← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 97

Sashe 65

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gwala-gwala masu tsananin ja! kamar garwashin wuta! Ya kalli Asp din da fadin." Ya akayi yanzu meye abin yi."? Asp din yace." Nafiso ka karanta rahotannin kafin mu tsaya a matsaya ana bincike ne a kansa da yaransa da suka sauka a garin. Ya mayar da hankalinsa kan takardar yana karantawa. Rahoto ne daga gidan jaridar *AMINIYA* cewa wasu 'yan gudun hijira da suka samu masauki a k'auye *KUYAN TA INNAH* ana zarginsu da ta'addanci tare da yiwa k'ananun yara fyad'e........Ana dai binkice a kansu domin tabbatar da gaskiya magana. Ya share zufar saman goshinsa, ya kalli Asp din da fadin." Ko shakka ba nayi zasu aikata abunda yafi haka, babu wani maganar binkice! wai shin me yasa jami'an tsaron *KANO!* suke da sakaci ne? to ni da kaina zan shiga Kanon domin a gudanar da binkicen dani idan ba haka ba zasu iya kyaleshi ya cigaba da ta'addanci tare da kashe rayukan da basu ji basu gani ba." Murmushi Asp din yayi kafin yace." Kai ka fiye gaggawa! yanzu idan akayi wani yun'kuri zasu ankara su samu damar tserewa.....wannan rahoton babu wanda ya san dashi sai ni da kai sai kuma Commissioner.......Domin Abokina *Wali Nasiru* dake *KANO* tare da sauran abokan aikinsa ne suka shiga 'kauyen suna binkice akan matsaltsalun dake faruwa.....nan suka samu cikakkaken bayani daga bakin wani dattijo cewa tsayin shekara dari da wani abu wata gagarimar matsala bata ta'ba faruwa ba a 'kauyen sai dalilin zuwan 'yan gudun hijirar.......Dalilin da yasa kenan suka tsananta binkice akansu domin gano gaskiyar lamari.......Kasan abokina ne sosai tare mu kayi karatu to yana bani labarin abunda ke faruwa sai na bukaci da ya turo min rahoton domin ni kaina sai da na zargin wani abu, saboda haka muyi hakuri kada muyi gaggawa domin hakan zai zaburar dasu, su gudu! a nutse zamu kamasu. ina kuma kara tabbatar maka da cewar babu wanda ya san wannan rahoton daga ni sai kai sai kuma mai gayya mai aiki don bana tsammanin ma gwamnati tasan da abunda ke faruwa domin yanzu muka gama tattaunawa commissioner din akan hakan." Dogon tsaki! yaja ransa duk a dagule! wane irin aikin gaggawa ai a ganinsa jinkiri shi zai cutar dasu, ya ga dama sun samu amma za suyi wasa da ita! ya dinga jan tsaki! kansa ya cigaba da sarawa! tabbas da ba dan a karkashin gwamnati yake aiki ba to da babu shakka yau zai yiwa garin *KANO* dirar mikiya duk inda *UBAN DABA!* Da yaransa suke sai ya lalubo su domin gwabzawa! Asp din yace." Ya kamata kaje gida ka huta idan zai yuwu ma gobe ka zauna ka sake jin 'kwarin jikin ka Allah ya sawwake." Ya amsa da "Ameen yana duba agogon dake daure a hannunsa, uku da rabi na yamma....Asp din ya mike da niyyar fita shima mikewar yayi, ya dauki gilas dinsa ya sakaye idonshi kafin yabi bayan Asp din da niyyar zuwa gida ya sha magani ya kwanta ya huta. 