Sashe 3
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kina girmama kanki kina mutunta kanki, duk wanda ya gaji saurata baya kambaba kanshi kamar yanda ke kike, ina so ki sani zargin da kike a kaina kar ki gazgata, Allah ya kawoni ne tareda jama'ata domin na taimakeki, kuma zan taimakaki bakin kokarina, amma ni zan koya miki tarbiya. Magana za tayi ya sanya yatsunsa biyu ya murje fatar bakin...........tsam! ya rike lebunan yana ligwigiwitawa, kukan zucci kawai take, jikinta yayi mugun sanyi, yana sakin bakin ta silale a gurin, yaja tsaki da furta "kalankasa kawai."! Zanin dake nannad'e a jikinta ya janye duk tana jin abinda yake amma tsabar yanda jikinta yayi tubus, ta kasa hanashi sarrafata. Bai damu da kallon wasu sassan na jikinta ba, domin gabad'aya babu wani feelings a tare dashi, tunda yake sai yace babu ranar da wata mace ta ta'ba tayar masa da hankali duk zubi da kirar dake gareta, Asalima yakan jima bai shiga yanayi na bukata ba, shiyasa auran baya gabanshi, wanda uwar rikonshi wato kakarsa Uwale keyi masa surutu akan hakan. Da kanshi ya lalubi inda kunamar! ta harbeta ya shefe gurin da magani, ganin duk yaran nashi sun bar gurin yasa ya bude mata jikin domin qunar tasha iska. Har ya gama abinda yake a gurin bata daina zubar da hawayen takaici ba, tayi turr! da wannan rayuwar da take ciki, a tunaninta hanya ba zata iya had'awa dashi ba, sai gashi w *Kazami- Bagidaje!* irin sa yana ganin sirrin jikinta. tana ganin wannan ko hadimanta (masu yi mata bauta) sun fishi kyawun gani sai gashi a banza yana yin yanda yake so a kanta ya tatta'ba jikinta babu tsoro ko shakka a tare dashi hawaye masu zafi ta goge tana jimanta al'amarin. Taji dadin maganin sosai domin tana tsaka da tunanin hanyar da zata bi domin kubutar da rayuwarta bacci mai nauyi ya dauketa. ***** Kana ganinta kaga bafulatana, doguwa ce sambal kyakykyawa a fuska, gata fara tas! ta tara duk wasu abubuwa da da namiji ke bukata amma hausawa sukace wai Dan Adam tara yake be cika goma ba, Hamra'u bata da cikkar kirji hakanan kuma babu baya a tsaye take kamar muciya da zani, sai dai akwai tarbiya da kunya irin ta fulani. A nutse tayi sallama a gidan, Uwale dake uwar daki ta amsa, da fadin.'' 'Yar halak yanzu nake maganarki a zuciyata. Murmushi tayi ta cire takalminta, ta shiga dakin, Uwale na kurbar kunu ta mika mata kofin da fadin " Bisimillah." Girgiza kai tayi tana murmushi tace." Ai daga gida nake kuma sai dana karya kafin na fito. Dariya tayi irin ta tsoffi tace." Hamra'u kenan wai me yasa duk sanda zan baki abu sai kice daga gida kike ko dai kankyamina kike ne."? Da sauri tace."Aa Wallahi ba haka bane Uwale na koshi." Tace."To ai shikkenan duk ya mutan gidan."? Tace."Suna nan lafiya lou alhamdullhi babanmu yace a gaisheki da kyau.'' Tace."Ina amsawa ai a cikin satin nan nake so nazo gidanku mu gaisa sai kuma *UMARU* Yayi tafiya gashi zai dauki sati guda bai dawo ba. A sanyaye tace."Yanzu fa nake shirin tambayarki ina yake shine zakice yayi tafiya kuma sai yayi sati zai dawo." Tace."Eh haka yace min da zai tafi kin san dai yanayin al'amuranshi, wani sa'in ma har wata guda ya kanyi yana gwagwarmaya a daji" A raunane tace." Ni wallahi ba naso yana irin wannan yawace-yawacen tsoro nake kada 'yan fashi su kasheshi ko kuma namun daji su cinyeshi." 