← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 97

Sashe 44

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsigar jiki, wani irin rawa jikinta ya shiga yi. Ya d'an juyo da ita domin su fuskanci juna. Sosai tayi namijin kokarin kallonshi........wanda har yanzu babu riga a jikinsa sai dogon wandon uniform na d'in shi. Rintse ido tayi gabanta na cigaba da fad'uwa, rayuwarsu a daji ce ta fad'o mata a rai. Hannunshi ya d'auke daga kan fad'arta ya lalubi hannunta guda ya rike a nashi, Cikin taushin murya yace." Amaryata." Gwiwarta ta dinga rawa bata tsammanci haka daga gurinshi ba, ta dauka za su cigaba da rigima kamar yanda suka saba a waya sai kuma taga akasin haka, koda yake a cikin maganganun Asp ya sheda mata cewa abokin nasa zai gyara kuskuransa. Zuciyarta ce tai rauni! ta kasa hasala komai tana kallo ya ja hannunta har cikin dakinshi ya zaunar da ita gefan gado......Kafin yace." Abokina yace dani wai ya kawo min ke domin kiyi min tausa! ki kuma hada min ruwan wanka ni nace kam *wane mutum!* ai idan tausar ce ni ya cancanta nayi miki a matsayinki na gimbiya kuma amarya ko ba haka bane." Kallonshi tayi tana mamakinsa, kamar bashi ne wannan masifaffan ba mai ba'kar maganar tsiya. Kafin ta ankara taji saukar hannunshi saman bakinta, tayi saurin kawar da kanta, bata yarda ta sake kallonshi ba, abun nasa kamar yana kokarin wuce gona da iri. Ganin yanda tayi rauni da yawa! yasa ya rabu da ita ya shige toilet din ya bar ta da mugun mamakinsa. Tana nan zaune ya fito daure da babban towel a jikinsa da wani karami a hannunsa yana goge kanshi. Ido suka had'a kawai ya sakar mata murmushi wanda yay masa bala'in kyau. dimples a kumatunsa sai kace mace..............*"GIMBIYA TA.* Ta ji wani iri a tare da ita, tana bala'in jin dadin ya kira ta da wannan sunan kamar a bakinsa aka kirkira. Kusa da ita ya zauna da man shafawa a hannunsa.......Saurin janyewa tayi saboda kusancin nasu yayi tsanani har yanzu mamakin al'amarin take mutum sai kace aljani, koda yake dama dasu yake tu'ammali. Da wayo da wayo sai da ya sake nani'karta ya mika mata man shafawar da fadin." Ki sha min a baya na duk da na san nayi tsaurin ido amma ina neman alfarma." Ta kalleshi a karo na farko da tayi magana tun bayan shigowarta............."Da can waye yake shafa maka, nima da kaina nake shafa abina don haka kai ma sai kayi dubara ka shafa abunka." Ya sake kusantar jikinta sosai yace." Ni nake shafa abina yanzu ganinki a zaune a kusa dani yasa nake miki sha'awar samun lada daga yau duk wani hidima da zakiyi min Allah zai baki lada mai yawa kuma zan d'aga miki 'kafa ki shiga aljanna da ikon Allah." Gabadaya ya gama kashe mata jikinta, ta dinga kallonsa tana tunanin wasu abubuwa a kanshi. Man shafawar ya mi'ka mata da ido yay mata nuni. A sanyaye ta kar'ba ta lakato a hannunta tana mutsikawa, ta rasa ma yanda tayi ta kai hannu jikinsa, sai mutsika man take a tafin hannunta. Hannunta ya kama ya dora a kan cinyarsa da fadin." Tunda ba zaki iya shafa min a baya na ba, shafa min anan." Da sauri ta cire hannunta tana galla masa harara! Zumbura baki tayi da fadin." Ni wallahi ka takura min, abinda banyi niyya ba." Yace." Ba kya san shiga aljanna madawwamiya ko."