← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 97

Sashe 31

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

akwai gidadanci da 'kauyanci a tare dashi wannan dalilin da yasa na tsaneshi! nake jin kunya a danganta shi dani a matsayin mijina, bayan haka bashi da wata makusa a suffar sa." Tsaki taja da fadin." Wallahi kin bani haushi sai maganar suffa kike suffarsa ta banza da wofi, me za kiyi da suffarsa ai yanzu ba'a duba wannan, gabadaya mata sun gane sunyi wayo yanzu basa yarda su kai kansu gidan wahala, ni nan da ki gan ni ba zan ta'ba yarda na auri talaka ba wallahi mai kudin gaske zan aura koda kuwa ya kasance tsoho tukuf babu ruwana da tsufansa kudinsa nake bukata ya fadi ya mutu na samu rabona, idan kuma bukatar namiji ta kamani na fita na samu wanda zai biya min bukata, abunda duk gasu nan mazan da kudi ko babu zasu gamsar dake amma duk kin damu mutane da maganar suffa da kyau, nan gaba kadan ina kyautata zaton kyawunsa ne zai rinjayeki ." Girgiza kai tayi da fadin." Baki fahimci magana ta bane shiyasa kike ganin kamar nan gaba zai iya jan ra'ayi na, kawai dai ina fada miki abinda yake zuciyata ne." Tabe baki tayi da fadin" Ke nifa ban yarda ma dake ba wallahi anya kuwa babu soyayya ba'kauyen nan a cikin zuciyarki, ni dai nasan mutumin da kake qi ba zaka zauna kana kwarzanta shi ba." Cikin takaici da jin haushin maganarta tace." Sakina mu bar maganar nan haka kada ki 'bata min rai, tunda dai kin kasa fahimtata shikkenan bana so mu rabu da bacin ran juna." 'Yar dariya tayi da fadin.'' Kada kiyi fushi k'awata tsokanarki nake yi amma don Allah bari nai miki wata tambaya." Ba tare da tace komai ba ta zuba mata ido tana sauraranta. Tace." Shin wanda za'a aura miki din mutumin wane gari ne."? Jim tayi tana tunani kafin tace."Mutumin Katsina ne cikin wani karamin kauye dake karamar hukumar malunfashi, duk wani binkice daya cancanta Maimartaba yayi akansa da iyayenshi basu da wani aibu kaf family nasu mutanan kirki ne, sai talauci da yayi musu katutu! kaf d'insu matalauta ne asalin sana'ar mahaifin shi korar jakai, yanda Maimartaba yake fada mana shi kansa Umar din be taso da mahaifiyarsa ba sai kakarsa wannan shine abinda na sani. Tace."Okay yanzu dai idan na fahimta can k'auyen zai kai ki ya ajiye."? Girgiza kai tayi da fadin." Aa na fada miki yanzu yana aiki a karkashin gomnati a matsayin jami'in tsaro, ya samu daukaka sosai dalilin jarumtarsa wannan dalilin yasa gomnatin mallaka masa gida tare da abubuwan more rayuwa yana nan tare da kakarsa a gidan. Murmushi tayi da fadin." Akwai hanyoyi masu sauki da za kiyi amfani dasu ki cuzgunawa rayuwarsa, ki hana shi jin dadi, sannan ki hana shi zaman lafiya, ni zan zan baki shawarwari masu kyau yanda za kiyi ki ha nashi kwanciyar hankali dashi da kakar tasa." Ajiyar zuciya ta sauke cikin jin sasauci tace." Nagode sosai k'awata. A daran ranar ta sake kiran wayarsa tun bayan kiran da tayi masa ya d'ankara mata magana mai zafi, to wannan karon a shirye take dashi tayi alkawari kan cewa duk cin mutuncin da yayi mata sai ta rama. Koda yaga kiran nata beyi kasa a gwiwa ba ya amsa cikin muryarsa mai cike da amo!! Ji tayi ta daburce sakamakon jin sautin maganarsa a kunnuwanta, da sauri ta aro jarumta kafin ta fara magana cikin Izzah! da isa! tace." Kana jina dai ko."