← Book details Goje Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 97

Sashe 80

Goje Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana, kawai taja bakinta tayi shuru takaici tare da tausayin 'yar ta kadai ke damun zuciyarta. Ganin yanda hankalinta ya tashi yasa Shafara'u kwantar mata da hankali da tausasan kalamai masu sanyaya zuciya gami da sa tawakkali da dangana. Yana kallonsu yayin da suke tattauna maganar so kaunar Safah na cigaba da bin kowane 'bargo na jikinsa, har yanzu tana nan da kyawun zuciya da kuma fahimta, a duk sanda Gimbiyar tasa ta rikice ta tafka wani shirman yana alfahari da ita gurin ganin ta shawo kan matsalar da duk ta shafe su baki d'aya. **** A daran Asp ya kira wayarsa don da shima har yayi zuciya da abubuwan da yake masa na rashin kyautawa, sai kuma yaga da cewar kiran wayarsa domin su tattauna akan maganar yarinyar da aka bashi amanarta. Dai-dai lokacin da ya fito daga wanka kiran ya shigo wayarsa. Sai da ya mula tukkuna kafin ya daga wayar yayi salama babu cikakkiyar walwala a tare dashi. Ya amsa shima babu sakewa kafin yace." I dan babu damuwa ina so mu tattauna muhimiyyar magana." Ya sauke ajiyar zuciya kafin yace." Ba damuwa ina sauraranka." Yace."Maganar dai akan Zinatu take duk da baka san na shiga cikin al'amarin amma ya zama dole na shiga tunda amana ce a hannuna." Ya danne 'bacin ransa kafin yace." Okey ina sauraranka." Ya cigaba da cewa." Yanzu Umaru dai-dai kenan abinda kayi ka kyauta! har ka rufe idonka kaci mutunci yarinya da juna biyu a tare da ita, 'bacin ran abinda kake har ya kai ta tattara kayanta ta tafi gidansu, Umaru kai a ganinka hakan dacewa ne."? Yace." Kaga Asp ni da hankali da tunani nake al'amurana, wannan m atsalar data shafe ni ce babu ruwanka da ita, maganar Zinatu ta tafi gidansu wannan matsalarta ce, idan tayi ra'ayi ta dawo idan tana ganin zama a can yafi mata bani da damuwa." Asp din ya fusata! da fadin." Kana da hankali kuwa Umaru shin ko ka manta waye mahaifin yarinyar ne."? Murmushin takaici yayi kafin yaja karamin tsaki da fadin." Shiyasa ai farkon magana ta da kai nace ni da hankali da tunani nake tafiyar da al'amura na, mahaifin Zinatu shine Sarkin *KANO* to sai me? bari kaji Asp Allah kadai shine abin tsoro ba wani mahaluki ba, kuma idan ka manta bari na tuna maka dama can ban furta ina sonta ba, bani akayi to akan me zan damu kaina, sai magana ta karshe da za muyi da kai dan naga ka damu da yarinyar nan da yawa baka kaunar damuwarta yanzu ma zan sake maimaita maka cewa zan iya rabuwa da ita ka aura sai kuma me."? Asp jikinsa ya mutu murus! bakinsa ya mutu ya gaza furta kalma daya hakika ya bashi mamakin da bai taba tunani ba. kawai sai ya kashe wayar ya ajiye a gefe ya shiga tunani akan al'amarin......Tabbas akwai alamun tambaya wannan abun da abokin nasa yake bana masu hankali da tunani bane. Kamar wanda aka daukewa sha'awa haka ya zama surkududu! duk da yana ganin amaryarsa a kusa dashi hakan bai sanya yayi sha'awarta ba, gashi nan dai zuciyarsa a kusa abu kadan yake fusata shi . Ta shigo dakin ta sameshi a kwance ya tsirawa rufin dakin ido......A sanyaye ta zauna a kusa dashi da fadin." Yaya na." Ya kalleta tare da