← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 97

Sashe 75

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dauki al'amarin, ai idan zakiyi yawo tsirara ba abun damuwa bane mutu'kar bukatarki zata biya, ki sayar da gado da katifarki ai ba'a kanki aka fara ba. Tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas hakan shine mafita domin idan ta tsaya kallon ruwa to kwado ne zai yi mata 'kafa gwara ta tashi a tsaye. Uwale ta kawo mata gurasa *(band'asho) * Kanawa mune gurasa Allah yasa akwai wa'inda suka san meye ma'anar *(Band'asho)* Taji k'uli da man gyada mai kamshi gefe da kabeji da sauran kayan had'i, sosai taji dadi gurasar taci ta k'oshi kafin tayi wanka ta shirya jikinta cikin wani milk din les mai taushi da stones a jikinsa, sai ta dora alkyabba mai tafe da hula a jikinta, ta sanya takalmi rufaffan takalmi irin nasarauta, sosai tayi kyau, kamshi turaranta duk ya cika gidan. Waje ta fito da wayar ta a hannunta.......ido yayi caaa! a kanta, itama kallonsu takeyi sunyi rukuni-rukuni a gindin bishiya suna ta cin abinci babu kimtsi balle kamun kai. Can gefe kuma amaryar ce da k'awayenta da ango da abokansa sun sanya katuwar redio a tsakiyarsu kalangu sai tashi yake amarya da ango suna rawa ana lika musu 'yan biyar-biyar. Abin ya burgeta ya bata dariya kai tsaye gurun ta nufa cikin yanayin tafiyarta. Hamra'u tare da Zabbah dake can nesa suka hangeta tawagar 'yan matan garin sun rufeta a lokacin da take tsakiyar amarya da ango tana manna musu 'yan dari biyar-biyar.......Ihu!!! da kaya-kaya ya cika gurun! Takaici ya hana Hamr'au karasawa gurin, ta juya a sukwane ta koma gida.....Ita kuwa Zabbah! sai da ta k'arasa gurin, ta kutsa ta samu rabonta dan sai da ta tsira da dubu biyu. Da wayarta ta dinga yi musu vedio sai hauka suke suna he da he kowa so yake tayi hoto dashi, amarya da ango kuwa kamar su zuba ruwa a kasa su sha a tarihi ba a ta'ba biki irin nasu ba. Hamra'u ta 'karaso gurin tana wani dauke kai! ita gata wacce ta fita zakkah a cikinsu, da ba a san asalin balbela ba sai ace daga masar tazo .......Ta zuge jakar hannunta ta fito da kudi 'yan dari -dari ta fara watsawa a gurin.........Wani abokin ango yayi saurin sanya wakar *Komai na Babah yafi na yaro!* Zinat kuwa ganin haukan da yarinyar take ya sanya tayi gaggawar fita daga gurin. Ita kuwa Hamra'u sai wani jin kai take tana wani ya mutse fuska! Zabbah taja ta gefe da fadin." Wannan wa'kar fa da Salmanu yasa dake yake, kinzo kina lika dari-dari ita kishiyar taki dari biyar biyar ta dinga watsawa kuma ta watsa yafi dubu ashirin kinga nima na samu dubu biyu. amma ke kina lika 'yan dari -dari sai wani jin kai kike." Jikinta yayi sanyi ta kalleta da fadin." Kina nufin dama saboda naji haushi Salmanu yasa wannan wa'kar! Ta fashe da dariya da fadin." E mana ma'ana kiji haushi kema ki watsa musu kudi." Ta girgiza kai da fadin.' Lallai Salmanu bashi da mutunci." Tace." Hamra'u ni dai shawarar da zan baki shine kiyi hakuri ki kwantar da kanki ku zauna lafiya, dan na fahimci matar nan kamar tana da saukin kai kuma ba zaki samu matsala da ita ba, sannan kuma a zahiri ta fiki ta ko'ina kada kice zakiyi gasa da ita." Tace." Idan na fahimce ki kina so kice na zauna nayi mata bauta ko."