? Ya maimaita maganar a fili da mamakin yanda take masa maganar gatsar kamar uwarsa. Be tanka mata ba kuma be kashe wayar ba. Ta sauke zazzafar ajiyar zuciya wacce taso ta jefe shi cikin wani yanayi yayi saurin janye wayar daga kunnashi, sai da ya daidaita nutsuwarsa sannan ya mayar da wayar kunnanshi da fadin." Ke nake sauraro." 'Karamin tsaki taja za ta cigaba da magana ya katseta da fadin." Na tsani wannan da'bi'ar taki ke kuma na fahimci abinda kika sa a gaba kenan rashin d'a'a da tarbiya, ayi miki magana kiyi tsaki! to kada ki kuskura kizo gidana da wannan da'biar zaki sha wahala a hannuna." Wani kuttun takaici yazo ya tsaya mata a wuya! wai gargadinta yake kamar wanda aka gaya masa cewa tana san zama dashi al'amarin ya bata mamaki mutu'ka ta daure ta had'iye bacin ran kafin tace." Magana nake so nayi da kai ni bakar magana nace ka gaya min ba saboda haka ina so ka tsaya ka saurareni." Ya kalli agogon dake kafe a dakin goma saura na dare dawowarsa kenan ya kwa'be kaya zai shiga wanka ta kira shi, yace." Ni nafi ki Uzuri wanka zanyi yanzu naci abinci na kwanta domin yau gabadaya a tsaye na yini ina bukatar hutu a halin yanzu saboda haka minti uku na baki kiyi sauri ki fadi abinda ke tafe dake ina sauraranki. Wata 'kwalla mai zafi ta ciko idonta, wai shin za tayi da wannan mutumin ne, wato bama shi da cikkken lokacin da zai saurareta. Hanci taja kamar ta fashe da kuka saboda tsabar bakin ciki da takaici tace." Matsalar kace wannan, abinda nakeso na fada maka shine ni ba zan zauna gida d'aya da kowa ba, idan wannan ne tunaninka sai ka sauya wani." Ya jima yana jajanta maganar a cikin zuciyarsa kafin yace." A yanzu dai baki isa ki tsara min yanda zanyi ba, ballanatana kuma kina k'arkashi iko na, kafin na san kowa a duniya Uwale na sani, saboda haka akan ki dai ba zan rabu da ita ba Ina tare da ita, duk inda nasa 'kafa zata ajiye tata, Idan kuma kina ganin zaki zo da gurin zama daga gidanku to ni zan baki fili ki dasa ki zauna ke kad'ai, amma ni ina tare da Uwale muddun rai insha Allah." Tace." Kana maganar nazo da gurin zama ai kasan nafi 'karfin wannan, kai ne matalauci ba'kon arziki da har kake wani tutiya! da arzikin gomnati, to shikkenan tunda kana ganin ba za kayi abinda nace ba, to kuwa kullum kana tare da bacin rai a cikin gidanka." Bata jira jin ta bakinsa ba tayi saurin kashe wayar tana wani irin numfarfashi irin na b'acin rai! *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 1/31/22, 17:50 - Buhainat: *GJSR* *47&48* Cikin tsantsar 'bacin rai da damuwa ya samu gefen gado ya zauna yana auna maganganunta, "Kai ne mataulaci ba'kon arziki wanda yake tutiya da arzikin gomnati to tunda ba zaka yi abunda nace ba kullum zaka kasance cikin bacin rai." Wa'innan maganganun sune kawai suke masa amsa kuwwa a kunne! babu shakkah auran wannan yarinyar bashi da fa'idah a gurinsa, Dole abunda yake gudu babu makawa sai ya faru, tun kafin ta shigo gidansa ga irin furucin da take a