← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 97

Sashe 62

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

shin ita ya za tayi da wannan kaddarar....Mutumin data ci wahala a kansa ta b'ata lokacinta a kansa shine yake rayuwar aure da wata akan idonta...........Kanta ya dinga juyawa! take ta zube a gurin bata san in da kanta yake ba. Gigicewa sukayi gabadayansu mussaman shi ya kai ya kawo a gurin hankalinsa ya tashi ainun! bai san lokacin daya dauketa ba ya fita da ita Uwale ta rufa masa baya tana gyara yafan mayafinta. Tsayuwa kawai tayi a gurin tana mamakin abinda yayi. Yarinya baliga kuma ba muharramarsa ba ya wani dauketa har da mannata a kirjinsa........Takaici da bakin ciki kamar su kasheta, tayi kwafa tare da girgiza kanta, sashenta ta nufa tana tunanin irin hukuncin da za tayi masa idan ya dawo domin ita ba zata yarda da wannan iskancin ba. Abin mamaki! jininta ne ya hau sosai! lokacin da likita ke sheda musu hakan, abun sai ya basu mamaki! shin wane irin tunani yarinyar ta sa a ranta haka wanda har zai janyo mata hawan jini.....Ita dai Uwale ta zargi wani abu, shine dai har yanzu beyi hasashen cewa rashin adalcinsa ne ya janyo mata kamuwa da lalura ba. Da kanshi ya bukaci cewar ta kwanta a asibitin zuwa gobe domin ta sake samun sauki sosai, domin a zahirin gaskiya hankalinsa ya tashi da al'amarin, yana tsoron kada yar mutane ta had'u da lalura a hannunsa. Sai bayan isha'i ya bar asibitin.........Yana shiga barrack din Asp ya fito daga block d'insa da waya a kunnansa. Motar ya tsayar ya sauke gilashi yana kallonsa har ya k'are wayar ya mayar da ita aljuhu ya k'araso bakin motar . Hannu ya mi'ka masa suka gaisa kafin yace." Yanzu mutuniyar ta shiga gida ai ta jima a gurinmu kasan Zeey mutuniyarta ce." Yay jim yana kallonsa da nazarin maganarsa. Shima Asp din ya fahimci wani abu, sai jikinsa yayi sanyi yace." Akwai magana kenan dan naga kayi sak! kodai bata fada maka ba."? Bagarar da maganar yayi kafin yace." Ina cikin damuwa wallahi yarinyar nan Hamra'u ce take kwance a asibiti babu lafiya." Da sauri yace." Subahanallahi me yake damunta."? Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya furzar da wani irin huci daga bakinsa yace." Haka kawai ta yanke jiki ta fadi yanzu likita yake tabbatar min da cewa jininta ne ya hau." Asp din ya jima yana kiran sunan Allah da jimanta al'amarin.....Yace." Jininta ne ya hau akan wane dalili kodai tana da damuwa ne."? Yayi shuru yana nazarin abinda kwakwalwarsa ke tuna masa tunda ya fito daga asibitin yake nazari da tunani. Yace." Baya rasa nasaba da mu'amula ta da matata kasan mata da kishi dasa abu a rai mybe wannan ne ya janyo mata matsala. Ya kalleshi da fadin." Hakane yanzu kai wane hukunci ka yanke? a zahirin gaskiya idan ba kayi wani abu ba akan yarinyar nan ba to hakkinta yana iya kama ka da kowane lokaci saboda haka ka zauna kayi nazari da tunani a yanda kake bani labarin hallacin da tayi maka yaci ace kayi wani abu wanda zai nuna mata cewa lallai kana da niyyar auranta." Murmushin takaici yayi kafin yace." Wallahi gabadaya kaina ya kulle Asp na shiga rud'u! ina jin tsoran auran yarinyar azo ana tashin hankali abunda bana bukata kenan bana son matsala ko yaya take. Ya dinga kallonsa yana girgiza kai kafin yace." Ka zama namiji mana abokina rigima kake gudu to bari kaji da kayi aure da ba kayi ba, kullum a cikinta kake, domin ba zata daina zarginka ba, gwara ma kayi da hujja! amma ban ta'ba tunanin cewa Zinatu zata dinga baka tsoro ba a yanda na sanka haba *Jan wuya!* kada ka bani kunya mana." Dariya kawai yayi yana girgixa kansa, lallai akwai rikici a gabansa dan wallahi idan ya tuna Gimbiyar tashi gabansa har wani faduwa yake. Sallama sukayi da juna yaja motar ya bar shi a gurin yana daga masa hannu. Yana shiga dakin kafarsa ta cake! da kwalba! duk da a cikin takalmi take sai da yaji rauni jini ya fara zuba ya rike kafar yana d'ingisawa, gefe guda ya matsa yana bin dakin da kallo. Komai a hargitse duk ta farfasa masa manyan turarunkansa masu tsada! kayansa muhimmai ta watsar dasu a kasa, dakin dai tamkar anyi yak'i a ciki! Kafin ma yayi wani yunk'uri ta turo kofar dakin ta shigo........Kallo daya yay mata ya hango tsantsar tashin hankali a tattare da ita. Jarumta! ya aro! yayi bala'in shan kunu! da fadin." Meye haka! waye yayi min kaca-kaca da daki."? Ta nuna kirjinta da hannu " Nice nan."! da karsashi da kwarin gwiwa ta fadi maganar! Yace." Kece akan wane dalili? ko kina hauka ne."