'Bangaranta kuwa tunda ya fita ta kasa samun nutsuwa, tana ji kamar ta kira shi a waya tana kuma tunanin kada ta zubar da ajinta.....Haka ta dinga juye-juye a saman gado sa'i da lokaci tana share hawayen takaici! ita kanta ba'a son ranta ta aikata masa hakan ba, kawai ya b'ata mata rai ne. Kafin ya shiga gidan sai da ya gabatar da sallar la'asar tukkuna.........Ya duba gurin su Uwale domin ya tabbatar da cewa sun fito daga asibitin saboda a d'azu da safen Likitan yake tabbatar masa da cewa zai sallamesu zai kuma sanya direba ya kai su gida. Sosai yayi farin cikin ganinsu A falo suna hira har ita Hamra'u domin ta wartsake kamar ba ita ba, hakan duk ya faru ne dalilin kwantar mata da hankali da Uwale keyi ta tabbatar mata da cewa suna zuwa k'auye manya zasu tsayar da maganar daurin auransu, wannan ne dalilin da yasa ta samu nutsuwa ta kuma kwantar da hankalinta. Gabadaya suka dinga bin sa da kallo har ya samu guri ya zauna.......Uwale ce ta magantu, cikin damuwa tace." UMARU mai ya samu 'kafar ka."? Shuru yayi na minti biyu kafin yace." Na d'an taka k'usa ne kin san tana da dafi! shine dalilin da yasa kafar ta kumbura! Sosai tayi mamaki kafin tace." Cikin wannan uban takalmin da kake sanyawa har kusa ta iya huda maka 'kafa UMARU anya kuwa."? Murmushi yayi da fadin." Uwale ki bar tsautsayi kawai! Allah ne kawai ya takaita min wahala 'kusar bata shiga sosai ba ku cigaba da yi min addua." Tace."To Allah ya kiyaye ya tsare gabanka da bayanka." Ya amsa da "Ameen ya rabbi kafin ya kalli Hamra'u da tunda suka fara maganar ba tace komai ba. Ya dan saki fuskarsa da fadin." Ya jikin naki."? Tace." Da sauki Yaya na, kai ma ya jikin naka? Allah kiyaye gaba." Ya amsa da "Ameen ya rabbi nagode sosai amma kin dai ji abunda likita yace miki ko? ki rage tunani dasa damuwa a ranki." Tace." To Yaya na insha Allah zan kiyaye nagode Allah ya saka da alkairi." Bece komai ba ya kalli Uwale da fadin." Uwale a dan bani abinci zanci kafin nasha magani." Ko kafin Uwalen ma tace komai zumbur ta mike ta kama hanyar kicin......Gabadaya suka bita da kallo suna girgiza kai, tausayi take basu. Yaci abincin sosai yayi godiya ga Allah kafin ya wuce sashensa dan beyi niyyar shiga gurinta ba gudun b'acin rai! abunda baya bukata kenan. Marakisiyya dake shanya kayan data wanke a harabar gurin ita taga wuce war sa, ta dur'kusa har kasa tana gaisheshi ya amsa ba tare da ya kalleta ba, ya wuce ya bar ta a gurin. Ita din ke shedawa uwar dakin nata dawowar mijin nata.........Tace mata ta ganshi ya fito daga sashen masu gidan ko za'a kai masa abinci." Ranta ya 'baci! ta kalli Marakisiyyar ta watsar kafin ta buga mata tsawa! had'e da nuna mata hanyar fita. Da sauri ta mike ta kama hanyar fita gabanta na faduwa! sam ba tayi tsammanin cewar maganarta zata fusata! Uwar dakin nata ba, a ganinta kamar gwaninta tayi. Ita kuwa har Marakisiyyar ta fita ba daina hararar hanyar data bi ba.......Wani irin kishi ne yake damunta. wannan ai abun kunya ne mijinta ya dawo amma ace mai'aikinta ce ke sheda mata, bayan haka kuma tana jin haushin abunda ya kai shi sashen masu gidan, hakan baya rasa nasaba da mutsiyaciyar yarinyar data tsana a rayuwarta. Sabon wanka tayi....... sosai tai gayu tayi cikin kananun 'kaya masu daukar hankali, masifaffun turarukan da take d'aukar hankalinsa dasu tasa a kowane sassah na jikinta, kai tsaye sashen ta nufa zuciyarta cike da wasiwahsi! Idar da sallarsa kenan domin tun daga magaribar har isha'in a gida ya gabatar bai samu shiga massalaci ba dalilin matsanta masa da kafarsa tayi, koda yake yasha magani da sauki akan da. Kamar bata so tayi masa sallama, shima babu yabo babu fallasa ya amsa, yana bin ta da kallo har ta samu saman kujera ta zauna. Shuru tayi tana dan wasa da yatsun hannunta!.....shi kuma bai fasa kallonta ba, da carbi a hannunsa yana ja yana nazarinta. Ta d'ago kai suka had'a ido! bai janye idonsa ba bai kuma ce mata komai ba......Itace dai ta janye idonta sakamakon dafin idanuwansa dake kokarin kassara ta! Da 'kyar ta iya bude baki tace." Ashe ka dawo."