← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 97

Sashe 2

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

cikinsu sun farauci k'ananun dabbobi irin wanda suka firfito, ya basu umarnin zuwa su nannad'o macijin da ya sare masa kai, yana gama basu umarni yayi gaba bai tsaya ba har sai da ya cimma inda ruwa yake, Kwantar da ita yayi kan rairaiyi, yasa hannunsa cikin ruwan yana debowa yana watsa mata a ko'ina na jikinta. Sai da jikinta ya jike jagab da ruwa sannan Allah ya bata ikon sauke ajiyar zuciya, gashin idonta ya fara motsi tana so ta bude idon amma sunyi mata nauyi ga wani irin ciwo da kanta yake mata, hannu ta dora saman kanta bakinta sai motsi yake, Tashi yayi ya bar gurin. Ta jima tana ganin dishi-dishi a idonta kafin su bude sosai, da yake garin ya soma haske can nesa ta hangoshi tsaye amma bayanshi kawai take gani, cikin mugun tsamin jiki da azabar qunar data tashi tai jawur! ta mike zaune tana bin ilahirin jikinta da kallo, wasu zafafan hawaye suka kwace mata, lebe ta ciza tana furzar da wani irin huci! wai kamar ita Gimbiya gaba da baya itace a wulakance a yashe a bakin kogi, wani kazami bagidaje yana ganin sassan jikinta, wannan abun yayi mata mugun ciwo a rai. Yana daga inda yake tsaye ya dinga jin shashshekar kukanta na tashi. Ya juyo tare da da zuba mata jajayen idanuwansa. Itama shi take kallo tana kisma irin hukuncin da za tayi masa mutukar ya kusanto inda take. Be saurareta ba, bakin kogin ya nufa ya tsuguna yana daura alwala. Jin sawun tafiya da haushin karnuka yasa da sauri ta waiwaya, yaran shi ne tare da karnukansu da kuma abunda suka farauto. Suka samu wani fili suka zube kayansu da yake duk inda zasu shiga sukan tafi da guzurinsu, wata katuwar dadduma suka shimfida, kafin su hura wuta, sannan suka nufi bakin kogin domin daura alwala kamar yanda suka ga ogansu yayi Shine ya jasu jam'i, duk tana zaune tana kallonsu, suka idar ya daga hannu sama yana addua suna amsawa mamaki sosai ya lullubeta ganin yanda yake azkar masu zafi da adduoin da takasa tantance mai yake fada tunda wasu da labarci yake, tayi mamakin hakan daga gurinsa a ganinta rikakken *d'an daba* *d'an ta'addah!* irinsa bai kamata a samu ilimin addini a tare dashi ba. A nutse ya juyo yayi wani irin zama tamkar basarake! ya kashingida tare da tankwashe kafa daya ya dogare dayar tare da dora hannunsa akai. A maimakon musabaha kamar yanda Annabi ya koyar sai kawai suka dinga dukan hannunwasu da sunan gaisuwa a gareshi, wasu daga cikinsu suka fara bushe-bushe irin nasu suka hada baki gurin fadin." *A lafiya Goje!* *Cauuu!!* Uban mafarauta! *Sa'a dai* mai maganin *wuka da kaho* *Dawa dai!! Umarul-Faruku* muna mika gaisuwa a gareka." Ya dinga girgiza kansa yana jin tsigar jikinsa na wani irin tashi, numfashi ya shiga saukewa yana furzar da wani irin huci, Shisha ya kaiwa raruma yasa a baki ya fara tada hayaki a gurin. Ganin haka sai suka tashi suka bar gurin, rabuwa sukayi wasu suka fara aikin gashe-gashen irin dabbobin da suke farauto, wasu kuma suka kutsa cikin dajika domin samun abun da zasu ci. Tana nan zaune a inda take k'aik'ayi duk ya isheta, rana ta kwalle a gurin, so take ta tashi ta sauya guri kunya da tarin takaici sunyi mata dabaibayi, yanda Allah ya taimake ta ma ta lura sam ita din bata gaba