← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 97

Sashe 59

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jajawur! "Me kake bukata wanda za kayi break fast dashi."? wannan tambayar tayi masa babu walwala a tare da ita. Ya sauke ajiyar zuciya idonshi gabadaya yana kanta yace." Dake nake so na karya kummalo." Zum'bura bakinta tayi tana dan matsawa daga jikinsa. Ya bita da wani mayataccan kallo kafin yace." Meye haka kike gudu na ko bakya so mu zama abu d'aya."? Tsaye ta mi'ke har yanzu taki sakin fuskarta tace." Ni dai ka fada min abinda kake bukata zan shiga cikin gidan yanzu." Ya mike zaune tare da kokarin janyota jikinsa, ta matsa gefe da sauri.........Yace." Na fada miki ke kad'ai nake buk'ata idan kuma zaki min rowa ne to." Ba tace komai ba ta kama hanyar fita, haka kawai taji tana sha'awar taja masa rai! haka kawai kai tsaye ba zata bashi kanta ba sai ta wana shi! Kasa katabus! yayi kawai ya saki baki yana kallonta har ta bude kofar dakin ta fita......Sai sanda yaji wani irin motsi da gabansa yayi ya dawo hankalinsa, ya kalli gurin yana girgiza kansa, gabad'aya girmansa ya bayyana bai ta'ba riskar kansa a irin wannan yanayin ba. Lamo ya kwanta yana matse k'afafunsa, ai ko ana ha maza! ha mata! sai ya sake aure saboda irin wannan ranar, domin ya lura mata da yawa mugwaye ne basu da tausayi! amma yana tsammanin ba duka suka taru suka zama daya ba, yana da tabbacin idan Hamra'u ce ba zata bar shi cikin halin ni 'yasu ba. Sosai cikinsa yake ciwo mussaman k'asan mararsa, ga wani irin girma da gabansa ke karawa sai hauhawa yake tamkar ya fasa wandon ya fito. Kira ne ya shigo wayarsa dake can nesa dashi.......ya sanya hannu yana lalubanta har Allah ya bashi ikon ganinta. Asp ne yasan za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya.........Cikin sha'kewar murya yake magana. Cike da kulawa Asp din yace." Subahanallahi baka da lafiya ne."? Gyaran murya yayi yana janyo maganar da 'kyar yace." Da sauki dai za'a ace amma ina jin jiki bana tsammanin ma zan fito aiki a halin yanzu." Yace." Nima abinda nayi tunani kenan, ganin takwas ta wuce baka shigo ba yasa nace lallai akwai matsala, shin me yake damunka."? Shuru yayi yana nazarin maganar, Asp abokinsa ne kuma kamar dan uwa yake a gurinsa amma baya tsammanin zai iya fada masa sirrinsa. Dawurwura! yake domin ya rasa ma abinda zai ce masa. Yace." Ashe har mun fara haka da kai, ai na d'auka abunda ya shafeka ya shafeni me yasa zaka b'oye min damuwarka? ni fa na d'auke ka tamkar dan uwa na jini." Gabadaya sai jikinsa yayi sanyi damuwarsa ta sake tsananta Asp din ya gama kashe masa jiki. Yace." Bafa wani gagarimin abu bane kada ka tashi hankalinka'' Yace." 'Karamin abu ba zai sanya ka damu kanka haka ba, a sanin da nayi maka jarumin namije ne wanda k'aramin abu da babba basa firgita ka babu shakka akwai abunda yake faruwa da kai." Jin yanda Asp din yake kambaba! shi ya sanya shi dariya, ya rintse idonsa tare da kokarin danne sha'awar dake damunsa.........Shi kansa mamakin kansa yake, kamar yanda Asp din ya fada k'aramin abu ko babbah basa ta'ba d'aga masa hankali, amma abun mamaki! abunda bai taka kara ya karya ba shine yake wahalar dashi, yarinyar ta zame masa matar jaraba ita kadai yake gani a gabansa koda ya hasaso wata macan ba kamar ita ba. Jin shuru bai magana ba ga wayar na bin iska yasa yace." Kodai har yanzu ban kai matsayin da zanji matsalarka ba kayi shuru, bahaushe yace (shuru ma magana ce.") Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya kafin yace." Matsalar mutuniyarka ce." 'Yar dariya yayi domin sai dama ya raya hakan a ransa, shi kansa matsalar da yake fama da ita kenan......Zeey bata barin sa ya sarara, k'orafin yau daban na gobe daban! yafi samun nutsuwa da Madam Uwargidansa, wannan dalilin ya sanya yaji gabadaya auran ya fice masa daga rai yana jin tsoron auro ta ukun tazo ta daga masa hankali domin tun kafin ta shigo gidan tana nuna zafin kishi akan matansa, yasan ba zai samu matsala da Madam ba, Zeey ce 'yar tujara! baya tsammamin kanwarsu zata jiku guri d'aya. Yana 'yar dariya yace" Umar matsalarka da Zinatu taki 'karewa amma kada kayi mamakin watarana kai da ita zaku iya zama kamar *Laila Majnun!* saboda tsananin so da 'kauna." cikin wasa yake maganar. Girgiza kansa yayi kafin yace." Bana tsammanin faruwar hakan domin ita wannan yarinyar babu macan da ta kai ta 'keta da mugunta! ban san da hakan ba sai yau." Iyakar gaskiyarsa yake maganar. Da sauran dariyar a tare dashi yace." Wai dan Allah me tayi maka ne? nifa kaina ya kulle wallahi." Tsaki! yaja kafin yace." Rabu da ita kawai ai nima ina da rana." Yace." Ai tambayar ka nayi amsa ya kamata ka bani naga kana waskewa. Shuru yayi na second biyu kafin yace." Naga kamar tana jin maganarka kayi mata nasiha cewar abunda take haram! ne mala'iku suna tsine mata! tabbas da taje islamiyya ba za tayi haka ba, amma kai a matsayinka na waliyyin ta sai ka nuna mata hanyar gaskiya." Shi kam Asp dariya kawai yake 'kya'kyatawa domin ya kamo bakin zaran! *Namiji!* har *Namiji!* mace ta mayar dashi sakarai! koda yake shima hakan take a gurinsa lallabawa kawai yake a gidansa, idan ya fito gurin aiki a fafata! Yace." Waye ya fad'a maka mata wasa ne! duk isa da jin kai! idan ka shiga hannunsu sai ka raina kanka.......kawai ka iya zama dasu shine samun kwanciyar hankalinka, domin yawancinsu basu da imani idan wani sa'bani ya shiga Tsakaninku ta nan suke fanshewa babu ruwansu da dokar Allah! sun bi sun take saboda san zuciya, amma kuma muma mazan muna da namu laifin domin bama sanin muhimmamcin matan mu sai bukatar kan mu ta kawo mu, sannan suke da daraja a gurun mu, wannan ba dai-dai bane, yana da kyau mu gyara kuskuranmu suma matan su gyara nasu." A sanyaye yace." Kwana biyu zaman lafiya muke sosai kuma na zauna nayi tunani domin gano dalilin da yasa take gudu na ban ga komai ba, kawai dai nafi tunanin mugunta ta shirya min shiyasa ta bari na saki jikina da ita." Yace." Kasan suna da wani abu, idan kazo biyan bukatarka a gurinsu to burinsu su ja maka rai! yanda na fahimci hakan yana musu dadi." Yace." Nima nayi tunanin haka mybe tana so naje na fashe mata da kuka ko."? Asp din ya fashe da dariya yana girgiza kansa yace." E to hakan ma ba laifi bane zaka iya zuwa amma dai kasan irin kukan da za kayi." Dogon tsaki yaja kafin yace." Allah ya kiyaye."