← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 97

Sashe 55

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gtbabk....Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number* *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 2/23/22, 17:10 - Binta: *GJ* *79&80* Ya jima dafe da kai yana tunanin hanyoyin da zai bi gurin ganin ya kawo gyara da zaman lafiya gidansa, maganar gaskiya dole yarinyar nan ta gyara kuskuranta mutukar tana so ta zauna lafiya dashi to tilas ta kula dashi da duk bukatunsa, amma baya tsammanin zai hana Hamra'u hidima dashi mutukar ita din ba tayi wani abu akan al'amarinsa ba, idan yaga ta mayar da hankali gurin bashi kulawa to da wayo da dubara zai iya dakatar da ita Hamra'un akan abunda take cewa ta bari tukkuna har sai an daura musu aure. Zazzafar ajiyar zuciya ya sauke yana yun'kurin tashi kiran Asp ya shigowa wayarsa, sai ya koma ya zauna yana laluben wayar a cikin aljihun rigar dake jikinsa. Sam bai tsammaci jin maganar daga gare shi ba kawai sai yaji yana tuhumarsa akan abunda ya faru a tsakaninsa da yarinyar. Ransa yayi mutukar baci da jin irin tuhumar da Asp din yake masa dan haka sai yayi saurin katse shi a kaurare yace......."Asp kada fa ka manta da cewa wannan yarinya da ake magana akanta itace za'bi na tuntuni ita nake da ra'ayin aure kafin maganar Gimbiya ta sanyo kai, mai yasa kullum idan yarinyar nan zata kawo maka k'orafi baka bin ba'asi idan an bi ta 'barawo to abi ta mabi sawu, yarinyar nan har yanzu bata cika mace a gidanta ba, domin kuwa akwai sangarta da lalaci a tare da ita, duk wasu hanyoyin kula da miji ba ta san su ba, shin laifi ne dan Hamra'u tayi min hidima? dama can ita take kula dani kafin wannan al'amari ya faru saboda haka don Allah mu bar maganar nan domin kai kanka kasan gaskiya kake takewa saboda gudun bacin ran mara gaskiya." Asp din jikinsa yayi sanyi yace." Umaru duk abunda ka fada gaskiya ne to amma ba kayi la'akari da gidan da yarinyar nan ta fito, kasan dai gidan sarauta ba komai sukewa kansu ba, komai yi musu ake dole ta samu na'kasu ta wannan bangaran, ba wai ina goya mata baya bane nima nasan gaskiya, amma lamarin mata akwai rikici bana so wannan matsalar ta hargitsa maka gida domin 'karamar magana tana iya zama babba! shine dalilin da yasa nake baka shawara kayi wa tufkar hanci tun kafin lamari ya 'baci abunda nake nufi anan shine ita Hamra'u ta janye jiki daga duk wani abu da ya shafe ka ta bari tukkuna ku mallaki juna ina ganin shine maslaha a tsakaninku." 'Karamin tsaki yaja da fadin." Asp dacewa ne ace yarinyar nan ta d'auki belt ta zane yar mutane dashi? ko kuma dacewa ne ace ta bar gurin da nake kwanciya kaca-kaca babu gyara, kana maganar daga gidan sarauta ta fito mata nawa ne suke da sarautar amma suna tsaye akan mazajensu da kulawa dasu.....Na tabbatar da cewar duk irin rashin mutuncin da yarinyar nan take tana sane, tunda ta san taci abinci tayi ado da kwalliya dare yayi ta nemi biyan bukatar ranta to mai zai sanya ta kasa aikata ayyukan da ta san zasu faranta min rai, Asp ina son yarinyar nan sosai amma dole na auri wacce ta san mutuncina dana 'yan uwana wannan shine hukuncin dana