← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 97

Sashe 71

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan......Wa'inda basu santa ba tambaya kawai suke "Wannan ce matar UMARU."? Uwale na basu amsa daidai da abunda suka tambaya. Ita dai kasa tsayuwa tayi kawai tabi bayansa dakin da taga ya shiga. Hamra'u na dakin sai share-share take.......Yanayin dakin ya nuna nasa ne tun lokacin samartaka duba da irin tarin kayan farauta da suka rataye a bagon dakin da kuma tarin buhun-buhun magungunan gargajiya irin wanda yake bayarwa. 'Kura duk ta tashi a dakin sakamakon rashin gyaran da bai samu ba tsayin watannin da suka wuce. Taja ta tsaya bakin k'ofar tana mata wani irin kallo, wallahi bata ta'ba ganin mara zuciya irin ta ba, kullum cikin bautar namijin da babu guarantee akansa. Ganin yaki mata magana yasa ita ta magantu tace." Kin ga ya isa haka don Allah! mutumin da ba zama yazo ba meye zaki damu kanki gurin gyara masa daki, ko kin manta yau zai tafi." A sanyaye Hamra'un ta kalleshi wai ko zaiyi magana, Uffan bece ba shima so yake ta fita ya samu sararin busa hayak'insa. Jiki babu kwari tazo za ta wuce da tsintsinya a hannunta, hanya ta matsa mata har yanzu kallon shashasha take mata, to idan ba haka ba akan me zata dinga wahalar da rayuwarta. Ta fita daga d'akin ya fito da shishar ya fara tada hayaki! Ta kalleshi da fadin." Ni ce marainiyar wayonka ko.''? Ya kalleta tare daso tayi masa karin bayani. Murmushin takaici tayi kafin tace." Ka b'oye ashararanci da kake a idon duniya saboda gudun abun magana amma da yake ni ka mayar dani towon tushe baka jin kunyar aikata abu mara kyau a gabana." Ya fesar da hayakin dake bakinsa kafin yace." Kwalbar giya ki ka gani a hannuna."? Tayi shuru tana kallonsa Yace." Wannan da yake hannuna! bashi da lada ko zunubi! sanya kai ne ga wanda yake da ra'ayi kuma bana sha sai irin haka ta faru, ko kin ta'ba tsintar karan Sigari a aljihun rigata."? Ba tace komai ba tana dai ta nazari da tunani a kansa. Yayi murmushi da fadin." Ko kin manta kalmar da take cewa (Mata sirrin miji) kece sirri na kuma ina da ta tabbacin cewa duk rintsi duk wuya zaki rufa min asiri a kowane hali, akwai bambanci sosai a tsakaninki da Hamra'u." Maganganunsa suka kashe mata jiki, ta dinga kallonsa tana sake jin kaunarsa na ratsa sassan jikinta. Da hannu ya nuna mata kusa dashi da fadin." Zo ki zauna kusa dani sanyin idanuwana." Murmushi tayi kafin ta nufi gurin ta zauna kusa dashi da fadin ." Dubi jikinka yanda ya 'baci! kayi wani dukun-dukun! sam wannan rayuwar ba ta dace da kai ba." Ya ajiye abunda ke hannunsa gabadaya ya mayar da hankalinsa kanta, yace." *ZINA* ina so ki fahimci wani abu, wannan abun fa ya kai matakin da ba za'a iya raba ni dashi ba, ya riga ya zama jiki da Jinina! duk sanda tsumin ya tashi bana iya sarrafa kaina, tun ina yaro nake shan magungunan tauri! a cikin dabbobin da Allah ya hallita masu rai kad'an ne ban ci ba. nayi gwagwarmaya da jinsi mutum da aljanu domin har so sukayi su bude min ido! ni ne ban bada goyon baya amma duk da hakan wani lokacin idan sun so suna ziyartata muyi hira su tafi salin alin ba tare da sun cutar dani ba.... babu tabbas akan aljani kuma ba'a yarda dasu amma ni bana tsammanin cewar zasu cutar dani da duk wanda ya shafe ni, dalili musulmai ne kamar yanda nake musulmi saboda haka ki kwantar da hankali kisa a ranki cewa ni ne abokin rayuwarki." Gabadaya jikinta ya mutu jin abinda yake fada........Dama ta jima tana zarginsa cewa bashi kadai yake rayuwa ba akwai masu taimaka masa. Ta rasa wane irin tunani za tayi a kansa. Yace." Bayan sallar la'asar za mu tafi gida bana tsammanin barin ki a garin nan." Wani bala'in dadi y rufe ta, amma bata nuna masa ba tace." Saboda me."? Shu'umin kallo yayi mata kafin yace." Ba zan iya bacci ba yau saboda sha'awar dake damuna kwana biyu kina fushi dani kin daina kwana a dakina." Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da yatsun hannunta. Hannu yasa ya daga fuskarta, wanda yayi daidai da shigowar Hamra'u dakin tana sheda masa ruwan wankan data dora masa yayi zafi." Hankalinsa gabadaya yana kan matarsa ya amsa da" Okey to na gode kanwata." A sanyaye ta saki labulan d'akin, zuciyarta kamar ta fashe sakamakon abunda ta gani a tsakaninsu. Yana fitowa daga wankan Uwake ke sheda masa cewa Kawunan sa suna son ganinsa......Yace." Babu damuwa yanzu zai shirya yaje ya samesu. Ya shiga dakin ya sameta a kwance saman katifarsa sai juye-juye take cikinta ne yake ciwo ga yunwa na damunta. Cikin kulawa yace." Zina akwai abunda ke damunki amma idan na tambayeki sai kice babu komai." Tana ya mutse fuska tace." Ciki na ne yake ciwo idan ba amai nayi ba to ba zan ji dadi ba. Girgiza kansa yayi da fadin." Sannu Allah ya sawwake me kike bukata idan na fita na kawo miki kin san muna da komai na gargajiya." Tace." Goba da mangaro amma irin wa'inda basu nuna ba." Yace." Shikkenan."? shuru tayi na minti biyu kafin tace." Meye ma sunan abun."? 'Yar dariya yayi kafin yace." Agwalima kuke ce masa ko."? tace." Yawwa dashi da kuma Magarya." Yace." An gama ranki ya dad'e! amma gyad'a marau-marau fa." Dariya ya bata kafin tace." Ina so." Yace." To insha Allah zan kawo miki, ki kwanta ki huta yanzu ni zanje gurin. Iyayana suna nema na.". Tace." To babu damuwa a ce ina gaishesu." Yana kokarin fita ya amsa da zasuji insha Allah." Yayi wa Uwale sallama lokacin tana kicin tana aikin soye-soye......da yake tana da irin kaji na hausa wanda take kiwo a can baya, sai ta bar su a hannun Tasallah shine fa tasa aka yanka mata guda biyar aka gyarasu tsaf ta kawo mata tare da duk abun bukata... *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/14/22, 10:51 - Binta: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *105&106* To shima nashi 'bangaran abinda yake faruwa kenan, domin tun bayan ya sauka gida yake kiran wayarta abun ya gagara, da ta fara shiga sai ta katse ya kira ya kai sau goma bai samu biyan bukata ba, sai kawai ya ajiye wayar ranshi gabadaya a 'bace yaso kafin ya kwanta yaji lafiyarta da ta babynsa dake kwance a cikinta, haka kawai yake tausaya mata, ya san duk wani abu da take daurewa take akan ta nuna masa kaunar 'yan uwansa, kuma abunda tayi ya siya mata kima da daraja a idonsa, ya sake jin sonta ya k'aru a zuciyarsa. Da tunaninta ya kwana ya kuma tashi dashi, wannan dalilin ne yasa yana dawowa daga massalaci ya dauki wayarsa ya kunna, ya fara laluben number ta, cikin ikon Allah sai ta kira shi, a jiyar zuciya ya sauke mai sanyi kafin ya sanya wayar a kunnansa da sallama a bakinsa. Ta amsa a sanyaye tana dan gyara kwanciyarta, yace." My GIMBIYA fatan kin tashi lafiya ya kwanan bakunta."? Tace."Lafiya alhamdullihi na kwana da tunaninka da kewarka rashin kwanciya a kirjinka ya janyo min ciwon jiki." Ya lumshe ido yana jin wani feeling na taso masa yace." Me yasa ki ka takura kanki lallai sai kin kwana umm? saboda na san hakan zai faru ya sa na sauya shawara, yanzu na gamsu da kaunar da kike a kaina da family na. Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace." Nifa ba'a takure nake ba, domin yanayin garin ya burgeni sosai da zamu dawo garin da zama da hakan yayi min dadi." Tafad'i hakane kawai ba har can cikin zuciyarta ba. Aikuwa yaji dadin maganar yace." Tunda yanayin garin yayi miki dadi zamu dinga zuwa hutu ko? zan gina miki gida mai kyau." Tayi 'yar dariya da fadin." Naji dadin hakan mijina." Yace." Ya babyna ina fatan yana lafiya."? A shagwabe tace." Jiya tun bayan da kuka gaisa dashi ya dameni da k'iriniya sai motsi yake min." Dariya yasa da fadin." Yana bukatar mu sake gaisawa sosai dan jiya baki sakar min jiki mun gaisa yanda ya dace ba, amma ki bashi hakuri kafin mu had'u." Itama dariyar take kafin tace." Aa ni babu ruwana idan kun had'u sai ka bashi hakuri dan da alama yayi fushi tun wayewar gari beyi motsi ba." Gabansa ya fad'i! da sauri yace." Beyi motsi ba fa ki kace."? Ta dora hannunta a saman cikin tana shafawa kafin tace." Eh mana ya tattara a guri daya kamar bashi da lafiya." Gabad'aya yaji hankalinsa ya dawo garin yace." Ganin tafe insha Allah." Da sauri tace." Laa da wasa fa nake maka."? Ya 'bata rai da fadin." ZINAT an ta'ba wasa da lafiya ashe.'? Jin yanda yayi maganar babu wasa yasa ta zama serious tace." Allah tsokanarka nake yanzu haka ma motsi yake yaji muryarka." Ajiyar zuciya ya sauke da fadin." Saboda kin ga na damu shiyasa zaki mayar dani shashasha ko.''? Kunshe baki tayi tana danne dariyar dake kokarin subce mata, tace." Kayi hakuri Darling." "Um-um! naki hakurin." Cikin shagawaba yayi maganar.........Tace." Dan Allah fa." Yace."
Chapter 71 · 0% Book details