kokarin tashi zaune. Tace."Kayi hakuri kayi bikon matarka domin Uwale da gaske take akan kudirin data dauka. dan naga tana yi min wani irin kallo, yanzu bata sakewa dani. Yayi jim yana nazarin maganar kafin yace." Babu ruwanki a cikin wannan al'amarin kin gane ko." Shuru tayi tana kallonsa, ya cigaba da cewa." Aiki zai kai ni Zamfara da yardar Allah gobe da asubah zamu d'auki hanya, ki kula sosai gida kuma duk rintsi kada ki bari Uwale tasa kafa ta fita daga gidan nan." Ta marairaice fuska da fadin." Yaya na tafiya kuma nifa amarya ce zaka tafi ka barni." Ya tsira mata ido yana kallo, sam abunda take bai burge shi sai ma mugun haushi da ta bashi. tsaki! yaja dogo kafin yace " Tashi kije ki kwanta." Ganin yanda ya murtuke fuskarsa! babu shiri ta tashi salo-salo ta fita daga dakin. ya koma ya kwanta yana cigaba da tunanin rayuwa. A 'bangaran Zinatu kuwa tunda taji yanda akayi da mijin nata, ta 'kara tsanarsa a cikin ranta, cikinsa ma da take dauke dashi ta dora masa karan tsana tun kafin yazo duniya, dan dai yayi kwari ne amma da duk wuya sai ta zubar dashi ta yar da kwallon mangwaro ta huta da 'kuda. **** Tafiyarsu Umar din da sati biyu, Asp ya shirya zuwa *KANO* domin tattauna maganar da ta shafi auran abokin nasa, ya kud'urce a ransa cewa kafin abokin nasa ya dawo daga bakin aiki yayi masa kokari gurin ganin matarsa ta dawo dakinta. Bahaushe yace." Kiwon mutum ake ba dabbah ba, wannan damar Commissioner ya samu ya dinga bibibiyar al'amarin har dai ya fahimci abinda yake da akwai. dama yana bala'in jin haushin kusancin dake tsakaninsu. A ranar da Asp din ya tafi shi kuma ya samu damar kiran Umar din su gaisa kana sukayi maganganun da ya shafi aikinsu, kafin ya shigo masa da maganar dake bakinsa Asp baya gari yaje Kano ziyara. Sai ya shiga tunanin abinda ya kai Asp garin Kano bayan bashi da wasu 'yan uwa a can, wani sashe na zuciyarsa yace masa yaje gurin matarka ne.'' Wani irin bakin ciki ya turnukeshi tabbas ko shakka ba yayi abinda ya kai shi garin Kano kanan. wato dai mutumin nan ba zai daina bibibiyar matarsa ba, lallai wannan karon dole ya tauna tsakuwa dan aya taji tsoro! Saboda haka yana sallama da Commissioner din bai jirayi komai ba ya nemi number Asp din, sai kuma aka samu akasi domin shi Asp din yana ganin kiran yaki dauka saboda jikinsa ya bashi ba alkairi bane. Ya kirashi ya kai sau biyar bai daga ba. Ya fusata! ya kira number ta, itama tayi shakulatun 'bangaro dashi yayi-yayi ya gaji tana kallo bata daga ba. takaici yasa ya jefar da wayar ya turmutsa yatsun hannuwansa cikin sumar dake kansa yana hargitsawa, jikinsa in banda karkarwa babu abinda yake. Sai da yaci abinci tukkuna ya huta sannan Maimartaban ya zauna dashi domin tattauna maganar da ta kawoshi garin. Da yake dattijo ne mai halin girma bai nuna 'bacin ran akan abinda ya faru ba, sai ma dinga kokarin dora laifin a kan 'yar tasa halin mutanan da kenan ma'ana (kaso naka duniya ta k'i shi) ka qi naka duniya taso shi) Asp din ya bada hakuri sosai ya bukaci a bashi Zinatu din domin tafiya da ita. Ya jima yana nazarin maganar kafin ya kalleshi da fadin." Da izinin abokinka kake tafe ko kuma dai kaine kake kokarin gyara al'amarin."