Sashe 52
Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kallonsa. Ya kar'bi cup din da fadin." Kin koshi ko.''? kai ta daga kamar wata 'kankanuwar yarinya. Yace." Alhamdulillhi." Agogon dake daure a hannunsa ya duba......'Daya shaura na rana, yana ganin ba zai tunkari wani abu ba yanzu saboda lokacin sallah ne, ya mike da fadin." Lokacin sallah yayi idan kina bukatar wani abu kina iya kiran waya ta." Ya kama hanyar fita daga dakin ba tare da ya tsaya jiran amsarta ba........Wani irin kallo ta bi shi dashi ta na jin kamar taje ta janyoshi ta ha nashi fita har sai ta samu abunda take bukata daga gurinsa. ***** *KUYAN TA INNA!* Wani 'karamin 'kauye ne a garin kano, Wanda bashi da jama'a sosai sai dai yawan gonaki wanda ake noman rani iri daban-daban, da yawa jama'ar dake cikin 'kauyen suna da rufin asiri ta dalilin noman abincin da suke duba da cewar abinda yake wuya kenan a cikin wannan zamanin...........Tunda suke zaune a garin wani gagarimin tashin hankali bai ta'ba faruwa ba kullum suna zaune lafiya kuma koda ba'ko zai shiga garin zasu kar'be shi hannu biyu su bashi masauki suci dashi kana kuma su jashi gona domin dogaro da kansa. *UBAN DABA!* Tare da a yarin sa da sukayi shaura a wannan gari suka yada zango..........Da yake da fuskar salihai suka shiga garin yasa jama'a da dama suka kar'be su hannu biyu, wani Dattijo mai suna malam Dauda ya jagorancesu zuwa fadar mai unguwa domin ya san da zuwan su garin. Mai unguwa ya kar'be su hannu biyu kuma ya bukaci sanin daga wane gari suke. *UBAN DABA!* ya kada baki yace." Ranka ya dad'e mu din mutanan Maiduguri ne kasancewar garin namu babu lafiya yasa mukayi hijira domin samun tsira da rai da lafiyarmu, muna roko a bamu gurin zama kafin komai ya daidaita mu koma garinmu." Mai Unguwa Malam Hassan ya girgiza kai yana jimanta al'amarin...........Yace." Kada ku damu insha Allahu kun zo inda za'a share muku hawaye, Najeria Uwa ce domin kuwa tana d'aukar kowa a matsayin d'anta, sannan garin *KANO* Gari ne da ya sha bambam da sauran garuruwa, da yawa akwai mutanan da suka tsallako daga garuruwansu suka zo suka yada zango a cikin wannan gari namu mai albarka suka zauna kafa sassani tare da kasuwanci kana kuma sukayi aure suka hayayyafa, mutukar ba'a fada ba babu wanda zai ce ba 'yan garin bane, wannan yana d'aya daga cikin halin girma da kuma dattako na wannan gari namu, saboda haka ba zamu k'yamace ku ba, tunda har kuka za'bi yada zango a wannan k'auye insha Allah za muyi iyakar bakin kokari gurin ganin mun baku taimako domin rike kanku har zuwa lokacin da Allah zai kawo zaman lafiya a garinku, saboda haka *KANO TA DABO!* Tare dani mai unguwa Malam Hassan mai wakilatar 'kauyen *KUYAN TA INNA!* Muna muku barka da zuwa." *UBAN DABA!* Ya girgiza kai kamar wani mutumin arziki yace." Ranka ya dade mungode k'warai da wannan karamci Allah ya saka da alkairi, Allah ya baku lada akan aikin alkairin da kuke." Mai Unguwa ya amsa da ameeen ya Allah wannan ba komai bane a gurinmu babban burin mu ace k'asar mu ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali saboda haka duka ku kwantar da hankalinku, ku zauna kamar kowa a cikin wannan gari." To a takaice dai mai unguwa da kansa ya basu masauki mai kyau, ya kuma dauki dawaniyar ci da shansu, kafin tafiya tai nisa, wasu daga cikin jama'ar k'auyen suka fara d'aukarsu suna tafiya gona dasu, amma banda shugaban nasu wato *UBAN DABA!