? Wani b'acin ran ya sake turnuke ta! tace." Kaine mahaukaci butulu maci aman...........Ya wanke fuskarta da lafiyayyan mari! yana wani irin tsuma! ya nuna kansa da fadin." Ni kike zagi saboda baki da mutunci."? Hawaye na zuba share-share a saman fuskarta........Tace." Kai waye da ba za'a zage ka ba maha'inci kawai."! Ya sake fusata! amma beyi yun'kurin dukanta ba saboda baya so ya saba da hakan ya danne bacin ransa yace." Ki fada min abunda nai miki wanda ya janyo har kike kira na da sunaye masara ma'ana." Taja hanci tana shashshekar kuka tace." Ba ni da lokacin zama na fada maka abunda kayi ai kai mai hankali ne ka zauna kayi nazari da tunani mtssswww!." ta k'are maganar da dogon tsaki! kafin ta juya ta fita zuciyarta kamar ta fashe saboda bacin rai! Da d'ingishi ya fita domin kwalbar ta cake shi sosai! d'aya daga cikin hadimanta maza ya kirayi d'aya shi ya jagoranceshi har cikin dakin ya bashi umarnin cewa ya gyara masa, ya zauna kujerar falo yana duba kafarsa, dole sai anyi dressing din gurin domin duk da ya cire kwalbar gurin yana bukatar gyara. Da yake a barrack din suna da likitocin dake duba lafiyarsu sai kawai ya kira daya daga cikinsu yazo ya dubashi ya bashi maganin rage zugi. Allah yasa ya gabatar da sallolinsa, kawai sai ya kwanta saman kujera yana mayar da numfashi..........Ya riga ya gano dalilin da ya sanya ta aikata wannan haukan! bai san wane irin kishi ne da ita ba.....hakika auranta yana nema ya zame masa matsala. shi kuma irin tashi jarrabawar kenan. Washe gari da ciwon jiki ya tashi domin k'afar ta tashi ta kumbura! haka nan ya daure yayi shirin fita domin baya tsammanin zai iya zaman gidan saboda gudun tashin hankali. Bai fita ba sai da ya nemi inda take saboda baya so ko yaya Allah ya tuhumeshi da hakkinta. Tamkar bata da damuwa haka ya sameta ta cakare! tayi gayu na kere sa'a! jikinta da dakinta in banda kamshin turare babu abunda yake.......Cikin zuciyarsa yake fadin *( D'an Adam tara yake bai cika goma ba)* Allah yai mata komai amma bata da kyawun hali. Babu yabo babu fallasa yai mata sallama........Gabanta ya fadi ganin yana jan kafarsa babu ma takalmi sai safa kawai! kafafun, yana tafiya da d'ya yana dingisa daya, ta tsirawa kafafun ido har ya k'araso kusa da ita bata sani ba. Babu walwala a tare dashi yace." Zan fita gurin aiki ina fatan baki matsala."? Idonta ta janye tana jin wani irin a tare da ita.......Ashe rauni yaji mai yawa! cikin zuciyarta take maganar.. Ganin ba tace komai ba kawai sai ya kama hanyar fita. Ta bishi da kallo 'kwalla na ciko idonta.....duk abunda tai masa shi ya janyo.......Idan ta tuna abunda ya faru kamar ta mutu da bakin ciki. Bai shiga headquarter nasu ba, sai da yaje asibitin ya dubata, babu shakka yaji dadin yanda ya ganta tayi garau! suna hira da Uwale. wacce take kwantar mata da hankali gami da bata tabbacin cewa ta kwantar da hankalinta Umaru kamar ya aureta ya gama. Maganganun Uwale sune suka sanyayar mata da zuciya.....Shi kansa likitan dake dubata yaji dadi sosai. nan ya cigaba da bata shawarwari masu kyau......... *Kuyi hakuri ina zuwa makaranta, shine dalilin da yasa bakwa samun update akan lokaci NAGODE *Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, 'yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne......0542382124....Binta umar gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 3/3/22, 19:56 - Buhainat: _Akwai ingantaccan maganin gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 4k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ *91&92* Wannan ciwon jikin da ya fita dashi ashe sa hannun zazzabi ne. domin koda ya zauna a ofis din kasa katabus! yayi kawai sai ya koma kan doguwar kujera ya kwanta zazzabin na sake k'arfi a jikinsa wani irin bacci mara dadi yana fizgarsa. Shigowar Asp ofis din ne ya zaburar dashi! ya bude jajayen idanuwansa yana kallonsa har ya k'araso gurinsa da wasu takardu a hannunsa. Ganinshi wani iri ya sanyayar masa da jiki da ya shigo da 'kwarin gwiwa sakamakon samun rahoton mutumin da suke ta nema ruwa a jallo. Gefansa ya zauna da fadin." Jarumi wai shin me yake damunka ne tuntuni nake kiran wayarka babu amsa wannan dalilin ya sanya kawai na yanke shawarar zuwa ofis din naka. Ya mike zaune da 'kyar! yana ya mutse fuskarsa yace." Bana jin dadin jikina wallahi zazzabi da ciwon jiki ke damuna." Maganar yake amma shi Asp din hankalinsa yana kan k'afarsa dake kumbure! Cike da al-ajabi yace." Rauni kaji ne babu labari."? Mirmushi takaici yayi yana danne b'acin ran dake
Chapter 62 · 0% Book details