'Yar dariya tayi tana sud'e kofin kunun data gama sha tace."Sai dai kiyi hakuri Hamra'u wannan mijin naki yayi nisa addua kawai zaki dinga yi masa. Tace."Kullum inayi masa addua tare da sauran jama'a." Tace."yawwa hakan yana da kyau, sannan ki cigaba da hakuri insha Allahu, hankalinsa zai karkato kanki." Idonta ya cika da ruwan hawaye, tace."Uwale sai nake ganin kamar baya sona tausayina kawai nake gani a kwayoyin idonshi. Tace." To in banda abinki Hamara'u ai sai da so ake tausayi, da baya sonki ba zai tausaya miki ba." Shuru tayi tana nazarin maganar, itafa tunda take dashi babu wata kalmar so daya taba furta mata, asalima yana kiranta da kanwata, amma bai taba cewa Hamra'u ina sonki ba, sai dai yana tsananin bata kulawa komai take bukata idan tayi masa magana kai tsaye yake mata, wannan dalilin yasa iyayenta da ita Uwalen suke ganin kamar sonta yake, ajiyar zuciya ta sauke ta kudire a ranta cewa idan ya dawo zata cire kunya ta tambayeshi matsayinta a zuciyarsa. Hamra'u 'yar kanin Uwale ce, tun tana yarinya Allah yasa mata so dakaunar Goje tun be fahinta ba har Allah ya fahintar dashi, be ajiyeta a wani matsayi na daban ba face wanda take dashi a zuciyarsa, gabadaya tunda ya taso baya da ra'ayin soyayya, shiyasa baya fahimtar tarin 'yan matan dake k'aunarsa, Samari da yawa a karkarar tasu suna kishi dashi, a cewarsu sai kace shi kadai ne namiji ko wacce budurwa bata da magana sai tasa, ransu yana baci mutuka, suna kuma bala'in kishi a kan haka, ita kanta Hamra'un akwai wanda yake mutuwar sonta amma fafur taki amince masa ita dai Umaru takeso wanda bata da tabbas a kansa.............. Uwale, kayan dillacinta ta dauko ta nada gammo ta dora aka, tana gyara yafan mayafi take fadin."Hamra'u ni zan fita dama a irin wannan lokacin nake samu na nemi halalina idan kin gama gyara min gidan ga kwado ( dan mukulli) akan taga ki kulle gidan ki bawa Tasallah ta ajiye min." Tace."Uwale inace Yayana ya hanaki yawon dillaci nan kuma kin san Babana ma baya so me kike bukata ne a duniyar nan." Tsaki taja da fadin." Sai kiyi kuma kinga tafiya ni babu wanda zai hanani neman kudi." tana gama maganarta tasa kai ta fita daga gidan. Hamra'u girgiza kanta kawai tayi idan da sabo ta saba da hakan , a nutse ta mike ta fara ayyukan dake gabanta.... *********** *WAIWAYE* K'allo d'aya nayi masa na fahimci wanene a gabana, ko da yake koda zanyi shekara d'ari ba tare da na sanyashi a idona ba to ba zan mance kammaninsa ba, *Sadauki Omar* kenan Sarkin dake kan karagar mulki a jahar *Kano* Adalin sarki wanda al'ummarsa ke jin dadin mulkinsa. Yana nan a yanda kuka san shi tsayayye! kuma jarumin namiji! kamanninsa suna nan sai dai alamun girma da ya baibayeshi amma a tsaye yake da jarumta babu abunda ya samu nakasu a cikin halayensa da d'abi'unsa. Yana tsaye a tsakiyar babban falonshi hannuwansa goye a banyanshi yana kai kawo a gurin, kallo daya kayi masa zaka fahimci yana cikin damuwa. Cikin nutsuwa da kamala tayi sallama be juyo ba ballantana ya amsa sallamarta, kai tsaye inda yake ta nufa, sai na bita da kallo, ina hasashen a inda na san fuskarta, Gimbiya *Aysha ce fa* zuciya tayi saurin tuna min ita Cike da dumbun mamaki nake kallonta tana sanye cikin laffaya milk color da adon zaiba kafarta sanye da takalmi rufaffe irin na sarauta, ban hango wata tawaya a tare da ita ba domin kuwa jikinta ya nuna alamun hutu da jin dadi sai dai alamun shekaru sun tura hakan ma sai ka 'kura ido a kanta sannan zaka fahimci cewa ta kwana biyu a duniya. Hannunta ta d'ora kan kafadarsa, a nutse ta kira sunanshi *"Jarumi."