* saboda nakasar dake tare dashi, kullum dai yana tare da mai unguwar a fada yana ganin yanda yake gudanar da mulki a garin. _*SAI MUN HA'DU RANAR MONDAY DA IKON ALLAH *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/21/22, 16:38 - Binta: *GJSR* *75&76* Yini tayi cikin wani irin yanayi mara dadi, domin duk yanda taso da ta danne abunda yake damunta kasawa tayi, hakanan ta kwanta kan gado tana birgima tare da shafa kasan mararta, ita a kan ki kanta tasan bata da hakuri da kawar da kai a wannan gurin domin kuwa da ta sanyawa zuciyarta juria da hakuri to da bata jefa kanta wani mummunan hali ba, to ta riga ta sanya al'amarin a cikin 'kokwan ranta ta kuma kwadaita dashi sosai, abunda ya faru a tsakaninsu a ranar da ya dawo gidan shi take k'ulafuci, dan ta ga alamar kamar hakan ba zata faru ba sai ta tagaza wani abun domin dai tunda ya sanya k'afarsa ya fita bai sake shigowa ba ballanatana wani abu ya ratsa tsakaninsu. Da 'kyar ta samu tayi wanka tayi sallah, don magariba da isha'i ma had'asu tayi tana kokarin tashi daga kan daddumar ya shigo dakin da sallama a bakinsa. Cikin ranshin kuzari ta amsa ta zauna gefan gado tana kokarin cire hijab din dake jikinta. Kawar da idonshi yayi sakamakon yanayin kayan dake sanye a jikinta kananu ne masu fitar da sura. Ya bita da kallon nazari yana mamakin sauyawarta gabad'aya ta zama wata lazy kamar mara lafiya. Gyaran murya yayi kafin yace." Zan dan je wani guri yanzu ina fatan baki da wata matsala."? Kallonshi tayi a karo na biyu, ya shirya tsaf cikin dogwayen kaya riga da wando na shadda dark blue da aiki a wuyan rigar besa hula ba amma ya taje sumar kanshi ta tafi tsaf da kyataccan sajen da ya kwata kyakykyawar fuskarsa, yay mata kyau sosai abinda take ji a tare da ita ya sake nunnukuwa. Lumshe idonta tayi tana sake takure jikinta guri daya. Murmushi kawai yayi be sake cewa komai ba ya juya da niyyar fita yana raya wani abu a cikin ranshi. Motsin fitarsa yasa a hankali ta bude ido tana kallonshi har ya fice daga dakin bata dauke idonta daga kansa ba. Ya fita ya bar mata 'kamshin turaransa wanda ya sake jefata cikin mawuyacin hali, ta kwanta lamo kan gado tana ji kamar ta fashe da kuka saboda rashin yanda za tayi, cikin zuciyarta kuwa tayi wa Faruk Allah ya isa yafi cikin kwando domin a ganinta duk shine silar shigarta wannan mugun yanayin. Meeting suka zauna wanda ya dauke su tsayin awani uku, sai sha daya na dare suka tashi. Sha biyu shaura ya shiga gidan.......kai tsaye gurin ta ya nufa domin duba halin da take ciki. Jin motsin bud'e kofarsa yasa zumbur ta tashi zaune tare da tsirawa bakin kofar ido. Ido suka had'a tana zaune daram tsakiyar gado babu alamun bacci a tare da ita, jikinta sanye 'yar karamar vest da wandon ta k'arami, gabadaya surar jikinta a waje........ta sanya kayan ne domin ta ja ra'ayinsa. Ya girgiza mutu'ka! amma kuma sai yayi namijin kokarin danne kwad'ayinsa, ya nufe ta da wata madaidaiciyar leda a hannunshi mai dauke da wani tambari a jiki. A marairaice take kallonshi tana motsi da bakinta magana take so tayi amma tana jin nauyi. Gyaran murya yay kafin yace." Baki bacci ba har yanzu."