gabansu, domin dik wanda yazo wucewa ta kusa da ita ba yayi mata kyakykyawan kallo. Kafafunta ta motsa, domin mikewa tsaye, aikuwa qunar ta kwaile ta fara fitar da ruwa da jini, tsananin azabar zafi ya sanyata tayi saurin mikar da kafar cikin tsautsayi ta danne kunama! lokacin ta d'ana! wani irin 'kara tayi jikinta ya dinga rawa! da rarrafe ta matsa daga gurin, idonta kan kunamar tana kokarin bin gefen kogin domin shiga wani rami...........Kafarsa yasa ya murjeta! yana cire kafar taga yanda tabi kasa tayi daga-daga a gurin!! Inuwarsa ta dinga kallo yayi mata rumfa gata tayi goho tamkar mai shirin haihuwa, gabadaya duwawunta a waje wando ne kawai ya taimaketa. Duk da tana jin tsoron sake zama a gurin hakan nan ta hakura ta zauna jikinta har yanzu rawa yake ga zufa sai ketowa take da sassan jikinta. Tsugunawa yayi kusa da ita har tana jin hucin numfashinsa, ta kalleshi, beyi aune ba yaji saukar kakkauran yawun bakinta a fuskarsa, yasa hannu ya sharce yawun yana me cigaba da watsa mata kwala-kwalan idanuwansa, Cikin zafin nama ta ciko hannunta da kasar gurin zata watsa masa ya kautar da fuskarsa, kasar ta zube a jikinsa, hannu yasa ya buge, ya kalleta fuskarsa a murtuke yace." Meye sunanki a wane gari kike."? Tana kuka me cike da azabar data rasa wace iri ce tace." Ni kake tambaya garinmu kaje ka daukoni a gaban iyayenta amma saboda rainin hankali kazo kana tambayata." Ya girgiza kai da fadin." Ni taimaka miki zanyi amma ban san abinda ya shafeki b.........."Karya kake."! ta katse shi da karfin gaske sai huci take! tana jira ya sake wata magana ta kaiwa fuskarsa mari! Ya jima yana kallonta da mamakin furucinta, tunda ya taso a lokacin yarinta da girma babu wanda ya ta'ba karyatashi cikin abokai da sauran jama'ar gari sai wannan karamar yarinyar, Sa'arta ta sameshi mai tsananin tausayin mace amma ba don hakaba da yau ta gane kuranta a hannunsa. Cinyoyinta ya zubawa ido yana kallon yanda qunar ta ruruce! tana ruwa da jini gashi har ta fara cin jikinta, ba tare da tayi aune ba taji saukar hannunsa, fittt ya d'aye fatar data qone! jiki na karkarwa ta rike hannunsa, tana aika masa da Allah ya isa. Be saurareta ba ya hade duka hannuwanta ya rike da hannunsa daya, ya sake bin d'aya cinyar ya d'aye fatar qunar! kawai sai ta zube a gurin tana makyarkyata. Tsallaketa yayi yaje ya dauko wata 'yar roba cike da gishiri yazo ya tsuguna yana kokarin bude robar gishirin. Ta dinga girgiza masa kai tana kokarin tashi zaune, ya mayar da ita ya kwantar, cikin rashin tausayi, ya barbade qunar da gishiri! ya tashi ya bata gurin..........Sandarewa tayi a gurin kamar matacciya yanzu kukan zucci take mai mutukar zafi, tsabar azaba hawaye ya bushe a idonta, yana daga inda yake ya hango yanda ta wargaje a gurin ta daina boye komai, ya bude wata jaka wani yadi mai kauri ya dauko, ya nufeta dashi, bata iya ce masa komai ba tana kallo ya cicibeta ya dora kan zanin ya nannade mata jiki, can inda shimfidar daddumar take ya nufa da ita ya samu gefe guda ya kwantar da ita. Sannan ya tashi daga gurin, ido kawai ta rufe tana sakin wani irin nishi irin na wahala.... *Ga wa 'yanda basu samu damar karanta Sadauki Omar ba, zasu tura 1k domin samun damar karanta littafi biyu, wato Sadauki Omar tare da Goje! Sadauki Omar return* *#500 via......0542382124....Binta Umar gtbank, idan kati zaki turo #600 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number... 