? Ta girgiza kai da fadin " Aa ba haka nake nufi ba, ina nufin ki dai daina kishi a kanta dan naga kin zafafa da yawa, baki da gashin wance dole ki zauna a matsayinki." Ta girgiza kai da fadin." Ba zai yuwu ba Zabbah shekara sama da goma ina dauki ba dadi akan biyan bu'kata na amma lokaci guda wata ta shiga rayuwata, wallahi ba zan iya daina kishi a kanta ba, domin bana kaunarta na tsaneta! kuma zan iya komai akan ganin bayanta." Zabbah ta dinga yi mata kallon mara hankali da tunani! itafa gabadaya rayuwar yanzu ta zama wayo da dubara da kuma siyasa mutukar ka iya wannan zaka zauna lafiya, amma shikkenan tunda tayi iya bakin kokari gurin ganin ta nusar da ita ta kasa fahimta zata kyaleta kawai taje duk abinda za tayi rayuwarta ce. Shida shaura ya sauka a garin.......Tun kafin ya fito a mota gurin ya hautsine! hayaniya da ifece-iface! tare da haushin karnuka! Saboda ba ta san ganin bacin rai yasa tayi gaggawar shiga gida, ta san mybe sai ya tsaya yayi abinda ya saba. Sai dai kuma bata jima da shiga gidan ba ya shigo cikin inform da alama daga gurin aiki yake. Koda ya shiga gidan hankalinsa gabadaya yana kanta....ya rungumeta yana ta sumbutar fuskarta. A lokacin su Uwale suka shigo gidan. Uwale Hamra'u da Zabbah dake bayansu......Gabadaya jikin su ne yayi sanyi ganin irin soyayyar da ake zabgawa a gurin, kamar zai cinyeta ya rike fuskarta sai so yake ya kama bakinta tana kaucewa. Gilmawar Uwale a gurin ita ta hankaltar dashi, ya sakar mata fuska yana sauke wani irin numfashi.....Juyawar da zai yi yayi ido hudu da Hamra'u dake tsaye kamar wacce aka dasa, gwiwarta tayi bala'in sanyi! Ya d'an ji kunyarta amma da yake namijin duniya ne sai ya basar yace." Kanwata ina fata dai kin shirya kin kuma yi sallama don yau zamu tafi." Murya na rawa tace." Ni ba zan koma ba." Ya kalleta da mamakin furucinta a tare dashi yace." Saboda me."? Ba tace komai ba, kawai ta juya ta fita kawarta ta rufa mata baya. Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin al'amarin. Ya dan juya in da take, wayam babu ita a gurin......bai kawo komai a ransa ba, ya cire takalman dake kafarsa ya shiga dakin da sallama a bakinsa. Gabadaya suna uwar dakin ita da Uwalen. Kusa da ita ya zauna yana d'an satar kallonta a idonsa ya hango rama a tare da ita kwana uku kacal ta sauya masa tayi haske sannan duk ta rame. Uwale dake had'a kaya tace." Naji kuna magana da Hamra'u ko." Yace." Eh wai me yake faruwa ne? Murmushi takaici tayi kafin tace." Alkairi ne, amma tunda tace ba zata koma ba, sai ka kyaleta a ranar da aka daura muku aure ai dole ta zauna a dakinta." Gabansa ya fadi da jin maganar da Uwalen tayi zata tona masa asiri! be shirya sanar mata da maganar yanzu ba, ya saci kallon fuskarta yaga babu abunda ya sauya a yanayin ta wayarta ma take dubawa. Ajiyar zuciya ya sauke cikin zuciyarsa yake addua Allah yasa ba taji maganar ba, duk da ya san da kamar wuya hakan dan kyau Uwale ta fadi maganar. Ya kalli agogon dake d'aure a hannunsa shida da rabi har an fara kiran sallar magriba, yace." Zan je nayi sallah mu gaisa da wanda ya dace kafin na dawo sai ku shirya." Tace." Ai mu a shirye muke Umaru sallah kawai za muyi. Yace." Uwale anya ba wani abu ne ya faru ba kuwa."