? Kai ta daga masa alamar "Eh yace." Me hanaki bacci."? Shuru tayi bata iya ce masa komai ba sai faman lumshe idonta take. Ya sauke ajiyar zuciya tare da ajiye mata ledar dake hannunsa a kusa da ita yace." Ga tsaraba nan nayi miki ina fatan dai kin ci abinci."? Kai ta girgiza a sar'ke tace." Ba wannan nake bukata ba."? Ya kalli idon mara kunya da mamakin furucinta yace." Okey kina da wata bukatar kenan."? Kai ta daga masa, ya kalli agogon hannunsa da fadin.'' Zanyi wanka yanzu amma kafin na dawo ki tabbatar kinci abinci shine zan saurari bukatarki." Ta dan sauke ajiyar zuciya tana kallonshi da sassarafa ya kama hanyar fita......Lips d'inta ta dan ciza tana ya mutse fuskarta, itafa a halin yanzu babu abunda take bukata sai soyayyarsa gabadaya ma cikinta a cushe yake Ledar da ajiye mata ta bude tana dubawa Manyan biscuit ne da tarin chocolates masu dadi.........leda biyu taci ba biscuits din kafin ta fara shan chacolate din gabadaya hankalinta da tunaninta yana kansa. Sai da yaci abinci sannan samu damar yin wanka, yana fitowa daga toilet ta shigo dakin........ ya bita da kallon mamaki. Daburcewa tayi kafin tayi namijin kokarin aro jarumta kawai taje ta zauna gefan gadonshi tana ya mutse fuskarsa, ita kanta mamaki kanta takeyi to ya ta iya da abinda yafi karfinta.......Kafin ma yay magana ta riga shi, cikin shagwaba da so lallai sai ta kare kanta tace." Tsoro nake ji a dakin." Yace." Tsoro kuma yau kwananki nawa a gidan nan ba kiji tsoro ba sai yau."? Ta daga kai da fadin." Kullum idan dare yay da kyar nake bacci dalilin motsin da nake ji kawai dai banyi magana ba ne " Girgiza kansa kawai yay sam bai yarda da wannan maganar ba, kawai ta fadi hakane saboda wata manufarta, sai kawai ya bagarar da maganar da fadin." Yanzu muka rabu da Mutuminki yace yana gaisheki." Ta d'anyi murmushi da fadin." Ina amsawa." Shiru dakin yay babu wanda ya sake magana a cikinsu..........Shi yana ta hidimar shirya jikinsa ita kuma ta kura masa ido tamkar kura ta samu nama. Ya juyo suka had'a ido da sauri ta kawar da kanta tana sauke ajiyar zuciya......Murmushi yay kawai ya kama hanyar fita shi ya san abinda ya shirya mata. Tsuru! ta zauna ita kadai a dakin tana sake-sake anya kuwa bata tafka wauta ba, ta lura kamar ya fahimci abinda takewa shiyasa yake mata wulakanci. Taji wasu hawaye masu zafi suna shirin kwace mata, bata ta'ba tsammanin zata dinga bibiyar namiji irin haka ba..................Garin ne ya rikice hadarin dake kwance ya tashi, iska da walkiya har cikin d'akin, da alama ruwan sama ne zai sauka. Falon ta bishi, nan ta sameshi kwance saman kujera da wayar a hannunsa yana dubawa.......Motsin zamanta a kusa dashi ya sanya shi tashi zaune yana kallonta da fadin.'' Ke har yanzu baki kwanta wai me kike so ne."? Taji wani 'katon abu ya tsaya mata a wuya, wai me yasa yake so ya mayar da ita wawuya ne........Amma ta san abunda za tayi masa. Ba tace masa komai ba kawai ta cire hijab din jikinta, yay sauri