? Uffan bece mata ba kawai dai ya zuba mata idonsa dasu yake hukuntata! Ta kalleshi a karo na biyu idonsu ya sake had'uwa.......Wani abu mai yuwar fassaruwa take hange a cikin kwayoyin idanuwansa, gabadaya jikinta ya mutu sai kawai hawaye ya kwace mata! suna zuba tana sa hannu tana sharewa tare da shak'ar hanci! tabbas da tana da iko da sai ta dawo da ciwon jikinta a ganinta ma kamar ta fishi damuwa! Gyaran murya yayi kafin yace." Me kuma nayi miki? zaki sanya ni a gaba kina kuka! ai ni zanyi kuka duba da ta'addancin da ki kayi min." Ta kalleshi hawaye share-share! "Nice 'yar ta'addah."? tafada tana nuna kirjinta. Kansa ya daga da fadin." Eh mana baki da imani! idan ba haka ba mai zai sanya ki farfasa min kwalabe a daki ai kinso ki cutar dani ne." Taja hanci tana goge ragowar hawayen daya rage tace." Okey kai yanzu a ganinka abunda ka aikata shine dai-dai."? Ya ajiye carbin dake hannunsa sosai ya mayar da hankalinsa kanta yace." Me nayi ? ina so kiyi min cikakken bayanin abinda nai miki ko'ina akaje baki da hujja! "Shikkenan tunda haka kace ni bazan yi wata magana da kai ba a yanzu amma ina mai tabbatar maka da cewa wallahi idan baka daina ba nima ba zan fasa ba."! Yace." Idan kuma ta hanyar halak nayi fa? shin ko zaki hana ni aikata sunnah da matata."? Shuru tayi tana kallonsa gabanta in banda faduwa babu abunda yake. Yace." Ki kiyaye domin kishin hauka babu inda zai kai ki, sai halaka hakan kuma da kike bashi zai ha nani abunda nayi niyya ba." Jikinta duk ya mutu da maganarsa, a sanyaye tace." Kayi hakuri." Wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa.......Lallai ya yarda da maganar Uwale da Asp in da suke cewa cikin laluma ake nusar da mutum idan yana aikata kuskure......gashi kuwa yayi amfani da damar bukatarsa ta biya bai ta'ba tsammanin zata bashi hakuri ba, koda yake yabi hanyar da hakan zata kasance! Yace."Na yafe miki Allah yayi miki albarka." Ta amsa da "Ameen Nagode." D'akin yayi shuru na 'yan mintina kafin tace." Kaci abinci."? Yace." Eh naci gurinsu Uwale yanzu kwanciya kawai nake bukata." A hankali ta mike ta iske inda yake zaune.........Hijab din jikinta ta cire kafin ta zauna kusa dashi..........Kallonta kawai yake yana sha'kar kamshin jikinta da yake masifar so!! idonta kuri kan k'afarsa kafin ta kai hannu gurin ciwon! Da sauri ya janye yana ya mutse fuskarsa! Tace."Da zafi ko."? K'amar karamin yaro ya daga kansa! Sai kawai ta taya 'bera 'bari ta janyoshi jikinta kansa ta rungume a kirjinsa tana jijjigashi tare da shafa sumar kanshi kamar k'aramin yaro! Tabbb! ai neman ciwo yayi ya rasa irin wannan soyayya! haka mai neman kuka an jefeshi da kashin awaki! mutumin da ake rarrashi! domin yayi bacci sai kawai ya 'buge da kusurkusur yana motsi tamkar yaron dake tsananin bukatar nono! haka ya
Chapter 65 · 0% Book details