yanke." Yace."Nima ban ha naka aure ba Umaru kawai ina baka shawara ne akan ka yi saurin gyara al'amarin kada ya 'baci, hakika abinda tayi bata kyauta ba, wannan dalilin yasa nake baka wannan shawarar." Yace."Shikkenan nagode sosai insha Allah zanyi kokarin ganin komai ya daidaita." Yace." To alhamdulillhi nagode da daukar shawarata." Sallama sukayi kowanne zuciyarsa cike da damuwa, mussaman shi Umar din da yake ganin kamar yarinyar tana nema ta dinga fitar masa da sirrin gidansa, duk yanda yake da Asp din baya bukatar yaji abunda ya shafi iyalinsa, ai ko babu komai sirri yana da dadi. Side din ta ya nufa, ya same ta kwance a gado taci kuka ta koshi kwayoyin idanuwanta duk sun sauya kala. Kallo d'aya tai masa ta kawar da kanta tana zumb'ura baki. Shi kam tsigar jikinsa ce ta tashi! ganin yanda idanuwanta sukayi jajawur! hakan ya daga masa hankali mutuka! wannan ya tabbatar masa da cewa tana sonshi tunda har take kishi a kansa. Ya zauna kusa da ita da fadin." Tashi muyi magana." Share shi tayi ta juya masa baya. Ya rike hannunta yana kokarin tayar da ita tana komawa. Kusa da ita ya kwanta ya janyota jikinsa sosai hannuwansa duk biyun yasa ya ratsa jikinta.........Ajiyar zuciya suka sauke a tare. Kimanin minti goma ya kai yana kokawa da zuciyarsa kafin ya daidaita nutsuwarsa ya fara magana kamar haka. "Me yasa zaki shedawa Asp sirrin gida na."? Kai tsaye tace." Saboda shi kadai zan shedawa abinda yake damuna ya rarrashe ni." Yaji wata kibiyar kishi ta soki makogwaronsa! yace." Kwanakin baya fa haka ki kayi min na gargade ki kan cewa bana so kina fita da duk wani abu da ya faru a tsakaninmu shin mai yasa ke ba zaki zama mace mai sirri da rike amanar mijinta ba." Da sauri ta mike zaune tana masa wani irin kallo tace." Yaushe ka bani damar hakan, bayan kullum kana munafurtata kana tare da yarinyar nan kuna mu'amula tamkar mata da miji, a ina ta samu key din sashenka? sannan meye hujjar ta na hawa gadonka, koda yake ban sani ba ko kana biyan bukatarka da ita." Ya dinga kallonta yana auna maganganunta......Maganar da tafi daukar hankalinsa "Ko da yake ban sani ba ko kana biyan bukatarka da ita." Wannan maganar ta bashi mamaki mutuka." Yace." Yanzu me ki kike nufi da wannan maganar? me ki ka dauke ni fasiki kome."? Ba tare data kalleshi ba tace." Duk abunda zuciyarka ta raya maka hakane a zuciyata." Ya sauke zazzafar ajiyar zuciya yana kokarin danne bacin ransa, baya so ya biye mata su zo suna hayaniya shiyasa yake bawa zuciyarsa hakuri, ya tashi zaune tare da kokarin rike hannunta tana fuzgewa. Yace." Ni Sulhu nazo muyi ba wata hayaniya ba, wannan maganar da ki ka fada a kaina ta 'bata min rai fiye da tunaninki amma ina so ki san wani abu da ni din mazinaci ne ina ganin da tuni kin sheda hakan tun a haduwar mu ta farko na samu dama iri-iri a kanki amma ban cutar dake ba, ki sani cewa yanda na tsani zina haka na tsani mutuwa ta, kullum cikin nesanta kaina nake da ita to mai zai sanye ki dinga alakanta ni da aikata hakan me nai miki ? ko kuma kina so ace mijinki ya kasance mazinaci ."