← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 97

Sashe 42

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shi yanzu domin naji komai daga bakinsa." Still ba tace masa komai ba har ya gaji ya kashe wayarsa, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tare da cire wayar daga kunnata. ta a jiye saman drowar, kwanciya tayi ta lumshe idonta kawai ta shiga tunanin abinda zai faru a tsakaninsu idan ya dawo gidan. Koda Asp din ya kira shi cikin mutumci da dattako suka gaisa kamar koda yashe, Asp din ya tambayeshi yanayin aikin da kuma maganar dawowarshi gobe, yace." Na kammala komai cikin nasara da sahalewar ubangiji kuma insha Allah gobe iwar haka na sauka da ikon Ubangiji. Yace." Alhamdullhi masha Allah, mutumina na taya ka murna da samun cigaba a rayuwa Allah kuma ya sauke ka lafiya." Cikin farin ciki ya amsa da ameen ya Allah mutumin kirki nagode kwarai." Yace." A babu komai fa abokina idan nai maka addua da fatan alkairi ai kamar kaina nayi wa sai dai kuma hanzari ba gudu ba, yanzu-yanzu na gama waya da mutuniyarka." Jin abinda yace yasa ya d'ora idonsa kan agogon dake kafe a dakin, goma da rabi na dare, sai ya shiga mamakin dalilin da yasa ya kira ta acikin wannan daran, be yarda da abinda zuciyarsa take raya masa ba, yace." ta kawo maka 'kara ta kenan."? Murmushi yay da fadin." Kwarai kuwa UMARU a gaskiya idan baka sauya halinka ba zamu 'bata domin ni yanzu gabadaya na daina ganin laifin yarinyar nan laifinka nake gani." Cike da mamaki yace." Wannan ya nuna min cewar kana goyon bayan duk iskancin da take." Yace." Ba nufi na kenan ba, na san abinda take bata kyautawa, to amma ni nafi yarda da cewa kaine kake janyo duk abunda yake faruwa me yasa ba zaka rarrasheta ba; me yasa ba zaka dinga tausasa harshenka gurin yi mata kalami ba? nasha fada maka cewa mata wasu irin hallita ne masu wuyar sha'ani amma daga ranar daka gane hallinsu to za kaji dadin zama dasu, domin suna da dadin sha'ani da kuma saukin hali, me yasa kai baka daukar shawara ne."? Asp yana da 'kima da daraja a idonsa, wannan shine dalilin da yasa ya dinga tausar zuciyarsa kada ta tunzurashi aikata abinda zai janyo musu samun sa'bani da juna, bayan haka kuma wannan gantafalfalar yarinyar bata isa ta shiga tsakaninsa da amininsa ba, hakuri ya bawa zuciyarsa dake turari! gami da jin kishi-kishin Asp din domin haka kawai yake jin haushin kyakykyawar fahintar dake tsakaninsa da yarinyar wanda hakan ya janyo yazo yana gaya masa magana a kanta..........Ajiyar zuciya ya sauke da fadin."To Naji na dauki laifina domin a yanzu yanda kake a tunzure ko nayi maka bayani ba zaka fahinta ba, okey komai zai yi dai-dai kamar yanda kake so, zan kuma yi kokarin ganin na gyara kuskura na." Asp din yace." Yawwa to ko kai fa mutumina, ni wallahi banga abin gudu a tattare da yarinyar nan ba, a ganina kai da kanka zaka sauya mata hallaya kada ka manta kuma bata da kowa a garin nan sai kai da family naka sai kuma mu da muke abokanan arziki." A d'an tunzure yace." Asp maganar nan abar ta haka don Allah, nace naji na kar'bi laifi na zan gyara kuma shikkenan ko."