? Ya sauke ajiyar zuciya da fadin." Kwarai kuwa ranka ya dade kafin nazo nan sai da muka tattauna maganar dashi, yace shi bai ce mata tazo gida ba sa'bani kawai suka samu ya dawo gidan ya samu bata nan. dalilin da yasa kuma ba muzo tare ba, yaje *Ran gadi!* garin Zamfara na san kana da labarin irin tashin hankali da yake faruwa a garin." Yace." Tabbas muna da labarin irin rikicin da yake faruwa a garin, muna kuma rokon Allah ya kawo mana zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa baki daya. Ya amsa da "Ameen ya Allah insha Allahu komai zai-dai ta za'a samu tsaro da kwanciyar hankali mutukar an hadu da shuwagabbani nagari." Yace." Wannan haka yake, samun shuwagabbani nagari a wannan zamanin yana wahala dole muma mu dage da addua mu kuma gujewa abinda Allah baya so sai mu zauna lafiya.'' Asp ya risina cikin girmamawa yace ." Allah ya taimake ka kayi magana mai ma'ana yawancin zagin shuwagabbanin da muke shine babbar matsala a gare mu, addua ya kamata muyi musu domin Allah ya basu ikon aikata abinda ya dace to kaga dole mu kiyaye harshen mu mutukar muna so mu zauna lafiya a k'asa." To tsakanin Asp da Sarki Umaru sun tattauna maganganu masu muhimmanci wanda sai mai hankali da tsinkaye ne zai fahimci inda suka dosa. Da farko bijirewa tayi da taji maganar ita kam duk abinda za'ayi ba zata koma ba ta gama auran har abadah. Babu wanda bai shiga dakin ya rarrasheta ba amma fafur! taki karshe ma sai kawai ta kwanta tana kuka ita ta gaji da wannan al'amari wane irin aure ne wannan mara 'yanci. Da yake akwai kauna mai tsanani a tsakaninta da mahaifinta, koda ya shiga dakin rungumeshi tayi tana kuka tace." Ni ba zan koma ba nafi bukatar rabuwa da auran saboda babu kwanciyar hankali a cikinsa, tun farko sai da nayi tunanin hakan zata faru amma babu wanda ya fahimce ni sai yanzu gashi abubuwa marasa dadi suna biyo baya ina ganin ko na koma babu abunda zai sauya. Jikinsa ne ya mutu a hankali ya zauna tare da zaunar da ita a kusa dashi, cikin laluma ya fara kwantar mata da hankali, shi kansa baya san ta koma a yanzu yafi bukatarta a gabansa saboda yana tausayawa halin da take ciki, hakika yaron ya bashi mamaki mutuka! Ya rarrasheta sosai tare da sake bata umarni a karo na biyu, ya kuma tabbatar mata da cewa shine na karshe wata matsalar ta sake faruwa a tsakaninta da mijinta to ba zai mata dole ba amma dai a yanzu tayi masa alfarma ta koma dakinta. Mahaifinta yafi karfin alfarma a gurinta, tabbas idan ta bijirewa bukatarsa ba zata ga da kyau ba, dole ta sanya hakuri da dangana a zuciyarta, amma a can kasan zuciyarta ita kadai tasan abinda damunta. Albarka da addua da fatan alkari iyayenta sukayi mata insha Allahu kuma adduarsu ba zata fad'i a kasa ba. **** Koda suka isa gidan Uwale kasa 'boye farin cikinta tayi ita kuwa Hamra'u kamar wacce aka aikowa da mala'ikan mutuwa! tayi kicin-kicin! idonta jawur kamar me shirin fashewa da kuka! Uwale ta kalli Asp da fadin." Hakika samun irinka a wannan zamanin sai an tsananta binkice! kai ba za'a kira ka da aboki ba domin ka wuce haka! kana tsaye akan Umaru da al'amuransa Allah ya saka maka da alkairi ya biya ka da aljanna madawwamiya. Ya amsa
Chapter 80 · 0% Book details