? Shiru tai tana cigaba da mutsika man a hannunta duk ta zama wata iri sakamakon abinda yake tsiro dashi, banbarakawai! Ganin taki tayi abinda yake so yasa ya kyaleta yana nazari da tunanin hanya ta biyu da zai bullo mata. Tsaf ya shafe jikinsa da mai dama neman fitina ne kamar yanda ta fada da can waye yake shafa masa. Ba ta sake kallonsa ba har ya gama shiryawa yana fesa turare, kira ya shigo wayarsa. Ya dauki wayar yana dubawa. Gefan da take zaune ya kalla akayi katari suka had'a ido! bece komai ba ya janye idonsa tare dasa wayar a kunnashi. "Hamra'u ke za'ayi wa bangajiya ai na samu sashena tsaf yana kamshi mai dadi na kuma ga daining cike da abinci iri-iri sannu kokari nagode sosai." da wannan maganar ya fara. Jin ya ambaci sunan yarinyar yasa tai saurin kallonshi, wayarsa yake hankalinsa kwance ga wani murmushi na mussaman a fuskarsa. Mugun haushinsa ya turnuketa shin wai me yake nufi ne.? "Bana bukatar komai Hamra'u hutu kawai nake bukata kuyi hakuri da safe zan shigo mu gaisa sosai gaisuwata dake ta mussaman ce." Daga daya bangaran tace."Shikkenan Yaya na, amma zan so nayi tozali da kyakykyawar fuskarka dawowarka ta sanya ni farin ciki da wuya yau na iya rintsawa." Farin ciki ya cika masa zuciya, a rayuwarsa yana masifar son kulawa da soyayya da kuma iya kalami ta inda yarinyar ta siye zuciyarsa kenan. Yana 'yar dariya yace."Ki kwanta kiyi barci zan zo miki a mafarki kar ki damu akwai amana a tsakanin mu." Be ji amsarta sakamakon jin bugun kofa kafin yai aune har ta fita, da sauri ya cimmata tana kokarin bude kofar falon ta fita. Hannunta ya rike tare da zuba mata idonsa yace." Ina zaki je kuma."? Sosai ta daure tayi jarumtar danne masifaffen kishin da yake taso mata......"Sakar min hannu bana san damuwa zanje na kwanta dare yayi." Ya girgiza kanshi da fadin." Asp ba haka yace ba, cewa yay ki kwana anan kuma ya sheda min cewa ka da nayi miki da k'arfi ma'ana na bi komai sannu a hankali." Sai ta rasa inda maganarsa ta dosa....."Kada nayi miki da karfi na bi komai sannu a hankali. sai yanzu ta fahimci abunda yake nufi.....Kallon banza tai masa kafin ta fizge tana jan tsaki! bude kofa take kokarin yi ya janyo ta da 'karfi! rumgumeta yay tsam a jikinsa tare da dora hannuwansa kan mazaunanta ya riketa da kyau! Ita dashi wani irin numfashi suka sauke sakamakon had'uwar jikinsu, gabadaya sai suka kama kyarma (rawar dari) kamar masu jin sanyi, ya wani 'kam'kamta a jikinsa yana sassana kamshin dake fita a jikin gashin kanta. Duk kokarin da tayi gurin ganin ta rabu da jikinsa abun ya gagara domin da kyau ya rik'eta! kafafunta suka dinga rawa! sam ba tayi tsammanin wani al'amari makamancin wannan za ta faru a tsakaninta dashi ba. Kalaman b'oyayyan masoyinta ne suka fara dawo mata a kunne........."My love ki rike min amana kada ki bari wani abu ya shiga tsakaninki dashi, baya sonki ni nake miki sasihin so ba zan bari ki wulakanta ba." Tuna wannan yasa taji wani karfi yazo mata, tabbas da akwai dalilin da yasa yake so ya raba da budurcinta idan ba haka ba me yasa da ganin sarkin fawa sai miya tayi zaqi, gashinan a gabanta yana waya da yarinyar da yake so." Tsananin sha'awar da ta