07084653262......Mutanan Nijar ku tuntubi wannan number...... 22796074090* 1/12/22, 20:31 - Buhainat: *GOJE!* _(SADAUKI OMAR RETURN *BINTA UMAR ABBALE *_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION _____________________ FREE PEGE *5&6* Kwanciyarta da kamar mintina goma bacci ya kwasheta sai dai baccin beje ko'ina ba dafin kunamar ya fara yawo a sassan jikinta, a gigice ta tashi zaune gabadaya jikinta ya dauki rawa ga wani irin gumi da yake karyo mata! rikicewa tayi ta rasa inda zata sanya ranta taji dadi. Gurin ya karaso, yana tambayarta, abunda ke damunta, da kyar ta iya bude baki tayi magana. Bece komai ba ya bar gurin, halin da take ciki besa ta bishi da kallo ba, har ya dawo kanta yana kasa wannan karan kuka ya samu ta nayi, ta dan bashi tausayi kadan, amma bai nuna a fuska ba. Ya bude gwangwanin Milo din dake hannunsa, wani abune mai duhu a ciki, da alama magani ne aka kwaba da mai, ya kalleta da fadin." Zaki iya nuna min gurin da kunamar ta cijeki."? Wani irin kallo ta tsawa masa, ta dauke kanta, ranshi ya baci ya daka mata tsawa da fadin" Taimakonki fa zanyi kike min kallon banza kin san wanene a gabanki kuwa."? Hannu tasa ta goge fuskarta ta daure zugin dake damunta, cikin rashin tsoro tace." Sanin wanene kai bai dameni ba, na dai san ka amsa suna biyu wato *barawo* kuma dan *ta'addah."!* Ya tsira mata idanuwansa masu kaifi! yana mamakin maganarta, *'barawo kuma d'an ta'addah!* tunda yake a duniya babu wanda ya ta'ba kiransa da sunan *barawo* sai ita, kalmar *d'an ta'addah* kuwa yana ji tana yawo a gari a kansa. Ya girgiza kansa cikin yanayin maganarsa yace." Wannan shine karon farko da aka ta'ba kirana da wannan kalmomin a gaban idona, kiyi kokarin kiyaye harshenki kafin ki bar hannuna, *GOJE!* nake ba'a kawo min wargi duk tsagerancinki ni zan daidaitaki. Ta kalleshi a wulakance kafin tace."A hakan? babu tarbiyar! ka fara daidai ta kan............'Barin makauniya yayi ya fuskarta, a take hancinta ya tsinke da jini, tasa hannu ta dafe, jiki na kyarma! take kallonsa, fuskarsa ta rikide da zallan bacin rai! "Zaki janyo nai miki mugun rauni a gurin nan, babu ruwana da kowace masarauta kika fito, ki sani ba'a nuna ni da yatsa ban karya ba! sannan ba'a jayayya dani, kuma bana magana biyu, *Billahil-lazi hurramanu!* duk sanda kika kara fadin wata mummunar magana akaina sai na illataki."! Shuru tayi jikinta yayi bala'in mutuwa ganin yanda hancinta ke zubar da uban jini shine abinda yafi zaburar da ita. Ta kalleshi, yana safa da marwa a gurin, tace." A kan me ba zan kira ka da wannan suna ba? ka sato ni a gaban iyayena domin su baka kudi. akan me ba zan kiraka da *'Barawo* ba me kake bukata? da ka kawoni daji ka ajiye kana azbtar dani, kamar ni *Zinatu* wacce ta gaji sarauta gabada da baya ina rayuwa a wannan kazantaccen gurin, tare da kai makaskanci to saurara kaji da kyau! wannan jinin da ya zuba, be zuba a banza ba, wallahi sai kayi daka sanin zubar dashi."! Hannu d'aya yasa cikin aljihun jins din dake jikinsa, ya dan sunkuya tare da dogare gwiwarsa, fuskarta ya dago da hannunsa, yana kallonta tana kallonsa, yace."Daga wace masarauta kika fito naga
Chapter 2 · 0% Book details