a sake tace." To masha Allah, nayi farin cikin hakan, amma UMARU ya za kayi da wannan yarinyar Hamra'u ta jima tana sonka don Allah kada ka watsa mata 'kasa a ido" Murmushi yayi kafin yace."Ai ita zan aura da ikon Allah." sai ta wangale baki tana kyalkyala dariyar farin ciki ta dafa kansa da fadin." Kai masha Allah naji dadin wannan al'amari UMARU Allah ya tabbata da alkairi ya nuna min lokacin da zanga zuriarka, amma ina alfarma a gurina." Ya kalleta da fadin." Wace alfarma kuma"? tace." Bana so aja dogon lokaci ayi komai a gama a lokaci k'ankani." Yace."Kada ki damu insha Allahu daga na dawo daga training za'ayi komai a gama da yardar Allah." tace." to Allah ya tabbatar mana da alkairi" ya amsa da ameen ya Allah." ***** A daran ranar Asp ya umarce su ita da Nabila yace su shirya zasuje unguwa, ba a son ranta ta shirya ba, suka fito harabar gidan a tare sai cika take tana batsewa tana ya mutse- ya mutse, ita kuwa Nabila kamar koda yaushe fuskarta a sake kamar gonar audiga sa'i da lokaci ta kan yi mata magana, idan ta kama, sai taga dama take amsawa, a bayan motar suka zauna Asp din ya zauna kusa da direbansa. Babban super market suka nufa, ya kalleta da fadin." Duk abinda kike da bukata kina iya dauka." Uffan ba tace masa ba tayi gaba tana zagaye gurin, girgiza kansa kawai yayi ya matsa can gefe tare da fito da wayarshi. Abokin nashi ya kira, don yanzu UMARU ya zama abokinsa duk da ya girme masa, amma abota suke tamkar tare suka taso aiki yasa sun shak'u da junansu, Cike da girmamawa ya daga wayar suka gaisa kafin Asp din yace." Ka tsammaci zuwana gurinka yanzu." Cike da mamakin hakan yace." Ina fatan ba wata matsala bace." Yace." Alkairi ne zamu tattauna wasu batu masu muhimmanci" Yace." Okey to shikkenan sai ka shigo din" sallama sukayi kafin kowa ya kashe wayarsa. Turaruka kawai ta iya dauka sai kayan za'ki data jida sai kace shazumamu! haka take da shan zaqi kamar me a cikin hakoranta ma akwai wanda suka dan samu matsala duk ta dalilin shan zaqi. Tana gama tsintar abunda take bukata ta mi'kawa Nabila kwandon kayan, ita kuwa ta kar'ba ta had'a na da na hannunta, kai tsaye gurin total ta nufa da kayan, ita kuma ta fita daga gurin.......Tun kafin ta k'arasa bakin motar direban ya bude mata ta shiga ta zauna har yanzu babu sassauci a fuskarta. Ganin fitowarsu yasa tayi saurin dauke kanta babu wanda ya tanka mata, direban ya bude masa mota ya zauna, kafin ya kar'bi ledojin hannun Nabila ya bude boot ya zuba, ba ta jira ya bude mata motar ba, ta bude da kanta ta zauna tare da bisimillah a bakinta. Koda suka shiga barrack din direba na kokarin parking ya umarceshi da cewa ya zarce dasu gida mai lamba shida(number 6) kai tsaye can ya nufa yayi parking a inda aka ta nada kafin ya fito da sauri ya bude musu mota. Tun sa'ilin da Asp din ya kira wayarsa ya sheda masa zuwansa ya fito ya tsaya domin tsumayinsa sai dai ganinshi tare da yarinyar ya d'an sosa zuciyarsa, amma be nuna hakan a fuskarsa ba, cikin wani irin taku na gwaraza! ya isa bakin motar gabadaya hannuwansa goye a bayansa. Hannu ya mika masa sukayi musabaha ga juna, Nabila da saurin gaske ta gaisheshi har tana kiran shi da Uncle, ya dan saki fuskarsa ya amsa shima ya darajata kamar yanda tayi masa ya 'boye asalin sunanta ya maye gurbin sa da daughter ina godiya." Murmushi kawai tayi tana sunkuyar da kanta.............Kamar yanda ya watsar da lamarinta ita itama haka ta watsar dashi, ta dinga cika tana batsewa tana banka musu harara! tabbas da ta san gidansa ne da tuntuni ta sauka a hanya domin bata bukatar abinda zai had'ata dashi. Asp ya juyo cikin tsare gira ya kalleta da fadin." Ku shiga ciki ku gaisa da mutan gidan, sannan ke Zinatu sai kiyi mata bayanin kanki." Ta kalleshi da niyyar caccakarsa, yanda ya sha kunu! yasa ta d'an ji shakkarsa domin ta fahimci shima dan had'in takaici ne mybe tana iya magana ya buga mata tsawa! a gaban mak'iyinta wannan dalilin yasa tayi shuru amma a fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a b'ace yake, Nabila ce tayi gaba, kafin tabi bayanta tana d'acin rai! Barin su gurin yasa gabadaya suka sauke ajiyar zuciya, suna shakkarta tana shakkarsu, tana da wata baiwa wacce ita kanta bata san tana da ita ba, koda yake jinin saurata gaba da baya yana yawo a jikinta, dole takewa mutane kwarjini a ido, dan dai
Chapter 22 · 0% Book details