? Tace." Me ka gani kake wannan maganar.''? Yace." Naga kamar kina Allah-Allah mu bar garin bayan kinyi alkawari cewa sai kinyi sati uku ko hudu." Shuru kawai tayi ba tace masa komai ba. Ya girgiza kai tare da mikewa tsaye. bahaushe yace shuru ma magana ce, lallai akwai abinda ya faru bayan barin sa garin. Uwale na idar da sallah ta kalleta da fadin.'' Kafin Umaru ya shigo zan dan shiga muyi sallama mutane." Tace."To shikkean ba komai idan ya shigo zan sheda masa. Fitar ta keda wuya ya shigo gidan, yana haska dakin da wayar hannnsa, kan dadduma ya sameta, ta idar da sallah amma bata tashi ba. Ya zauna saman gadon karfen dake dakin yana kallonta. Babu yabo babu fallasa ta juyo suka had'a ido taga yana mata wani irin kallo kafin yace." Zo nan ki fada min abinda ya faru bayan tafiya ta." Ta iske in da yake ya rike hannunta tare da zaunar da ita kusa dashi, gabadaya hankalinsa yana kanta, yana jiran abinda za tace. Tace." Kai me kake tunanin zai faru."? Shuru yayi be san me zai ce ba kawai yana ji a jikinsa ne." Tace." Kamar yanda Uwale ta fada maka alheri ne hakane, Allah ya sanya alkairi a tsakaninku.'' Ya rasa gane abinda take nufi......Ganin yana kallonta yasa tace." Ya aiki ina mutuminka Asp ina fatan kuna lafiya.''? Hannunta ya rike da fadin.'' Asp yana nan lafiya har ya bani sakon gaisuwarki amma da ba kiyi maganarsa ba na manta, sai kuma ni da nake cikin matsala." Tace." Matsala kuma.''? Kai ya daga mata kamar karamin yaro. Ta zuba masa ido tana kallonsa. Hannunta dake cikin nasa ya fara kokarin cusawa k'asan mararshi.......Tsigar jikinta ta tashi da sauri ta fizge hannun tana harararsa. Ido jawur! yake kallonta, kafin yace." Kin gane matsalar ko."? Tace." Kai kam baka da matsala sai wannan."? Yace." Ina dasu amma wannan itace a kan gaba." Ta'be bakinta kawai tayi ta d'auke kanta. Duk ya rasa yanda zai yi baya so tana sha masa k'amshi! tabbas ya san da akwai wani abu a kasa. Ganin abinda take yasa ya kama kansa, yayi kokarin danne kwad'ayinsa, saisaita muryarsa yayi kafin yace." Ina Uwale take ne."? Ba tare da ta kalleshi ba tace." Ta fita domin yin sallama da mutane." Ya mike ba tare da yace mata komai ba ya kama hanyar fita, kallo ta bishi dashi tana girgiza kanta. Bata yarda ta zauna kusa dashi ba, a kusa da Uwale tayi zamanta suna hira, shi kuwa kamar maraya suka mayar dashi direba haushin hakan ya sanya bai sa musu baki a maganarsu ba, sai dai sa'i da lokaci yana amsa waya jefi-jefi! a haka suka isa gidan kowa da abunda ya dameshi. A maimakon ya nufi side dinshi kawai sai ya bita nata, ta riga ta san bin diddigin da yake mata, haka kawai ta tsinci kanta da jin haushinsa. A nan yayi wanka ya kimtsa ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya kaiwa Uwale nata sannan yayi mata bankwana, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa babu wani kuzarin kirki a tare dashi. *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500
Chapter 75 · 0% Book details