kansa da famliy nasa, Annabi SAW yace ku auri salihan mata masu hankali da tarbiya duk wanda yake so ya gina zamantakewar auransa dole ya cire son zuciya gami da rudin duniya ya nemi nagarta ya aura, yarinyar ta tara komai na hallita wanda zata iya ja ra'ayinsa amma ta samu nakusu gurin mugun hali da rashin tarbiya, tana ta'kama da kudi da mulki da suffar jiki, wannan dalilin yasa take ganin tafi karfin kowa babu wanda ya isa ya tursasata! dama haka rayuwa take, ya jima yana addua akan Allah ya arzurta shi da mace tagari dalilin tsoro da gujewa hallayarsu, hakan yasa be tsawwalawa rayuwarsa akansu ba duk da cewa yana da bukatarsu amma bai bari hakan yayi tasiri a zuciyarsa da gangar jikinsa ba, ya cigaba dai da addua da neman zabin Allah, sai gashi kuma Allah ya jarabceshi da auran yarinyar da kwata-kwata tunaninsa be kai kanta ba, hakika kowane bawa yana tare da jarrabawarsa...................babu shakka shigowar yarinyar rayuwarsa babban kalubane a rayuwarsa tunda ya fahimci cewa shaid'aniya ce bata k'aunar zaman lafiya da kwanciyarsa hankali, dole ya zage damtse a kanta ya nuna mata bambancin mace da namiji, babu ruwansa da mulki da sarautarta domin basu ne a gabansa ba, mutukar an d'aura auran nan to dole ta zauna karkashin ikonsa ko tana so ko bata so kuma ba zai yarda da shirme da shashanci ba, kullum maganarta bakin rijiya ba gurin wasan makaho bane to shine zai tabbatar mata da hakan daga zarar ta shigo gidansa zai nuna mata cewa ita ba komai bace a gurinsa. Da wannan tunanin ya shiga wankan yana sake jin tsanarta a cikin zuciyarsa duk wasu iskanci da take masa bai ta'ba jin haushinta irin yau ba, in banda hauka da jahilci waye yayi mai kudi da talaka idan ba Allah ba, maganar yana ci da gomnati ai halak yake ci ba sata yayi ba, to duk wannan ma bai dameshi ba sosai akan yanda take kokarin kafa masa dokoki wannan shine yafi 'bata masa rai! yana samun nutsuwa zai auri wacce zata kwantar masa da hankali yayi rayuwar jin dadi da ita wannan shine shawarar da ya yanke. ***** A cikin 'yan kwanakin da suka rage a daura auran gabadaya ta sauya tayi wani bal'in kayau na mussaman fatar ta tamkar kasa harshe ka lashe domin kyau da taushi sai sheki take saboda gyara na mussaman da Mamanta tasa ake mata, in ta zauna a guri kuwa har ta tashi kamshinta yana gurin, tasha gyara ciki da waje, wanda yake janyo mata feelings sa'i da lokaci shiyasa wani lokacin take fakar ido ta zubar da rabin maganin a toilet domin ita kadai ta san halin da take shiga idan sha'awarta tashi, Sosai ta jinjinawa mamanta ta kuma yaba da kokarinta a kanta, sai dai kash duk wannan gyaran da ake har yanxu zuciyarta ta nan a kangare bata jin za taje gidan mijin nata da sigar san zaman lafiya. Asp ya kira wayarta suka gaisa a mutunce da yake yanzu ta saki jiki dashi dalilin matarsa aunty Zeey kenan, suka dan ta'ba hira kafin ya shiga tsokanarta da fadin" Yau saura kwana biyu ki zama amaryarmu ina fatan dai yanzu kun sansanta da mutumin naki."? 'Bata fuska tayi tace." Asp ka daina yi min maganar wannan mara kirkin abokin naka saboda ya same ni a arha shine har
Chapter 31 · 0% Book details