* be juyo ba ballantana ya kalleta, sai ta dora kanta kan kafad'arsa, hawayen da take boyewa suka kufce, wai shin ya za suyi da wannan ibtila'in da yake kokarin ruguza musu farin cikin da suke ciki na tsayin shekaru masu yawa................ *Ga wanda bai samu damar karanta Sadauki Omar ba, zai tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu tare da Goje! Sadauki Omar return* *#500 via 0543282124...Binta umar gtbank, idan kati zaki tura ki min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262........Mutanan Nijar ku tuntunbi wannan number....* *22796074090* Mutanan Nijar zaku turo min katin Mov ko airtal na Dala dari. 1/12/22, 20:31 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ FREE PEGE *7&8* _*Banyi tsammanin rubuta wannan littafin a kusa ba, asali ma nayi wa kaina alkawari cewa na daina sakin littafi sai na kammala, amma cikin ikon Allah ya nufe ni da fara rubuta wannan littafin ba tare da nayi tunanin hakan ba, ina rokon Allah ya bani hakuri da juriyar rubuta abinda za'a amfana dashi, sannan ina mika godiya ga dubbanin masoyana wanda na sani da wanda ban sani, hakika duk wanda Allah yayiwa baiwa ta jama'a dole ya gode masa, babu abunda zance da masoya sai godiya da fatan alkairi, sannan a cigaba da hakuri da yanayi na rayuwa, koda zanyi wa wani laifi a bisa rashin sani to ina neman afuwa d'an adam ajizi ne, ina fatan zaku bibiye ni a wannan littafin nawa mai suna a sama, ku bani hadin kai sannan ku bini a sannu a hankali domin isar da sakon dana dauko, #500 kacal zaku biya domin karanta cikakken labarin.*_ *WANNAN NAKI NE* _(AUTAR MANYA)_ *A cikin marubuta ke ta dabban ce a gurina Jin kukanta yake har tsakiyar kansa, koda can baya son ganin tana zubar da hawaye ballanatana yanzu da ta riga ta zama garkuwa a tare dashi. Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo tare da rike kafad'unta, hannu yasa ya share mata hawayen dake zuba a saman fuskarta, ta rike hannunsa da fadin.'' Ka bari nayi kukan domin shi kadai zanyi na samu sassaucin abinda nake ji a cikin zuciyata." Ya girgiza kansa da fadin." Ke kin san bana son zubar hawayenki Aysha me zai sanya ki kara tayar min da hankali bayan wanda nake ciki." Ta tsira masa idanuwanta wanda suke cike da ruwan hawaye " Me yasa ka kasa fahimta ta? me yasa ka dauki laifi kacokan ka dora a kaina bayan idan adalci a za'ayi kaine babban mai laifi dangane da faruwar wannan al'amarin." Girgiza kansa yayi zuciyarsa nayi masa wani irin zafi da k'yar ya iya magana." Bani da laifi Aysha ba zan haifi d'a a cikina na lalata shi ba, ba zan gaji da fadi miki cewa tarihi ne yake maimaita kansa." Ranta ya 'baci da jin furucinsa, a duk sanda zai fadi wannan kalmar akan wannan al'amarin sai taga kamar akwai rashin adalci a cikin maganarsa. Tana kokarin magana, Safa ta shigo da sallama a