? Shuru tai gabadaya jikinta yayi sanyi da kalamansa . Ganin haka yasa yace." Maganar Hamra'u muke a yanzu ba kya so ta cigaba da kula dani to kiyi gaggawar gyara kuskuranki, abun nufi anan shine ki dauki ragama ta da duk wani abun da ya shafe ni, ina nufin ci da sha na da kuma tsaftace makwancina ladabi da biyayya, sai kuma abu na karshe bani hakkina na aure wannan shine abubuwan da zakiyi wanda zai sa Hamra'u janye jikinta dani." Ajiyar zuciya ta sauke tare da d'an zumbura baki abunda ya zame mata jiki, tace." Ni a guri na duk wannan mai sauki ne, burina kawai ka fita daga sabgar yarinyar domin bana bukatar wata mu'amula ta shiga tsakaninku, kawai ta tattara kayanta domin bana bukatar ganinta a in da nake." Yace." Wannan ne kuma ba zai samu ba, na fada miki tun kafin kizo gidan nan yarinyar take, tun muna 'kauye muke tare tayi min hidima sosai kana kulawa da kakata babu dalilin da zai sanya ta bar gidan nan babu kwakwkwaran dalili." Wani irin kallo tai masa mai kama da harara kafin tace."Wai shin ma meye dangartakar dake tsakaninku."? Yace." 'Yar 'kanin Uwale ce a matsayin 'kanwa take a guri na." Tace." Bayan wannan ala'kar ai akwai wata dan ba zan mance ranar da kake shedawa Asp ita a matsayin wacce zaka aura ba shin ko ba haka bane."? Da yake yana bukatar maganar ta mutu sai kawai yace." Wannan ai tsohon zance ne ki ajiye shi a gefe ke dai kawai ki gyara kusakuranki sai mu zauna lafiya, amma ki daina k'yamar ahali na." Ajiyar zuciya ta sauke tana jin sassauci a cikin zuciyarta, tace." Idan ka rike min alkawari nima zan baka mamaki."! Murmushi yayi wanda yake fito da zahirin kyawunshi yace." Kada ki damu amma wane irin tanadi ki kayi min yau domin ina tunanin angwancewa kin shirya ko."? Jin abinda yace yasa tayi masa wani irin kallo, ya daga mata gira gami da so ya tabbatar mata da maganarsa.........Gabadaya jikinta sai ya mutu, sai kawai ta sunkuyar da kanta tana tunanin abunda zai faru a tsakaninsu idan daran yayi. Koda ya shiga sashen Uwale domin ya samu Hamra'u da maganar don ya nuna mata kuskuran abinda take a yanzu, ada idan tayi hakan babu laifi amma yanzu tunda yayi aure to abinda yafi kamata ta janye jikinta domin samun zaman lafiya. Da maganar ya shiga amma abun mamaki sai ya kasa cewa da ita komai gabadaya tausayinta ne ya rufe shi ganin yanda take ta rawar jiki a kanshi, baya tsammanin zai iya watsa mata 'kasa a ido kuma mutukar ya cika shi dan halak ne dole ya aure ta ko dan irin soyayyar da take nuna masa, amma ya tabbatar da cewar hakan ba zata samu ba sai an kai ruwa rana a gidan. Allah kenan, yayin da ya ci burin angoncewa da amaryarsa a daran ranar sai amaryar tashi ta 'bule jini ya 'balle! godiya tai ga Allah daman tunda ya sheda mata kudirinsa take cikin damuwa ganin wannan jinin ya sanya ta kwantar da hankalinta kamar tsumma a randa. Da yake ba ta da kirki ba ta fad'a masa halin da take ciki ba ta kyaleshi ya gama sakin jiki domin ba tayi masa waigi da duk sassan jikinta ba pant kawai ta bari a jikinta, ta sakar masa ko'ina yana yin yanda yake so, sosai ita dashi suka kai makura gurin bukatuwa, ya dinga kyarma zufa na keto masa, kaf ya cire kayan baccin dake jikinsa ya raba kafafunsa a kanta kokarin cire pant din yake yaji
Chapter 55 · 0% Book details