taso masa ita ta sanyaya kuzurin sa, dalilin kenan data samu nasarar kwace kanta a hannunshi. Ta kalleshi cikin 'bacin rai tace." Wato abunda kake nufi kenan! kana rawar jiki zaka more ko? to ba zaka samu abunda kake so ba a tare da ni domin duk na fahimci in da ka nufa, kaje ka sauya wata dubarar domin na fahimci wannan." Cikin zafin nama ta kama hanyar fita bayan ta gama maganarta. Kafin ta fitan ya ritsa ta..............danneta yayi sosai a jikin bango(garu) ya zuba mata jajayen idanuwansa da suke cike da tsananin sha'awa, shi kansa ba a son ransa yake aikata abinda yake ba, duk cewa yarinyar halalinsa ce amma ba yanzu ya shirya kusantarta ba. Mayataccen kallo yake mata irin na kurrula wanda ya kassara mata duk wata gaba ta jikinta, ita bata ta'ba ganin mayata irin ta yau ba, shin wai me yake shirin faruwa ne.? Hannu yasa ya tallafo fuskarta ya tsirawa bakin ido! Gabanta ya dinga bugawa! ganin yana kusanto da fuskarta kusa da tata. Kokarin kawar da kanta take ya rike fuskar da kyau! duk dubarar ta, sai da ya samu nasarar had'a bakinsa da nata............Harshenta kawai ya cafka ya fara tsotsarsa kamar wanda ya samu alawa. Shi yake jin dadin kiss din amma ita kuwa gabadaya bakinta da harshenta rikicewa yay da wani irin zafi na rashin sabo. Wani irin dadi yake ji sakamakon tsotsar bakinta, duk ya shanye mata yawun bakinta dole haka ta hakura ta dinga kar'bar nasa yawun tana shanyewa amma ba dan ranta yaso ba sai dan ba yanda za tayi. Sosai ya galabaitar da ita kafin ya cire bakinsa daga nata. Kuka ne ya kufce mata kawai sai ta shiga rerawa kamar ta dora hannu aka tayi ta kurma ihu!! Hannunta ya riko, ya fara janta domin shiga daki. ta turje tana komawa baya tare da rike lalube, sosai take kuka hawaye duk ya jik'a mata fuska, mutukar ta yarda ta bishi dakinsa zai samu nasara a kanta, shine dalilin da yasa take turjewa, da fadin. "Wai meye hakane ka sakar min hannu na tafi guri na wannan ai wulakanci ne na gaji da abinda kake min." Kansa ya shiga girgiza mata alamun ba zai yi abinda take so ba. Tace." Wallahi ba za ka samu abunda kake so ba dan iska kawai." Kalmar tai masa ciwo amma sai ya danne domin tafadi wacce ta fita muni a kansa. lallai yau zai nuna mata kalar iskancinsa. Ta dinga dukan hannunsa tana komawa baya kawai sai ya sa'bata a kafad'a! ya tallafe mazaunanta, kai tsaye dakinsa ya nufa da ita sai duka da cizo da yakushi take masa amma ko gezau! wata irin power da fitina yake ji. Saman gado ya jefar da ita ya tsaya a kanta da fadin." Kin jima kina zagina tare da kira na da kalmomin 'batan ci, iskanci ba hali na bane amma yau zan gwada miki shi." Hanyar fita ya nufa ta bishi da wani irin kallo na fargaba da tashin hankali, tana jin sanda yake murzawa kofar key daga waje, taji kamar tace wayyo Allah ta shiga uku. wace irin masifa ce wannan ace mutum daga dawowarsa ko hutawa beyi ba zai fara wani abu, gaskiya tayi mamakin hakan kuma ba tayi tunanin faruwar hakan da wuri ba, koda yake wani irin shaid'anin mutum Allah ya had'ata dashi wanda duk tsanani ba'a iya gane kansa "Kada ki kuskura ki yarda dashi akwai manufarsa a kanki." Zuciyarta ce take bata wannan shawarar,
Chapter 44 · 0% Book details