! da karsashi! da karfin gwiwa! ya fadi maganar kamar gaske baya kukan Yace." Ka daina cika baki fa." Cikin jin takaicinsa yace." Ranka ya dade mu bar wannan maganar haka domin wallahi ni raina ne ma yake b'aci! kawai abunda za kayi anan shine ka kira wayarta kayi mata nasiha watakila taji tausayi na ta bani hakkina, amma ina mai tabbatar maka da cewar idan ta'ki to zan k'wata ta karfi da yaji." Yace."Duk ba za'ayi haka ba, kayi hakuri insha Allah zan mata magana kuma komai zai wuce amma ina so dan Allah ka bata muhimmanci domin su mata babban burinsu suga ana kula dasu gami da nuna musu soyayya." Murmushi kawai yayi yana girgiza kansa, a ganinsa duk wata kulawa da soyayya ya bawa yarinyar kawai dai ta shirya zalinci ne don ganin ya jarabtu da tsananin sonta. To kamar yanda Asp din yayi alkawari zai kira wayarta domin yay mata nasiha hakane ya faru..........bai fito 'karara ya nuna mata abunda yake nufi ba, amma yayi mata hannunka mai sanda wanda yasa ta fahimci abunda yake nufi.......Ba ta iya cewa komai ba, har yayi mata sallama, ta kashe wayar tana sauke ajiyar zuciya. Tabbas bata raba daya biyu shine ya shedawa Asp din abunda yake faruwa a tsakaninsu..............Ita fa akwai manufarta kai tsaye ba zata amince masa ba a yanzu sai nan da wasu kwanaki. Na farko tana tsoron daukar ciki tunda tsarkinta kenan.........tana da tabbacin cewa idan rabo ya rantse a tsakaninsu za ta iya samun ciki dalilin k'ofofin jikinta da suke a bude.....Wannan shine babban dalilin da yasa take gudunsa, tafiso ko wani abu zai shiga tsakaninsu ba yanzu ba tukkuna. Wanka tayi taci gayu tana kamshi turare kala-kala ta zauna a falo tana kallo tana tsikarar duniyarta da tsinke babu abunda ya dameta! Ta manta dashi domin duk a tunaninta ya tafi gurin aiki..... ........Kawai sai ta tura Baraka ta nufi sashen domin gyarawa kamar koda yaushe. Baraka tasa key tana muzara kofar taki bud'ewa, shi da yake kwance a uwar daki ya dinga jin motsi ya fito falon yana tambayar waye." Gabanta na faduwa tayi saurin barin gurin.........tana kokarin shiga wani korido ya hango bayanta, nan ya fahimci cewa d'aya daga cikin masu aikinta ne, ya koma ciki da mamakin hakan a tare dashi. Baraka ta sheda mata cewar yana nan bai fita ba, jikinta a sanyaye tace." Amma dai baku had'u ba ko."? Da sauri tace." Eh ai jin yay magana yasa da sauri na matsa daga gurun. Ajiyar zuciya ta sauke tare da jin sanyi a cikin zuciyarta, tasan duk ranar da yasan abunda yake rufe akwai rikici. Sai bayan la'asar ya samu kansa, a gida ya gabatarsa da sallah dan bai iya shiga massalaci ba gudun abunda ka iya zuwa ya dawo kawai ya hakura yayi sallar a gida...............Kai tsaye sashen Uwale ya nufa ya same su zaune a falo suna kallo. Ya samu guri ya zauna yana kiran sunan Allah.....Uwale ta kalleshi da fadin." Ashe baka fita."? Yace." Eh wallahi na yini bana jin dadi sai yanzu na samu sassauci." Tace." Ayya ai ba labari me yake damunka."? Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Ciwon ciki ne amma yanzu da sauki tunda nasha magani." Tace." To Allah ya sawwake." Ya amsa da "ameen yana kallon gefan da Hamra'u take zaune sai cika take tana batsewa! Abun ya bashi mamaki sosai! yarinyar ba ta'ba share shi irin yau ba......Cikin kulawa yace." Kanwata lafiyarki kalau kuwa? bako gaisuwa." Ta kalleshi tana sake hasaso abunda ya faru! kawai sai wasu zafafan hawaye suka ciko idonta.......Wani irin
Chapter 59 · 0% Book details