? Yace." Shine abinda nake bukata a tare da kai, ka dawo gida naga sauyi daga gareka." Shuru yay masa yana jin wani irin abu na sukan zuciyarsa, a duk sanda Asp din yake nuna kulawarsa akan yarinyar yakan ji abun ya dame shi a ransa, sai yayi auziyya ya kori shaidan din dake kusa dashi tukkuna yake samun sassauci, shi kansa be san me yasa yake tsananin kishin yarinyar ba. *Kika futar min da littafi keda Allah! ki ka karanta baki biya ba kema keda Allah!* *#500via.....0542382124.....Binta umar gtbabk, idan kati zaki turo kiyi min magana ta WhatsApp da wannan number.... 07084653262.....BINTA UMAR ABBALE* 2/9/22, 10:22 - Binta: _*GOJE!! _*Ya dawo!! ga Akuya ga kura!! tofah! 'ka'ka-'kara-'ka'ka-tsara!! A yanzu ne labarin zai fara....! Na jima ina rubuce-rubuce amma ban ta'ba rubuta littafin daya dauki hankalina irin wannan ba, dalili littafin yazo da sabon salon da ba'a ta'ba yin irinshi ba, bahaushe yace yabon kai jahilci a wannan ga'bar dole na jinjinawa kaina gurin rubuta littafin farauta ba tare dana shirya hakan ba, Tirk'ashi idan ana dara fidda uwa ake, shin wai ina labarin uban daba ne? ina nufin (mashekin daji) wanda Ubana UMARU ya samu nasarar sare masa hannu guda akwai badakala anan gaba.......GOJE ya dawo cike da nasarori masu yawa shin ya zaman auran su zai kasance da 'yar rigimarshi wato GIMBIYA ZINATU, wanda Tun a daji suka fara son junansu amma dukkaninsu sun 'ki gazgata cewa suna son junansu to zamu ga yanda game d'in nasu zai kasance tare da boyayyan masoyinta shin a tsakanin waye zai saduda kowa dai ba kanwar lasa bane..........! Domin samun damar shiga paid group....#500 0542382124.....Binta Umar gtbank. Idan kati za'a turo sai ayi min magana ta WhatsApp da wannan number...... 07084653262......BINTA UMAR ABBALE *61&62* *GJSR* Wayewar garin ranar da zai dawo tun safe gidan ya fara cika da mutane yan uwa da abokan arziki daga can garinsu, yaran shi ma kaf sun hallara, jiran saukar sa kawai suke, hayaniyarsu har part d'inta, ta dinga mamakin al'amarin, Baraka ce take shaida mata cewa ai ba'ki akayi a gidan, kuma da alamar su mutanan k'auye ne, jim tayi tana nazarin meye dalilin zuwansa, wani sashe na zuciyarta ya tunasar da ita cewa sun zo tarar d'an uwansu ne, kasancewar a cikinsu shike da kumbar susa shine dalilin da yasa suke tururubin zuwa gidanshi. Tsaki taja a fili tace." Duk inda d'an kauye yake sai ya nuna halin dabbanci." Ta kalli Barakan dake zaune a gefanta tace." Ki sheda musu cewar hayaniyarsu tayi yawa su rage." Ta amsa kafin ta yun'kura ta mike kai tsaye hanyar fita ta nufa. Da yake a 'bangaran da suke zaune ba'kin suka sauka, kai tsaye can ta nufa. aikuwa ta samesu sunyi kaca-kaca da guri sunci abinci duk sun zubar sai dirkar lemon roba suke da sun shanye sai su ajiye su dauki wani, lemo da ruwan kusan kwali biyar aka a je musu amma sun shanye saura kadan. Sosai ta cika da mamakin yanda ta gansu mazan da mata sai hira suke suna shewa kowanne rike da robar lemo a hannu. Tayi musu sallama suka amsa tace." Dama sa'ko ne daga matar gidan wato Gimbiya Zinatu tace na sheda muku cewa hayaniyarku tayi yawa ku tak'aita." Sai suka hada baki gurin fadin." To shikkenan amma dai mutum da bakinsa ai ba za'a ha nashi magana ba ko."? Tace." Eh itama ba tace kuyi shuru ba cewa tayi ku rage hayaniya." Wasu daga ciki suka amsa sauran kuwa shewa sukayi irin ta shakiyanci suka fara kuskus da yawa daga cikinsu mutanan 'Dayyiba ne wato mahaifyar Hamra'u, domin ita bata samu damar zuwa ba, sai ta tura wakilai domin dauko mata rahoto. Tun kafin ya sauka ya samu labarin tarin jama'ar dake jiransa, sosai yay farin cikin hakan ya kuma dinga Allah-Allah ya sauka domin haduwa da 'yan uwansa wanda bashi da kamarsu. Uwale da kanta ta jagorance su duk yawan su maza da mata suka nufi sashen Gimbiyar. Suka cika falon duk girmansa ko wanne sai zare ido yake da kalle-kalle falon ya dumame da wani irin wari da tsami mara dadin ji!! Marakissiya ce ta shiga ta shiga ta sheda mata cewa tana da baki. Koda ta fito ta riske su jigum-jigum! a zaune ga tsami da hamami! ya cika mata falo, ranta yay masifar b'aci, toshe hanci tai ba tare da tace musu komai ba ta juya da sauri ta koma daki.................A gaggauce ta nufi toilet ta dinga kwara amai! wanda ta kasa tantance na meye, ta dai fi zargin warin data sha'ka ne. A galabaice ta fito ta zauna kan Sofa tana mayar da numfashi, ita kanta ba ta ji dadin faruwar hakan ba, sai dai ba yanda za tayi ta iya zama a falon yana wannan uban warin! Uwale kuwa kunyar duniya ce ta isheta ta kalle su suna zaune har yanzu sai dai akwai alamun 'bacin rai a tare da wasu mussaman Kawun sa wanda suke 'yan maza zir da mahaifinsa. Ya kalleta da fadin." Uwa le wannan yarinyar i ta ce matar UMARU."! Tace." Eh ita ce kuyi hakuri da abunda ya faru. Kawu Ado ya girgiza kansa rai a bace yace." Babu shakka albasa ba tayi halin ruwa, yanda muke jin labarin mahaifinta a duniya mutum mai nagarta da dattako, bashi da nuna bambanci ko 'kyama ga al'ummah! yana da kyauta da sakin fuska, kowa nasa ne, tabbas da yarinyar nan ta gaji halin mahaifinta to da ba zata tozarta dan adam ba, amma babu komai. saboda nagartar Mahaifinta za'a zauna da ita amma dole sai UMARU ya auri za'bin mu matar da zata girmama ta kuma mutunta mu." Gabad'aya suka amsa da fadin." 'Kwarai wannan hukuncin shine dai-dai Kawu." Ya mi'ke tare da basu Umarnin tashi su fita, gabadaya har ita Uwalen suka fita duk jikinsu a sa'bule. Kai tsaye sashen Uwalan suka nufa kowanne da b'acin rai a fuskarsa, ganinsu a sa'bule babu karsashi! ya sanya Hamra'u murmushi dama ai ta san za'a yi haka, da kamar ta hana Uwale jagorantarsu saboda ta san hali, to amma hakan ma babu laifi sun ga halinta a zahiri a gaba sai su kiyaye. To Asp da kanshi ya d'auko daga airport kai tsaye Headquarter 'yan sandan suka nufa, nan ya tarar da yanda abokan aikinshi da wakilan manyan manyan 'yan siyasan da sukayi dafifi gurin taron shi, yaji dadin hakan sosai, ya saki fuska yana gaisawa da kowa, sai fatan alkairin suke masa yana amsawa da farin ciki a tare dashi, a zahiri yana ganin 'kauna tun daga kan abokan aiki da kuma jama'ar gari. A takaice suka tattauna da Commissioner kafin ya bashi hutu na sati daya, Asp yace." Ranka shi dade ango ne fa, ya kamata a bashi hutun wata guda ya huta sosai ya kuma ci angoncin sa a tsanake." Cike da barkwanci yake maganar. Yana 'yar dariya ya kalleshi da fadin." *GOJE* kaji abinda abokinka yake cewa." Murmushi yayi yana kallon Asp din yace." Hutun wata daya yay min yawa sai kace mace na dingi
Chapter 42 · 0% Book details